Mene ne bambancin dandalin shirya fina-finai da kulob ?
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Mene ne bambancin dandalin shirya fina-finai da kulob ?

Editan  Aminiya. Ku ba ni dama in bayyana ra’ayina, wanda ya kunshi tambayoyi ga wadanda suke ganin gina dandalin shirya fina-finai na Film billage ne hanyar lalata tarbiyyar al’umma a Arewacin Najeriya.

Shin mene ne bambancin Filmbillage da gidajen casu (Clubs) da ke manyan biranen mu na Arewa, idan ana maganar tarbiyya ne ? Mene ne bambancin Filmbillage da gidajen kallon kwallo, filayen wasanni (Stadium) da babu garin da babu a yankin Arewa idan ana maganar tarbiyya ? Mene ne bambamcin Filmbillage da gidajen ‘yan iska na karuwai da ‘yan koroso ta fuskar tarbiyya ? Idan ka ce Filmbillage zai bata tarbiya. Shin gidajen rawa, gidajen wasanni da gidajen kallon kwallo da muke da su tun da can, gyara tarbiyya suke yi? Idan ka ce Filmbillage zai bata tarbiyya, amma ba ka hana shirya fina-finai a Arewa gaba daya ba. Anya ka kama hanyar gyara tarbiyyar da ‘yan film ke batawa ? Idan ka ce Filmbillage zai bata tarbiya, amma yanzu idan aka je gidanka ba za a rasa fina-finan Hausa ba, anya ba yaudarar kanka kake yi ba, tunda ko ba a gina #Filmbillage ba, ba za a daina shirya fim ba ?
Wai me ya hana mutane bai wa gwamnati shawarar tabbatar da daukar matakan tsaftace masana’antar fina-finan Hausa wajen lalata tarbiyya, da hanyar samun mafita idan an gina Filmbillage? Idan har kishin addinin muke da gaske, da son gyara tarbiyya da kawo karshen lalata tarbiyya a wannan shiyyar kasar, ya zama wajibi a rufe gidajen kallo, filayen wasannin da Musulunci bai ce a yi ba, gidajen rawa da casu, gidajen koroso da karuwai, kamar yadda za ku ce wasu daga cikin wadannan na da amfani, haka film akwai inda yake da amfani duk da cewa akwai tarin kura-kurai.
Daga Comrade Usman Bin-Affan Damaturu a Jihar Yobe. This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited