Fatan alheri ga ’yan jarida
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Fatan alheri ga ’yan jarida

Salam   Edita barka   da aiki. Ya ya ibada? Allah ya sa mu dace, Ya samu   cikin bayinSa  wadanda zai   ’yanta a wannan  wata na  Rammadan amin. Edita ina so ka ba ni  dama in mika   godiya ta da kuma fatan   alheri a gareku   ’yan jarida.  A gaskiya in ba don ku ba da yawancin ’yan Najeriya ba za mu san abin da yake wakana ba  a kasa  baki daya ba. Allah ya saka muku da alheri.  Don haka ina kira ga matasa ’yan uwana, wadanda za ka ji su  suna cewa   wai Gwamnati  Baba Buhari   ita ce ta sa  jama’a cikin mawuyacin hali,  ina so   su rika  karanta  jarida ko kuma  su rika sauraren  shirin idon mikiya na gidan  rediyon bision  FM  da ke Abuja, ta yadda za su fahimci irin barnar da aka yi  a Najeriya.   Allah ya kara   kawo mana zaman lafiya  da ci gaba a Najeriya  baki daya.
Daga Mamman S. dan Charanchi mazaunin Deidei Abuja 08119606614

Tir da harin Madina!
Innalilahi wa’inna’ilaihi rajiuun.  A gaskiya harin da aka kai kasar Saudiyya kusa da masallacin Fiyayyen halitta abin Allah wadai ne,  Ya Allah ka kare addininKa ka yi hukunci ga wadanda ke nuna masa kyama. Daga Mudassir Maishayi Ningi. 08169139393

Gwamna Masari a gyara mana hanya
Don girman Allah Gwamnan Jihar Katsina ya taimaka a idan aikin hanyar da aka dakatar daga Gwarandama zuwa Babban-mutum a karamar Hukumar baure. Domin mutane na wahala. Daga Ibrahim Katsina Jihar Katsina

Addu’a ga IBB  
Assalam edita don Allah ka ba ni dama domin in nuna murnata game da dawowar IBB kasata lafiya. Kuma masu yi masa fatan mutuwa, to su sani kul nafsi za ikatul mauti.’ Dan haka ta Allah ba taku ba. Daga dan Bukur Yaro.08162565182

Kira a Gwamnatin Zamafara
Gwamnatin Jihar Zamfara ki kara azama, ki cika alkawarin samar da tsaro ingantace a jiha baki daya muna cikin yanayin rashin tsaro. Daga Hafizu Balarabe Gusau 07035304499 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.  

Ga shugabannin APC   
Salam Edita ina so a isar min da sakona ga duk wani da’babbe na jam’iyar APC’ ya kamata a hada kai a fitar da talakawan kasar nan cikin mawuyacin halin da ake ciki na tsadar rayuwa. Daga Hon-Isma’il Alkyabba Funtuwa

A rage yawan rantsuwa
Aminiyya Edita. Ina kira ga mutane da su daina yawan rantsuwa da abin da Ubangiji Ya yi. Daga Saminu Mayentea Unguwa Alkali Batsari,08036773485

Godiya ga Sarkin Musulmi
Assalamu alaikum. Aminiya don Allah a mika min sakona ga fadar Sarkin Musulmi.Muna godiya ga Maimartaba Sarkin Musulmi Saboda Jajircewar da yayi wajen kira ga gwamnati a bude kan iyaka. Allah Ya kara masa lafiya. Allah Ya kara girma. Dalilin wannan maganar da ya yi Allah dilolin shinkafa na Kano sun rage Naira 2000, wasu har Naira 2500  duk buhu daya. Suna tsoro kada Gwamnati Ta bude boda su yi asara Suke So Tahannunsu Takare. Allah Yasaka mai Da Alkairi Amin. Daga 08125555569 09033322295

Kira ga Miyetti Allah
Zuwa ga kungiyar Miyetti Allah. To fa aiki ya asaki in gaskiyakike domin ga abin tausayi nan gabanki. ’Ya’yanki mata wasu kauyukansu, an kore shanunsu an kashe mazajensu yaran su ba su yi karatu bap; ba sa yin noma ba su iya kasuwaba. Wasu matan sun zare, zararrun nan ki kula da su. Allah ya kyauta. Daga Lawan dankado Bulelkore Kaita Jihar Katsina 08076905760

Shugaba Buhari a kara himma
Salam muna kira ga Maigirma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki mataki kan azzalumai masu bata masa mulki. Don idon kowa a kansa yake mun san abubuwa sun yi yawa a kasar, amma dai ya kara himma. Muna yi  masa addu’a Allah ya kara masa lafiya. Daga Isah Dilwaala Abuja 0805 904 4449

Dangote mutane na jira a Maiduguri
 Dangote mutanen Maiduguri suna nan suna jiranka. Domin ka sa a cire hatimin (stamp) na buhun sumintinka guda 5 a sa a cikin ambulam tare da lambar waya ga duk wanda ya yi, ya kai bankin Access. To mutanen Maiduguri sun ji shiru. Shin ko ba gaskiya ba ne? Idan ba gaskiya ba ne to a yi bayani ga mutane kowa ya cire rai. Daga Ibrahim Ahmad Maiduguri

Jinjina ga Buhari
Asslamu.alaikum. Don Allah Edita ka ba ni dama a wannan jarida tamu mai yawan, albarka duk da na sha rubutowa,  amman ban taba gani ba. Don haka zan yi amfani da wananan  dama inyi kira ga jama’ar kasar mu  Najeriya da mu yi koyi da halin (M.S.A) na  hakuri kada mu manta da halin da muka fito na rashin kwanciyar hankali da fargaba. Fara daga masallaci, zuwa Coci da kasuwa. abin bai tsaya nan ba, ka yi har makabarta ma an kai hari  aka wayi gari ba haka, idan aka yi la’akari da haka to ashe ko an samu sauki da fatan Allah ya sa mu ci gaba da samun haka. Amin. Daga Umar Maiungwa, Kontagora, Jihar Neja.09056058182

Barka da shan ruwa
Assalamu alaykum. Barka da shan ruwa. Da fatan Allah Ya karbi ibadummu amin. Daga Laminu Aliyu L. Gurbin-bore

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited