Ina makomar masu shaidar NCE?
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Ina makomar masu shaidar NCE?

Sabon shirin xaukar malaman wucin gadi har dubu 500 da gwamnatin Najeriya ta qaddamar abu ne mai kyau, sai dai kuma gwamnatin ba ta yi wa masu takardar shedar karatun N.C.E  adalci ba, domin da farko shugaba Buhari ya faxi cewa har da su za a haxa amma kuma yanzu da aka soma xaukar sai muka ga ba haka ba ne, masu digiri kawai ake buqata.  
To shin su masu N.C.E  waxanda su aka fi sani da aikin koyarwa wane tanadi gwamnatin ta yi masu?  Daga Mahmud Salihu Qauran Namoda, Jahar zamfara. 07067557586

’Yan kasuwa a tausaya wa talaka

Assalam Edita don Allah ka ba ni dama na yi kira ga ’yan kasuwa su dubi halin da jama’a ke ciki musamman talaka su rage farashin kayan abinci duk da cewa mun san halin da suke ciki amma akwai sauqin da suke samu wajen sayen kayan don yanzu koda xan kasuwa ya sawo kaya da sauqi amma sai ka ji ya ce kaya sun yi tashin gwauron zabi, don haka da mu da ku mu ji tsoron Allah ko zai kawo mana sauqi. Daga qarshe  ina roqon Allah Ya albarkaci qasarmu da sauran qasashen musulmi amin.  
Daga Zaki Abubakar Bashire 08161831138

Ta’aziyyar Amodu Shu’aibu

Muna  jajajantawa  ‘yan uwa  da  iyalai  da ma  al’ummar  Najeriya  sakamakon  rasuwar  gwarzo  kuma  haziqi  mai  kishin qasa  Marigayi  Amodu  Shuiaibu.  Rashi ne  babba  a harkokin wasanni  a Najeriya.   Ba rabo  da gwani ba  kafun  a mayar da  kamarsa. Allah Ya jiqansa  kuma  Ya gafarta  masa,  Ya sa  mutuwa  hutu ce a gareshi.   Mu kuma  idan  tamu  ta zo  Ya sa  mu cika  da imani.
Daga Alhaji Umar Forever Gashua.

Jinjina ga Shugaban Hukumar EFCC

Ina so na yi amfani da wannan dama wajen jinjinawa Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu, akan irin qoqarin da yake na kama waxanda suka sace kuxin Najeriya don su azurta kansu. Sun bar mafi yawan ‘yan Najeriya a cikin qunci, ba wutar lantarki, ba ruwan sha mai kyau, ba kiwon lafiya ba tsaro, ba hanyoyi, ba ilmi mai inganci. Saboda haka muna goyon bayanka, akan wannan aiki mai mutuqar wahala, kuma wannan aikin da kake sadaukarwa ce ga qasa.  Allah Ya kareka.  
Daga Muhammad Babangida Kiraji Gashua 08029388699.

Ga Gwamna Bello Masari

Assalamu alaikum , don Allah ku bam u dama domin mu yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina Honorabul Aminu Bello Masari, a madadin al’ummar garin Tsagem da ke Qaramar Hukumar Mani muna kira a gare ka ka kawo mana xauki a kan tarin matsalolin da ke damunmu.   Na farko ba mu da kyakykyawar hanya daga Muduru zuwa Tsagem ta wuce Qaramar Hukumar Mani. Na biyu ba mu da ruwan sha mai kyau domin dam xin garin ya cike yana bukatar a sake yashewa sannan asibitin garin babu likitoci ba malaman lafiya babu kayan aiki, idan mutum ba shi da lafiya sai dai ya je asibitin garin Mani ko na Katsina ko da mutum yana cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai ne, musanmanma mata masu juna biyu sun fi fuskantar wannan matsala.   Da fatan ka ji wannan kira namu amin.
Daga ’yan qungiyar taimakon kai da kai ta garin Tsagem ta hannun Abdulsalam Muhammed Lema Tsagem 08038792668.

Jinjina ga shirin
xaukar malamai

Allah ya sa wannan yunkuri na samarwa matasa ayukkan yi na N-Power, da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kirkiro, ya sa kwalliya ta biya kuxin sabolu.
Daga Abdulmalik Sa’idu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08069807496

Jinjina ga Sarkin Musulmi

Salam Edita don Allah ka ba ni dama na bayyana ra’ayina dangane da namijin qoqarin da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya yi wajen yin kira ga shugaban kwastan na qasa ya qyale a shigo da shinkafa saboda halin da talakawan Najeriya suka shiga.   Haqiqa wannan kiran ya dace. Ya zama dole shugabanninmu su yi koyi da Sarkin domin faxawa gwamnati gaskiya.  
Daga Aminu Baka Noma Sani Mai Nagge Kano 08028505350

Kira ga hukumar
wutar lantarki ta Jihar Kebbi

Assalamu alaikum, Edita don Allah ka isar min da wannan saqo zuwa ga hukumar bada hasken wutar lantarki masu kula da yankin Qaramar Hukumar Maiyama da ke Jihar Kebbi cewa cika  alqawari yana daga cikin cikar kamala.  Kun sava alqawarin da kuka xaukar wa al’ummar Maiyama cewa su ba ku kuxin watan huxu za ku ba su wuta a watan 5 ba tare da wata matsala ba.   Sai gashi gara jiya da yau.  Don haka ku sani daga yanzu babu kuxin da za mu sake biya idan ba mu samu wuta ba.  
Daga Nasiru Musa Maiyama a madadin al’ummar Maiyama 08062206733 ko 07066516731

Kira ga Gwamnan Bauchi

Allah ya sa gwamnatin Jihar Bauchi ta waiwayi ’yan fensho, da ma’aikatan gwamnati don ta share musu hawayensu, wajen biyansu albashinsu musamman a wannan lokaci na watan Azumi.
Saqo daga: Sani Mohammed Chindo 08030918913

Jinjina ga Aminiya

A gaskiya Aminiya kuna qayatar da mu sosai saboda ire-iren labaran da kuke samar mana. Da fatan za ku dore da yin haka.  
Daga Hassan Haliru  This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited