Ramadan: Watan neman lada
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Ramadan: Watan neman lada

Salam, Edita zan so ka ba ni fili a wannan jarida ta Aminiya don na tofa albarkacin bakina a kan zagayowar watan Ramadan.  Watan Ramadan, wata ne mai alfarma da bayin Allah ke ninka ibada don neman lada a wurin Ubangiji.  Wata ne da ake neman rahama da gafara da ’yantuwa daga wutar Jahannama.
Don haka ina kira ga Musulmin duniya musamman na Najeriya da mu zage damtse wajen yin ibada, ko ma yi dace daga Rahamar Ubangiji.  Haka kuma ina kira ga gwamnati da kuma ’yan kasuwa da su yi wa Allah su saukaka wa talakawa wajen rage farashin kayayyakin masarufi musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki.  Abin takaici da mamaki shi ne za ka tarar wai a wannan lokaci ne wadansu marasa tsoron Allah suke wasa wuka don cin kazamar riba daga wurin talakawa masu yin azumi.  Maimakon su sassauto da farashin kayayyaki, sai ka tarar a wannan lokaci ne suke ninkawa tun da sun san dole ne talaka ya saya ko yana so ko ba ya so.  Sannan wadansu masu hannu da shuni, maimakon su rika tallafawa talakawan da ke kusa da su ta hanyar ciyar da su abincin azumi sai kawai su yi biris daga su sai iyalansu, inda za ka rika jin kanshin toye-toye yana tashi daga cikin irin wannan gidaje alhali wani ko kunen da zai yi buda baki bai da shi.
Ina fata gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma na kananan hukumomi za su fito da hanyoyin da za su rika ciyar da marasa galihu da wadanda suke cikin wani yanayi musamman a wannan lokaci na Ramadana.  Ina yi wa daukacin Musulmi barka da zagayowar Ramadan.  Allah Ya sa mu dace, amin.
 Daga A’isha Kabir Jos 07011305295

Real Madrid ta kashe bakin tsanya!

Salam, Edita ina son ka ba ni dama don in taya daukacin magoya bayan kulob din Real Madrid da ke Sifen da ke zaune a sassan duniya musamman na Najeriya murnar lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) a karo na 11 a ranar Asabar da ta wuce. A gaskiya wannan nasara da muka samu ya kashe bakunan ’yan adawa irin su magoya bayan FC Barcelona da na Manchester United da Arsenal da Chelsea da Bayern Munich da PSG da kuma na Atletico Madrid da sauransu.  Yanzu dai mun kashe bakin tsanya. Edita, ban san lokacin da na zuba ruwa a kasa na sha ba saboda murna.  Yanzu mun kashe bakin tsanya, don babu wani kulob da ya kama kafar na Madrid wurin lashe wannan kofi a duk fadin duniya.  Yanzu sai dai mu ce na gaba ya yi gaba, na baya sai.....
Sako daga Alhaji Jinjiri na Alhaji Shu’aibu Mil 12 Legas 07083382075

Mu cigaba da yi wa Buhari addu’a

Aminiya ku taimakeni wajen yin kira ga ’yan uwana ’yan Najeriya da mu cigaba da yi wa kasarmu addu’a ta alheri kuma mu kara yi wa shugaban kasarmu addu’a.  Wallahi Buhari ba shi da manufar cutar da mu talakawa  duk abin da da yake yi saboda mu ne kuma saboda dawo da martabar Najeriya.
 Haba ’yan uwana kun manta da katin da kuka saya don taimakawa Buhari?  Kada ku sake makiya sun cimma burin ganin bayan gwamnatin Buhari da ma ba kaunarta suke ba.
Allah Ya ba mu zaman lafiya kuma Ya taimaka Shugaba Muhammadu Buhari, Ya ba shi kariya.
Daga Rabi’u Yunus Agege, Shugaban kungiyar Gizago reshen Jihar Legas  09093333955

Gani ga wane ya ishi wane tsoran Allah

 Na yi wannan magana ne kan hukuncin daurin rai da rai da wata kotu a kasar Senegal  ta yanke wa tsohon shugaban kasar Chadi Hussene Habre kan kisan gillar ’yan adawa lokacin milkinsa.  Hakika wannan hukunci ya yi daidai, kuma ya zamo darasi ga sauran shugabanninmu na Afrika masu milkin kama karya.  Daga Muhammad Idris Kabuga Kano.  08069006931

Ga Gwamna Kashim Shettima

Assalamu alaikum, Aminiya mai farin jini. Don Allah ku ba ni dama in yi kira ga gwamna Kashim Shettima, na Jihar Borno. A gaskiya lokaci ya yi da za ka kawo karshen bambancin da ake nuna wa kananan ma’aikatan Kudancin Jihar Borno.  A yanzu haka maganar da nake yi Wallahi albashin da ake biyan ma’aikatan  jihar aaalla ya yi kashi uku domin  wasu suna samun dubu 10, wasu dubu 15, amma har yanzu ma’aikatan Kudancin Borno dubu 8 ake biyansu. Da wannan nake kira ga gwamna Kashim Shettima in har da gaske kake ikirarin kai na kowane ne to wajibi ka gaggauta kara wa ma’aikatan Kudancin Borno albashi, domin  ba za mu kyale a rika fifita wasu a kanmu ba.
Da fatan sakona ya isa kunnuwan gwamna Shettima amin.
A karshe muna addu’ar Allah ya kawo mana karshen matsalar rashin tsaron da ya addabi Jihar Borno, da ma sauran sassan kasarmu Najeriya baki daya amin.
Adamu Aliyu Ngulde, daga Maiduguri.  08032135939.

Jinjina Ga Gwamna Bello Masari

Bayan kwashe shekaru muna jiran romon dimokuradiyya a Jahar Katsina, yanzu a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, mun samu aiyyukan raya kasa. Don haka mu al’ummar garin Funtua babu abin da za mu ce sai godiya.
Daga Mainasara Nasarawa Funtua. 08034208356

PDP ta shiga tsaka mai wuya

Assalamu Alaikum Edita; hakika wasu hukunce-hukunce biyu da wasu kotuna biyu masu daraja daya suka yanke a kan
rikicin shugabancin da ya dabaibaye jam‘iyyar PDP sun kara ruda al‘amurra, ganin yadda kotunan biyu saka yanke hukunce-hukunce masu karo
da juna, inda daya kutun ta dakatar da shugaban rikon kwarya wato Ali Modu Sheriff, yayin da daya kotun ta dakatar da Ahmed Makarfi tare da umartar Ali Sheriff ya ci gaba da rike shugabancin Jam’iyyar ta PDP.
To a gaskiya yin hakan da kotunan suka yi a lokaci guda, sam bai dace ba.   Kamata ya yi ‘yan jam’iyyar PDP su koma su dinke barakar da ke tsakaninsu domin masu iya magana na cewa mai daki shi ya san inda yake masa yoyo.
Daga Kwamared Mohammed Mai Kaset Cross Kauwa karamar Hukumar Kukawa a Jihar Borno. 08138775015

A taimaka wa ’yan gudun hijira

Yakamata gwamnatin Najeriya ta yi wani tsari mai kyau, wajen tallafawa ‘yan gudun hijirar Arewa maso Gabashin Najeriya, saboda a gaskiya ‘yan gudun hijirar suna cikin matsala, suna mutukar bukatar taimako, saboda yawancin tallafin da ake bayar wa saboda su, ba ya kaiwa garesu, kuma da yawa daga cikinsu abincin da za su ci ma yana yi musu wahala.
Daga Muhammad Babangida Kiraji Gashua 08029388699.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited