Gwamnoni sun nuna gazawar biyan albashi
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Gwamnoni sun nuna gazawar biyan albashi

Editan Jaridar Aminiya, ka ba ni dama in yi bayyana fahimtata kan yadda gwamnonin mu suka nuna gazawa wajen biyan albashi. A gaskiya ina mamakin irin yadda Gwamnonin Najeriya,  musamman na Arewa maso Gabas,  ganin yadda gwamnatin tarayya ta ware musu tallafi na musamman domin biyan albashi a yankunansu,  amma hakan ya ci tura.  Wata sanarwa a kwanan baya da ta mamaye jaridu da gidajen rediyo, ta yi magana a kan makudan kudin da shugaban kasa ya ware,  duk domin ganin gwamnoni sun biya albashi a jihohinsu,  sai ga shi shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.  Ina kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya dauki mataki na musamman a kan duk gwamnan da ke neman dakushe masa tagomashin mulkinsa.  Don wannan tamkar nuna gazawar gwamnatinka ne, ganin yadda  sallah ta karato, amma talaka ya kasa gane bambancin Shugabancin PDP da na APC Canji. This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. .

Jinjina ga Aminiya
A bisa yadda suke nishadantar da mu da labarunsu na yau da kullum. A gaskiya duk ranar Juma’ar da ban karanta Aminiya ba, ba na jin dadi. Daga Adamu Musa Gimba Ningi This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Tambaya ga Aminiya
Assalamu alaikum. Aminiya wai mai ya sa ba a samun labaran ku a shafin facebook ne kamar irin su bbc hausa da rariya da sauran su? Daga  This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. .

Ban goyi bayan Sanata dansadau ba
Edita kai tsaye ban goyi bayan Sanata Sa’idu Muhammad dansadau ba, ganin tunaninsa daya da masu cewa “in jifa ta wuce kansu to ta fada kan kowa ma”. Domin ya yi kira  ne a kan ‘yan uwansa ‘yan dansadau da lamarin ya fi shafa kacokan!  Duk da cewa ya yi abin da ya dace, amma sai dai kash! Tun shekarun baya ya kamata ya ci gaba da irin wannan fafutikar ganin an magance wannan matsalar, ba sai yanzu da aka yi wa al’ummar yankin mummunar barna ba. Wanda kamarsa da  irin matsayin da ya rike da ba wani mai fada a ji a wannan yankin tamkarsa. Da ya jajirce da yanzu talakawan wannan yanki sun samu sa’ida daga wannan ibtala’in rayuwa da suke ciki a halin yanzu. Tunda ya farka to Alhamdulillahi. Ya kamata ya yi amfani da kalaman da suka cancanta ba wai shiga kafafen yada labarai, da rubuta wa shugaban kasa takardar neman sanya wa Jihar Zamfara dokar ta baci, ba. To me ya danganta maganar dokar-ta-baci da halin da manoma suke ciki? Don haka muna kira ga gwamnatin tarayyar ta kara kokarin kawar da barayin Shanu da suka addabi Jihar Zamfara. Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. (Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar Muryar Talaka Reshen Jahar Zamfara. 08069804496

Goyon baya ga Sanata dansadau
Edita,ina so ka ba ni dama domin in bayyana ra’ayina na goyon baya dangane da kiran da dattijo sauran mazan- jiya, masu fadar gaskiya komai dacinta, wato tsohon Sanata Sa’idu dansadau, ya yi ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya kawo kantoman riko a Jihar Zamfara (state emergency).Tabbas ina goyon bayan wannan shawara. Kuma ina fatan shugaban kasar mu mai adalci zai share mana hawayenmu. Domin Gwamnatin AbdulAziz ba ta nuna damuwarta game da halin kunci da talakawan jihar ke ciki, musamman matsalar satar shanu da ke addabarmu.Da a ce,su ma malaman addini da iyayenmu sarakuna da sauran dattawan jihar za su yi irin wannan kiran,da tabbas tuni Gwamnatin A.A.Yari ta shiga taitayinta, kuma ta kara mayar da hankali wajen kara samar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama’arta. Daga Nura Sule Jangebe, dan kungiyar Muryar Talaka a Jihar Zamfara.(This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. ) 07051184738
Gwamna Masari ya shimfida ayyuka
Juma’ar da za tai kyau tun daga Laraba ake ganewa! Na shigo da wannan kalami ne domin yin godiya ga Allah bisa ga samun adalin gwamna a jiharmu ta Katsina, watau Aminu Bello Masari. Babu shakka a shekara guda gwamnan ya samu nasarori na a zo a gani, inda kawo yanzu al’ummar Jihar Katsina ke ta godiya da ala’sambarka. Domin kuwa irin manyan ayyukan da ya shimfida babu abin da  za mu ce sai dai Allah ya maimaita mana. Daga karshe muna kara addu’ar Allah ya taimaki Gwamnatin Bahari da ta sauran jihohinmu amin. Daga Mainasara Nasarawa Funtuwa. 08034208356 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Kira ga Hukumar NCC
Ina so yin amfani da wannan damar don  kira ga Hukumar Sadarwa ta Najeriya (Nigerian Communications Commission) da cewa yakamata su sa kamfanonin MTN, AIRTEL, GLO, ETESILATE, da ta samar wa yan’ Najeriya ingantaccen tsarin kiran waya ko isar da sako, wato “serbice,” a Turance, ta yadda ’yan Najeriya za su samu damar yin waya mai kyau, ba wai kamar yadda yake yanzu ba, sai ka kira mutum a waya, amma ba za ka ji shi yadda ya kamata ba. Kuma ana cinye wa mutum kudi, kai a wasu lokutan ma, rashin kyawun serbice din ma, sai ya sa ka yi ta neman mutun ba za ka iya samun sa ba.  Kamfanonin waya na na cin karen su ba babbaka, kuma cajin da suke yi wa jama’a a duk minti daya, ya yi yawa sosai. Saboda haka muke so Hukumar NCC ta sa su yi gyara tare  da saukin cajin mutane kudi. Daga Muhammad Babangida Kiraji Gashua 08029388699 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Gwamnatin Kebbi a dubi karkararmu
Assalamu alaikum Edita don Allah ka isar min da sakona zuwa ga Gwamnatin Jihar Kebbi cewa, mu ’yan Jihar Kebbi muna nan mun zura ido muna sauraron ko wane aiki za ta fara yi wa al’ummar jihar ta, don ganin cewa har yanzu ba mu ji inda ta fara wani aiki ba, kamar yadda takwarorin ta na wasu jihohi suka fara aiki, musamman a yankunan kananan hukumomi da karkara. Daga karshe ina mai yi mata fatan Allah ya ba ta ikon cika alkawarin da ta dauka yayin da take yakin neman a zabe ta amin. Daga Nasiru Musa Maiyama Jihar Kebbi 08062206733/07066516733 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Makiyaya da manoma a zauna lafiya
Salam. Edito ka ba ni dama in yi kira ga manoma da makiyaya, da su yi wa Allah su zauna lafiya da juna don masu iya magana kan ce zama lafiya ya fi zama dan sarki. Daga: Sani Mohammed Chindo. 08030918913 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

A duba zargin likitoci
Muna kira ga Shugaba Buhari da Gwamnan Jihar Barno ya kamata su gaggauta binciken halin da ’yan gudun hijira suke ciki, ganin yadda kungiyar Likitocin Duniya, wato nagari na kowa suka yi zargin cewa a kullum ana samun mutane da ke mutuwa a dalilin yunwa. Daga Naziru Abubakar  Sabo Gusau 07033565999 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. .

Kira ga Saraki da mataimakinsa
Assalamu alaikum. Hakika gurfanar da shugabannin majalisar dattawa da aka yi gaban kuliya manta sabo, shi ya nuna an samu canji a bangaren shari’ar Najeriya. Sai dai anya ba akwai lauje cikin nadi ba? Ya kamata Saraki da mataimakinsa su yarda kwallon mangoro su huta da kuda haka nan. Daga Hafizu Balarabe Gusau 07035304499 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.Addu’a ga dangote
Allah Yasa tallafin Naira biliyan biyu da Alhaji Aliko dangote ya bayar ga ’yan gudun hijira da ke zaune a sansanin  Jihar Barno ya kai ga wadanda aka yi domin su. Da fatan wasu sauran attajiran Najeriya da ma na kasashen duniya za su yi koyi da shi. Daga Alh.
Umar Foreber  Gashua. This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited