Allah ya jiqan Muhammad Ali
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Allah ya jiqan Muhammad Ali

Dukkan mai rai sai ya dandani mutuwa.  Rasuwar shahararren madambacin nan dan asalin kasar Amurka, watau Muhammad Ali,babban  rashi ce idan aka yi da irin shaharar da dan kwallon yay i kuma ya karbi addinin Musulunci.

Sannan duniya ta shaidi marigayin a matsayin mai dabi’u masu kyau kuma hatta wadanda ba Musulmi ba sun shaide shi a kan mutum mai rikon gaskiya da taimako da kuma amana.  Wannan ia ishe mu isahara mu rika tuna cewa duk mai rai mamaci ne.  Muria tunani da cewa mutuwa ta kasance mai yanke jin dadi, mai raba ‘ya’ya da iyaye, mai yanke zumunci wacce ba ta kuskuren zuwa ga inda aka aike ta, wacce ba ta gaggawar isa inda ba a aike ta ba, wacce duk talauci duk matsayi duk dukiya zamowar mutum na kwarai ko akasi ba ya hana ta zuwa don yin nata aikin.
Daga karshe ina fata Allah Ya yi jinkai da rahama ga
Muhammad Ali, ka ba zuriyyarsa hakuri da juriya da lada. Mu kuma idan tamu ta zo Allah Ya sa mu cigaba da kyau da imani, amin.  Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina,
07066434519, 08080140820.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited