Saqonnin waya
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Saqonnin waya

’Yan kasuwa ku tausaya wa talaka

Da yawan ’yan kasuwa kan wasa wukar u don samun riba mai yawa musamman idan aka ce watan Azumi ya kama, kayayyaki na yin tashin gwauron zabi. Mu sani cewa dukkan wanda ya saukaka a harkar kasuwancinsa musamman a cikin watan azumi wanda ke tare da dmbin falala, to Allah Zai saukaka masa tare da sa albarka a kasuwancinsa.  Don haka muke kira da roko ga ‘yan kasuwarmu a duk inda suke da su dubi girman Allah su saukaka musamman a irin wannan lokaci na Azumi da muke ciki. domin a gaskiya ana cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa, kuma hakan na shafar talakawa marasa karfi. Allah Ya ba mu ikon yin amfani da wannan shawara, Ya sa mu gama wannan ibada lafiya, Ya ba mu dukkan alkairan dake cikinsa amin.
Habibu Ibrahim Central Market Katsina  07038653949

Shugaba Buhari bai cika alkawari ba

Salam, Edita don Allah ka ba ni dama a wannan filin mai albarka domin in yi tsokaci akan alkawarin bayyana dukiyar da gwamnatin Shugaba Buhari ta ce ta kwato a hannun jami’an tsohuwar gwamnatin da ta gabata wadanda ta ce an sace ba bisa ka’ida ba, wanda shi shugaban ya ce zai bayyana yawan kudaden a ranar 29-5-2016 wato ranar da gwamnatinsa ta cika shekara daya, amma maimakon mu ji ya cika wannan alkawari sai kawai muka ji shiru wanda duk dan Najeriya bai yi tsammanin haka za ta faru ba, musamman ganin yadda muka dauki shugaban kasa mai magana daya.
Daga Abdulsalam Muhammed Lema Tsagem, Ma’ajin kungiyar Muryar Jama’a Reshen Jihar Katsina  08038792668.

 Tafiyar Buhari Landan
Hakika tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari Landan domin neman magani ya nuna a fili cewa ba mu da kwararrun likotoci ko kuma ingantattun asibitoci a kasar nan. Hakika yin hakan zai kara rage kimar Najeriya a idon duniya, musamman a bangaren kiwon lafiya, Dan haka kamata ya yi a inganta asibitocinmu na cikin gida da kwararrun likitoci da ingantattun kayan aiki, maimaikon yawon neman magani a aasashen ketare.
Daga Kwamared Mohammed Mai Kaset Cross Kauwa a karamar Hukumar Kukawa Jihar Borno Najeriya. 08138775015.

Allah ya ba Shugaba Buhari lafiya
Aminiya ku taimake ni da fili don in yabawa fadar gwamnatin Najeriya da ta sanar damu cewa Shugaban kasar mu Muhammadu Buhari zai tafi neman magani na kunnensa.   Muna yin godiya da aka ba mu hakkin mu, wannan shi ya nuna mana cewa mun samu canji. Ina kiraga ‘yan  uwana ‘yan Najeriya da mu yi wa shugaban kasarmu addu’a Allah Ya ba shi lafiya.  Sako daga Rabi’u Yunus Kura Agege, Shugaban kungiyar Gizago Reshan Jihar Legas 09093333955

Allah Ya jikan Shehu Musa Kallah Kano
Aminiya don Allah ku ba ni dama in mika sakon ta’aziya ga iyalai da ’yan’uwa da masoyan Shehin malamin nan, Shehu Musa Kallah Kano da Allah Ya yi wa cikawa  ranar Litanin 30 ga watan Mayun 2016.  Shehun malamin dai ya sha jinya. Allah Ya gafarta masa, Ya sa Aljanna ce makomarsa.  Mu kuma idan lokacin mu ya zo Allah Ya ba mu ikon cikawa da imani. Daga Muhammad Kabir Salisu, Gazarawa Communication Center Katsina, 08034200141

Ina taya Hillary Clinton murna
Ina taya uwar gida Hillary Clinton murnar samun adadain wakilai da zai ba ta damar yi wa jam’iyarta ta Democrat takarar shugabancin Amurka.  Da fatan Allah Ya ba ta nasarar kayar da Donald Trump a babban zaben da ke tafe.
Daga Mahmud Salihu kaura Namoda. 07067557586

A taka wa ’yan Biyafara birki
Muna kira ga shugaba Buhari da hukumomin tsaro ya kamata su dauki matakin gaggawa domin ganin sun taka wa masu fafutikar Biafara birki, ganin yadda kullum suke cigaba da yunkurin ballewa
Daga Najeriya.  Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999

A sassauta dokar zirga-zirgar Keke-Napep a Yobe
Assalamu alaikum Aminiya, ku ba ni dama na yi kira ga Shugabannin tsaro da na gwamnatin Jihar Yobe, dangane da dokar takaita zirga-zirgar da suka sanya mana a manyan biranen Jihar kamar na Damaturu da Potiskum da sauransu, na dakatar da zirga-zirgar mashinan Keke-Napep daga karfe 6 na dare zuwa 6 na safe.   Fiye da shekara guda kenan wannan dokar take aiki, Muna kira ga duk wadanda ked a ruwa da tsaki a wannan bangaren da su taimaka su kara wa mashinan lokacin zirga-zirga a wannan lokaci na azumi, domin saukake mana wajen tafiya wuraren tafsirai, da sallolin tarawi a cikin wannan wata mai albarka na Ramadan. A batu na gaskiya kowa yasan an samu cigaba ta fuskar tsaro a jiharmu, amma har yanzu muna takure saboda wannan matsi na dokar. Don haka muke kira da babbar murya gare su albarkacin wannan wata mai daraja, da su kara mana lokaci domin gudanar da ibadunmu a tsanake.
Daga karshe ina yi wa daukacin al’ummar Musulmi murna dangane da shiga watan Ramadan, tare da addu’ar Allah Ya ba mu albarkar da ke cikinta, Ya kuma nuna mana karshensa lafiya kamar yadda muka ga farkonsa. Amin.  
Daga Usman Bin Affan Damaturu, Jihar Yobe 08038001563

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited