Jam’iyyar PDP ku bi shuruddan kundin dokoki
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Jam’iyyar PDP ku bi shuruddan kundin dokoki

Salam. Edita don Allah a ba ni dama a wannan jarida tamu mai albarka domin in yi tsokaci game da rikice-rikicen da babbar jam’iyyar adawa ta PDP take fama da shi a matakin tarayya, tsakanin shugabanninta na kasa, inda kowane bangare na magoya baya suke ganin cewa nasu ne jagoran jam’iyyar ta PDP, wato tsakanin bangaren Sanata Ali Modu Sharif, da na Sanata Ahmed Makarfi, inda kowane daga cikinsu yake ganin shi ne shugaban tafiyar ba don komai ba, sai don rashin bin tsarin da jam’iyyar take da shi a cikin dokokin da ta shimfida da a kundinta na tsarin mulkinta. Hakika idan da shugabannin jam’iyyar PDP za su bi dokokin da ke cikin kundin jam’iyyar sau da kafa, su cire son zuciya, to babu shakka za ta zauna lafiya, kuma za ta iya cimma nasara a kan abubuwan da ta sa a gabanta. Saboda haka, muna kira da babbar murya a kan kowane dan jam’iyyar PDP da ya zo ya ba da tasa gudunmuwa domin ciyar da ita a gaba, sannan ya kamata ku daina zarge-zargen juna a kan matsalolin da ke cikin jam’iyyar ko ‘ alakanta matsalar ta da umarnin wata jam’iyya ke bayarwa. Ya dace ku yi abin da zai ciyar da ita gaba wajen zaunawa da kowane bangare domin gano inda matsalar take domin warwareta sannan mu zama masu bin doka da oda a duk sharuddan da dokokin da jam’iyyar ta shimfida. Hakika idan aka yi haka za mu ga ci gaba da sauye-sauye a cikin tafiyar nagode.
Daga Abdulsalam Muhamed Lema Tsagem, Jihar Katsina    08038792668 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. .

Barka da zuwa Shugaba Buhari

Edita na shigo wannan fili ne domin in bi sahun milyoyin ‘yan Najeria wajen mika sakon ban-gajiya ga Shugaban kasarmu Muhammadu Buhari, dangane da dawowarsa gida Najeriya daga birnin Landon na kasar Birtaniya, inda aka duba rashin lafiyar dake damunsa ta ciwon kunne.  “Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai.“ Hakika wannan ya kawo karshen dukkan wani ce ce-ku ce da aka sha fama da shi a kasar, dangane da rashin lafiyar shugaban kasa, Inda ma har wasu mutane makiya Najeriya ke yin mummunan fata ga shugaban kasar a lokacin wannan tafiya. “To yanzu dai karya ta kare bori ya kar boka“. Shugaba Buhari dai ya dawo Najeriya lafiya, kuma mu talakawa a har kullum fatanmu shi ne Allah ya kara masa lafiya da nisan kwana, domin ci gaba da gudanar ayyukan alheri ga kasar mu.
Daga Isah Ramin Hudu Hadejia. 08060353382 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

’Yan majalisa ba mu yarda ba
Yunkurin ’yan majalisun dattawan Najeriya na samar da dokar kariya daga tuhuma da kuma fansho na tsawon rayuwa ga shugabannin majalisar abin Allah waddai ne, ganin yadda zuwa yanzu ’yan majalisun sun gaza wajen samar da dokoki da za su taimaka wajen inganta rayuwar talakawan da suka zabe su, amma kuma sai ga shi suna neman yi wa shugabanninsu katangar karfe daga fuskantar tuhuma, da kuma samar musu da kudin fansho na har karshen rayuwarsu, alhali talakawa na cikin mawuyacin halin tsadar rayuwa. Wannan ya kara tabbatar mana da cewa galibin ’yan majalisun kawunansu kawai suka sani. Hakika  mu talakawa muna  Allah wadai da wannan yunkuri, kuma muna jan hankalin ’yan majalisar wakilai da kada su goyi bayan wannan yunkuri. Sannan su sani akwai ranar kin dillanci.
Daga Mahmud Salihu kauran Namoda, mataimakin sakataren kudi na kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Zamfara. 07067557586 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. .

’Yan kasuwa a ji tsoron Allah
Salam Edita ina maka fatan alhairi tare da dukkan ma’aikatan gidan jaridarmu mai farin jini da tarin albarka ta Aminiya.  A yau ina so ka ba ni dama na nuna bakin cikina kan yadda ’yan kasuwarmu suke amfani da wannan wata na Ramadana suna ta kara wa kaya kudi da sunan samun riba mai yawa, to su sani arzikin da Allah ya ba su ba ya fi son su da kowa ba ne aka ba su, an ba su ne don nuna mulkinSa da buwayarSa.  Daga karshe ina kira gare su da su ji tsoran Allah da ranar karshe, su  daina tsawala wa al’umma da sunan samun riba. Domin Annabi sallallahu alaihi wasallam ya ce, duk wanda ya kuntata wa al’ummata to baya tare da ni.’ Don haka idan kunne ya ji gangar jiki ta tsira.
Daga Muhammad Ahmad Idris Kabuga Kano 08069006931 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
Uwargidar shugaban kasa ta kyauta
Ku ba ni dama in jinjina wa uwar gidan shugaban Nijeriya. Aisha Buhari. Dangane da aike wa da kayan tallafi da ta yi zuwa jihar Borno. Hakika wannan abin yabawa ne.  Zan yi amfani da wannan dama wajen jawo hankalin masu hannu da chuni da su yi wa Allah da ManzonSa su taimaka wa irin wadan nan bayin Allah ko su ma za su samu sa’idar rayuwa kamar kowa. Domin a gaskiya ‘yan gudun hijira suna bukatar taimako. Domin kuwa su ma ba’ a son ransu hakan ya kasance da su ba, duba da abun da Allah ya kaddara sai ya auku. Daga karshe nike addu’ar Allah ya kawo musu saukin wannan lamari. Amin summa amin.
Daga: Sani Mohammed Chindo. 08030918931 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
Kira ga Shugaba Buhari
Assalamu alaikum, tsokacina shine dawowar Shugaba Buhari daga jinya da fatar Allah ya kara masa lafiya. Kana kiranmu gareka shi ne da ka shiga office ya kamata ka mayar da hankali kan yadda za a shawo kan matsalar karancin abinci da muke fama da shi sanadiyyar rufe kan iyaka da ka ba da umarnin yi. Ya kamata a sake lale, al’umma na cikin tsadar rayuwa fa! Daga Hafizu Balarabe Gusau This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.


A taimaka wa manoman Yobe
Assalama  alaikum.  Edita  Don  Allah  ka ba ni  dama  in yi  kira ga gwamnatin  tarayya  da ta  taimaka  ta kawo wa  manoman  Jihar  Yobe irin  shinkafa  ta  Zamani,  kamar  yadda  aka  raba wa  al’ummar  Jahar Kebbi . Saboda  a wanan  lokaci ne  kogin  Jama’are  da  Hadejia  yake yaduwa  a  sassan  jihar. Da fatan  gwamnatin  tarayya  ta ji wanan  bukata ta  Manoman  Jihar  Yobe.  Daga  Garba  Sabiyola  Sa’idawa, Gashu’a  Jihar  Yobe  08096284154 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Masu kudi ku taimaka wa mabukata
Edita yau so nike in karkata hankalina wajen yin kira ga masu kudinmu, da su guji musayar kyaututtuka a tsakaninsu a cikin wannan wata mai alfarma, kamar yada muka saba gani yana faruwa abaya. Su sani mafi kyautatuwar kyauta ita ce kyautar da aka bayar da ita ga mabukaci. Da fatan za ku himmatu wajen taimaka wa bayin Allah mabukata da suke cikin kuncin rayuwa a wannan wata mai alfarman.  Daga  Muddassir Muhammad Tafawa balewa  This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
Jinjina ga Aminiya
A bisa yadda suke nishadantar da mu da labarunsu na yau da kullum. A gaskiya duk ranar Juma’ar da ban karanta Aminiya ba, ba na jin dadi. Daga Adamu Musa Gimba Ningi This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.


Tambaya ga Aminiya
Assalamu alaikum. Aminiya wai mai yasa ba a samun labarain ku a shafin facebook ne kamar irin su bbc hausa da rariya da sauran su? Daga  This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. .

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited