A shigar da matasa cikin gwamnati
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

A shigar da matasa cikin gwamnati

Editan Aminiya tabbas ya dace matasa a fara damawa da su a majalissar dattijai, wanda hakan ne zai bai wa matasan gogewa ta musamman a harkokin mulki. Baya ga haka matasan za su fi mayar da hankali ga lamuran matasa sabanin dattawa. Najeriya kuma kasa ce da take da tarin matasa masu yawa, don haka yana da kyau a ce sun samu wakilcin matasa a majalisa, musamman idan na tuna wani karin magana da ke cewa “Ciwon ‘Ya mace na mace ne.” Don haka matsalar matasa sai matasa.
Ina goyan bayan kungiyoyin matasa da suka bukaci a rage shekarun wadanda ke samun damar zuwa zauren majalissunmu guda biyu. Saboda a komai ana bukatar matasa, akwai gudunmawar da za su iya bayarwa kamar yadda idan matasa ne zalla da matsala haka nan idan dattawa ne zalla akwai matsala.
Ya Allah ka taimaki Gwamnatin Baba Buhari Ka kara masa lafiya da juriya, Ka ba shi ikon sauke nauyin da ke kansa na mulki; munafukan nesa da na kusa Ya Allah Ka Kare shi daga sharrinsu.
Daga Nasiru Kainuwa Hadejia 08100229688 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Sakonnin waya

Goyon baya ga ’yan Majalisar Zamfara
Tabbas mu al’ummar Jihar Zamfara musamman matasa muna goyon bayan ’yan majalisa bisa yunkurin su na tsige Gwamnan Zamfara, wato Abdulaziz Yari Abubakar daga kujerarsa, domin babu wani abin kishi da da ya yi wa talakawansa face yawo a cikin jirage, ba ya Abuja ba ya kasashen waje, amma sai dai kash su kansu ’yan majalisar ba da gaske suke yi ba. Domin wannan tayar da jijiyoyin wuya da suke yi ba don talaka suke yi ba, sai dai don ya hana su kudi ne kawai, amma da don halin da talaka yake ciki da wallahi tallahi da tuni sun tsige A.A YARI daga karagar mulkin gwamna. Fatarmu dai Allah ya ba mu shugabani nagari a Jiharmu ta Zamfara masu kaunar mu da son ci gaban mu albarkar Annabin rahama S.A.W.
Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau Sakataren Kudi na kungiyar Muryar talaka, Jihar Zamfara 07033565999 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
 
Kira ga ’yan Majalisar Zamfara
Don Allah ku ba ni dama in bai wa ‘yan Majalisar Jihar Zamfara shawarar su ci gaba da fafutukar da suke yi, matukar a kan hakkokin talaka suke takun saka da Gwamna A A Yari na Jihar Zamfara, to su ci gaba da kokarin kare martabar talakawan da suke wakilta, har su kai ga nasara.
Daga Hafizu Balarabe Gusau This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Babu matsalar albashi a Katsina
Mafi yawancin Jihohin Najeriya albashi na yi masu ‘batan dabo, wato da kyar suke yin albashi, sakamakon matsin tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta. Cikin ikon Allah sai ga shi yanzu jiharmu ta Katsina ta magance wannan matsala cikin kankanin lokaci, inda yanzu haka babu wani ma’aikaci da ke bin Gwamnatin Masari albashi. Hakika wannan wata babbar nasara ce garemu. Don haka muna kara godiya ga Allah da ya ba mu adalin gwamna, wato Aminu Bello Masari, Allah ya yi mana jagora amin.
Daga Mainasara Nasarawa Funtua. 08034208356 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Gwamnatin Turkiyya ki hukunta sojoji
Gwamnatin kasar turkiyya ya kamata ki hukunta sojojin da sukayi yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a makon da ya gabata daidai laifin da suka aikata, ba tare da amfani da ramuwar gayya ba. Domin yin ramuwar gayya tamkar rashin gode wa Allah ne, wanda shi ne Ya kii bai wa sojojin nasara.

Daga Mahmud Salihu kaura Namoda, Jihar Zamfara. 07067557586 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Taron hadin gwiwa a Afirka ta Kudu
Allah ya sa wannan taron hadin gwiwar tsakanin Afirka ta Kudu da Najeriya, wajen yakar ta’addanci ya yi tasiri.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08069807496.

Jinjina ga Gwamnati Jihar Adamawa  
A gaskiya Gwamna Umaru Bindow Jibirilla ya yi abin a yaba,  a makon da ya gabata ne. ya kaddamar da gyaran hanyar Shellang,  shekaru da dama ‘yan siyasa sun sha yin alkawarin gyaran hanyar, amma shiru jama’ar garin suke ji, ba a cika alkawarin, sai wannan lokacin Gwamna Umaru Bindow ya share wa mutanen Shellang hawaye,  tabbas hakan abin farin ciki ne da murna ga dukkan mutumin Jihar Adamawa, musamman mazauna karamar Hukumar Numan.
Daga Faisal Muhammad Girei, a Jihar Adamawa. This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Kalubalenku ‘yan majalisa
Hakika matakin da ’yan Majalisar Dattawa suka dauka na yunkurin tsige Shugaba Buhari daga kan mulki za mu iya cewa, haka ya dace, kuma hakan bai dace ba.  Domin idan ka ga ’yan majalisu na babatun tsige shugaban kasa to wallahi yana kawo musu nakasune wajen kudin da suke samu, suna sharholiyarsu amma in dai don talakawa ne su samu saukin kuncin rayuwar da suke ciki ne, to ba za ka ji ’yan majalisu na yunkurin tsige shugaban kasa ba. Don haka ’yan majalisun Najeriya kalubalanku an yi walkiya mun ganku.
Daga Abbakar Lawal Gidan Danmaye a Jargaba 08097627776 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Fatan alheri ga Aminiya
A madadin daukacin ’ya’yan wannan kungiya mai albarka, muna yi wa ma’aikata da shugabanni wannan kamfani fatan alheri.  
Daga kungiyar Matasan Najeriya reshen Jihar Kano. (NIGERIA YOUTH ORGANIZATION KANO STATE CHAPTER ). This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. .

Gaisuwa ga Malam Shekarau
Edita ka isar da sakon barka da salla ga Malam Ibrahim Shekarau. Malam kai ne jagoran jam’iyya a Jihar Kano. A kara kokarin daidaita matasa a kan sahu. Allah Ya sakla da alheri. Amin.
Daga dan Dubai Kabo, 07030675722.

Goyon baya ga ’yan Majalisar Zamfara
Tabbas mu al’ummar Jihar Zamfara musamman matasa muna goyon bayan ’yan majalisa bisa yunkurin su na tsige Gwamnan Zamfara, wato Abdulaziz Yari Abubakar daga kujerarsa, domin babu wani abin kishi da da ya yi wa talakawansa face yawo a cikin jirage, ba ya Abuja ba ya kasashen waje, amma sai dai kash su kansu ’yan majalisar ba da gaske suke yi ba. Domin wannan tayar da jijiyoyin wuya da suke yi ba don talaka suke yi ba, sai dai don ya hana su kudi ne kawai, amma da don halin da talaka yake ciki da wallahi tallahi da tuni sun tsige A.A YARI daga karagar mulkin gwamna. Fatarmu dai Allah ya ba mu shugabani nagari a Jiharmu ta Zamfara masu kaunar mu da son ci gaban mu albarkar Annabin rahama S.A.W.
Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau Sakataren Kudi na kungiyar Muryar talaka, Jihar Zamfara 07033565999 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
 
Kira ga ’yan Majalisar Zamfara
Don Allah ku ba ni dama in bai wa ‘yan Majalisar Jihar Zamfara shawarar su ci gaba da fafutukar da suke yi, matukar a kan hakkokin talaka suke takun saka da Gwamna A A Yari na Jihar Zamfara, to su ci gaba da kokarin kare martabar talakawan da suke wakilta, har su kai ga nasara.
Daga Hafizu Balarabe Gusau This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
Babu matsalar albashi a Katsina
Mafi yawancin Jihohin Najeriya albashi na yi masu ‘batan dabo, wato da kyar suke yin albashi, sakamakon matsin tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta. Cikin ikon Allah sai ga shi yanzu jiharmu ta Katsina ta magance wannan matsala cikin kankanin lokaci, inda yanzu haka babu wani ma’aikaci da ke bin Gwamnatin Masari albashi. Hakika wannan wata babbar nasara ce garemu. Don haka muna kara godiya ga Allah da ya ba mu adalin gwamna, wato Aminu Bello Masari, Allah ya yi mana jagora amin.
Daga Mainasara Nasarawa Funtua. 08034208356 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Gwamnatin Turkiyya ki hukunta sojoji
Gwamnatin kasar turkiyya ya kamata ki hukunta sojojin da sukayi yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a makon da ya gabata daidai laifin da suka aikata, ba tare da amfani da ramuwar gayya ba. Domin yin ramuwar gayya tamkar rashin gode wa Allah ne, wanda shi ne Ya kii bai wa sojojin nasara. Daga Mahmud Salihu kaura Namoda, Jihar Zamfara. 07067557586 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Taron hadin gwiwa a Afirka ta Kudu
Allah ya sa wannan taron hadin gwiwar tsakanin Afirka ta Kudu da Najeriya, wajen yakar ta’addanci ya yi tasiri.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08069807496.
Jinjina ga Gwamnati Jihar Adamawa  
A gaskiya Gwamna Umaru Bindow Jibirilla ya yi abin a yaba,  a makon da ya gabata ne. ya kaddamar da gyaran hanyar Shellang,  shekaru da dama ‘yan siyasa sun sha yin alkawarin gyaran hanyar, amma shiru jama’ar garin suke ji, ba a cika alkawarin, sai wannan lokacin Gwamna Umaru Bindow ya share wa mutanen Shellang hawaye,  tabbas hakan abin farin ciki ne da murna ga dukkan mutumin Jihar Adamawa, musamman mazauna karamar Hukumar Numan.
Daga Faisal Muhammad Girei, a Jihar Adamawa. This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.
kalubalenku ‘yan majalisa
Hakika matakin da ’yan Majalisar Dattawa suka dauka na yunkurin tsige Shugaba Buhari daga kan mulki za mu iya cewa, haka ya dace, kuma hakan bai dace ba.  Domin idan ka ga ’yan majalisu na babatun tsige shugaban kasa to wallahi yana kawo musu nakasune wajen kudin da suke samu, suna sharholiyarsu amma in dai don talakawa ne su samu saukin kuncin rayuwar da suke ciki ne, to ba za ka ji ’yan majalisu na yunkurin tsige shugaban kasa ba. Don haka ’yan majalisun Najeriya kalubalanku an yi walkiya mun ganku.
Daga Abbakar Lawal Gidan Danmaye a Jargaba 08097627776 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.Fatan alheri ga Aminiya
A madadin daukacin ’ya’yan wannan kungiya mai albarka, muna yi wa ma’aikata da shugabanni wannan kamfani fatan alheri.  
Daga kungiyar Matasan Najeriya reshen Jihar Kano. (NIGERIA YOUTH ORGANIZATION KANO STATE CHAPTER ). This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. .
Gaisuwa ga Malam Shekarau
Edita ka isar da sakon barka da salla ga Malam Ibrahim Shekarau. Malam kai ne jagoran jam’iyya a Jihar Kano. A kara kokarin daidaita matasa a kan sahu. Allah Ya sakla da alheri. Amin.
Daga dan Dubai Kabo, 07030675722.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited