Martani ga kungiyar ceton ’yan matan Chibok
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Martani ga kungiyar ceton ’yan matan Chibok

Salam. Editan Aminiya a yau ina so ka ba ni dama domin mayar da martani kan masu fafatukar ceto ’yan matan Chibok.  Haba ’yan kungiyar Bring back our girls masu fafatukar ceto yan matan chibok da yan ta’addan boko haram ke garkuwa da su ya kamata ku sani, ita gaskiya daya ce, kuma daga kinta sai bata kada ku manta da yadda gwamnatin baya ta rika yi muku alkawarin karyar cewa ta san inda ’yan matan Chibok suke, kuma za ta ceto su, amma ta kasa ceto su. Tunda Shugaba Buhari ya fadi cewa bai san inda matan suke ba, domin da idan an san inda suke za a ceto su da ransu, sai kuka fara tada jijiyoyi wuya, kuna kumfar baki, wai ya yi muku alkawari, amma ya saba. To, idan har ba ku yaba wa Shugaba Buhari da jami’an tsaron da ke fagen daga ba, kan yadda suke samun galabar fatattakar ’yan ta’addar boko haram ba, ina ba ku shawarar ku yi damara idan kun san inda suke ku ceto su da kanku, mu gani idan har da gaske kuke fafutikar ganin an ceto ’yan matan Chibok, ba ku tsaya Abuja kuna cika baki ba. Daga karshe muke yi wa Shugaba Buhari addu’ar Allah ya taimake shi Ya ba shi ikon sauke nauyi, tare da alkawarin da ya yi wa al’ummar Najeriya.  Daga Naziru A. Sabo Gusau, Sakataren Kudi na murya Talaka Jihar Zamfara 07033565999 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Shugaba Buhari barka da sallah
Aminiya  yar amana  don Allah  ku mika min  sakon  barka  da sallah  ga  jagoran  talakawa,  kuma  shugaban  kasar  tarayyar  Najeriya  Muhammadu  Buhari  da kuma  al’ummar  Musulmin duniya.  Daga  Musa  unguwar Maiyasin,  danja Jihar  Katsina  08060611124.   

Rikicin Sudan ta Kudu
Ba da umurnin tsagaita wuta da bangarorin Shugaban Sudan ta Kudu da Mataimakinsa, suka yi ga magoya, bayan su abin a yaba ne. Allah ya sa hakan ya kawo karshen duk wani tashin hankali da ke faruwa a kasar. Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi, Tashar Bagu Gusau. 08069807496 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
Kira ga Shugaban kasa da gwamnoni
Assalamu alaikum. Edita ina yi maka barka da hutun sallah’ ina so wannan sakon ya isa fadar gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi,’ kai har ma daukacin masu rike da madafun iko.’ A tunanina bai kamata a hana shigo da abinci a kasar nan ba, alhali ba mu noma namu ba! Bai kamata a rika kiran gwamnati ba ta da kudi, alhali ba a yin wata daya gwamnoni da shugaban kasa ko ‘yan majalisa wani cikin su bai tafi kasar waje ba, ko kyauta ake kai su ne? A wasu jihohi sai a yi wata biyar ba a biya malaman makaranta albashinsu ba, wanda duk kudin ba za su wuce cefanen gidan gwamna na kwana biyu ba. Don haka ina kira ga shugaban kasa ya daure ya bari a shigo wa talakawa masoyansa da abinci, su kuma gwamnoni su rage wa kansu da ‘yan majalisu albashi, domin a biya malaman makaranta in dai da gaske suna so a samu canji a zahiri.’ Daga lsma’il Alkyabba Funtuwa  

Muna farin ciki da auren Masallacin Abuja
Hakika bullo da wata hanya ta hada auratayya tsakanin al’umma da wani Massallaci a Abuja ya yi, ake cika Sharudda kafin a kulla auren abu ne mai kyau. Don Annabi ya ce ku yi aure, ku hayayyafa don ranar gobe alkiyama in yi alfahari da ku.’ Tabbas mu al’ummar Najeriya mun yi farin ciki kwarai da gaske da irin samun wannan lamari. Kura gaban ku masu dabobi ina magana ne a kan mazan ban da matan. Allah ya sa mu dace. Daga Alhaji Umar Foreber Gashuwa 08108003333 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

A dawo da kwabbai da sulalla
Daina cudanya  da kudin karafa a hannun jama’a na Naira daya da Naira biyu  ya sa wasu ’yan kasar ba su ma san akwai wadannan nau’in kudi a cikin kudin kasar ba. Ya kamata a ce mun maido da martabar su, ta hanyar yin amfani da su, musamman a Arewacin Najeriya. Domin a nan akwai sauran saukin rayuwar da za a iya amfani ko sayen abin kasa da Naira 5, kuma yin hakan zai taimaki tattalin arzikin mu. Don haka ya kamata ’yan kasuwar mu su inganta yin amfani da kudin sulalla, ta hanyar karbar su a duk lokacin da aka ba su. Daga Habib Ibrahim Central Market Katsina 07038653949 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
Kan rikicin Juba
barkewar sabon rikici a birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu a daidai wannan lokaci da ake neman ganin yarjejeniyar sulhun da aka cimmawa tsakanin bangaren Shugaba Salba Kiir da na mataimakinsa Reik Machar ta samu gindin zama. Wani abin Allah wadai ne, muna kira ga wadannan bangarori da su ja wa magoya bayansu kunnuwa, su daina kai wa junansu farmaki, matukar dai ba shugabannin ne ke rura wutar wannan rikici ba. Kuma ya kamata Majalisar dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afirika su yi duk mai yiwuwa wajen ganin kasar ba ta sake komawa cikin yakin basasa ba. Allah ya zaunar muna da kasashenmu na Afirika lafiya da ma duniya baki daya.
Daga Mahmud Salihu kaura-Namoda, Jihar Zamfara. 07067557586 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Kukan Hadejawa ga Gwamnatin Jigawa
Hausawa dai sun ce babu wani dare da jemage bai gani ba, komai daren da ka yi za ka iske karen unguwarku idonsa biyu. Mai girma Gwamnan  Jihar Jigawa ya kamata a ce titunan cikin garin Hadeja an kammala su, idan ma ba a kammala ba, to a ce aiki ya zo karshe. Sai nike ganin kamar aikin Hadejia ne ke da wannnan matsalar. Idan kamfanin da suke aikin ba zai iya ba sai a nemi wani. Abin da nike tsoro shi ne ka da a ci mu da bagu, ko ina ka je ka ji ana “Gwamnan Hadejawa,” amma ga shi ana neman cinmu da bagu. Ayyukan da za ayi mana sai jan ciki ake. Tsohuwar gwamnati haka ta bar mu da auwon tituna ba tare da ta yi ba. Ba mu da isassun kwalbati, da zarar an tafka ruwa sai ya rika shiga gidajen mutane, ga matsala ta kogi yadda a duk shekara takan zame mana barazana ga amfanin gonarmu, abubuwan dai da yawa. Mai girma gwamna ba ma so ayyukan da aka yi mana alkawuransu a ce za a sake yi mana kamfen da su. Fatanmu a cika su. Allah ya taimaki Gwamnatin Jihar Jigawa da ta Baba Buhari amin. Daga Nasiru Kainuwa Hadejia 08100229688 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

dangote abin koyi ne ga attajiran kasa
Edita na rubuta wannan wasika ne, don jinjina ga Alhaji Aliko dangote, saboda kamfaninn  da yake budewa a Najeriya. Hakika yana taimaka wa tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa, saboda mutane masu dmbin yawa ne suke samun aikin yi. Kuma Gwamnatin Najeriya tana samun haraji mai dimbin yawa, wanda hakan yana mutukar tallafa wa tattalin arzikin kasa ya bunkasa. Dadindadawa, yana da FOUNDATION, wadda yake tallafa wa mararsa karfi, kamar yadda na ga yana tallafa wa ‘yan gudun hijirar Arewa maso Gabas. Yanzu haka ma yana kokarin kafa matatun man fetur da zai samar wa ‘yan Najeriya masu yawa aikin yi, kuma matatun man da zai samar za su samar wa  Najeriya  wutar lantarki da ya kai MEGAWATTS dubu shabiyu (12  Megawatts). Hakan ya sa ina ganin idan muka duba irin abubuwan da Alhaji Aliko dangote yake yi a Najeriya. Hakika ya kamata a jinjina masa, kuma ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga sauran attajiran na kasar nan su yi koyi da shi, kuma irin wannan kokarin da yake yi, ya nuna a fili cewa Alhaji Aliko dangote mai kishin kasa ne. Ina yi masa addu’a, Allah ya kara buda masa, kuma ya saka masa da alkhairi. Allah ya bunkasa Najeriya. Daga Muhammad Babangida Kiraji, Gashuwa, 08029388699.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited