Saqonnin waya
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Saqonnin waya

Kira ga Shugaba Buhari
Edita ina rokon Shugaba Muhammadu Buhari kan ya taimaka ya bude kan iyakokin mu don a shigo da abinci ko da na wata daya. Yin hakan na da fa’ida domin talakawa ne suka zabe shi, kuma su ke cikin kunci. Saboda ya zama wajibi ne a samar da hanyar samun sauki a rayuwar talakawan kasar nan. Kuma kyautata rayuwar al’umma da yi musutarbiyyar bin doka da oda za ta bambanta Gwamnatin APC da ta PDP. Daga Alhassan Yaryasa, Jami’in Hulda da Jama’a (PRO) kungiyar Wanzaman Kano. 08086799248/08093637754.


A tausaya wa talaka
Don Allah Edita ka ba ni dama in tofa albarkacin bakina a kan matakin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dauka na dakatar da shigowa da abinci, musamman shinkafa ta wadansu hanyoyin, amma mu kuma ana daukar namu abinci kamar masara da sauran su ana fita da su wasu kasashen ketare. Wane alfanun ke cikin hakan? Kuma mece ce fa’idar yin hakan a gwamnatance? Ina kira ga mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya duba wannan lamarin da idon basira, kuma ya canza shawara a kan matakin da ya dauka a nan bangaren, domin talaka ya samu sa’ida.
Daga Adamu Aliyu Amo, Katsina. 08034630083 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. .


A kai zuciya nesa ’yan Jigawa
Mafi yawancin Jihohin Najeriya albashi na yi masu ‘baSakamakon wata arangama da aka yi tsakanin tawagar Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar da magoya bayan tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Jigawa a Jam’iyar PDP, Malam Aminu Ringim. Wannan taho mu gama ta faru ne a garin Ringim, sakamakon halartar daurin aure da mai girma gwamna ya yi. An yi artabun ne a kofar gidan Aminu Ringim a lokacin da tawagar gwamna ta zo wucewa. Abin da zan ce da ‘yan PDP ya kamata ku dangana, idan har zafin kayin da aka yi muku ne bai sake ku ba. Yana da kyau ku huce, ku daina tsokanar fada. Ku kuma ‘yan jam’iyyar APC, ku daina takalar fada kasancewar ganin ku ne da gwamnati, ku sani da cewa in yau ku ne gobe sai labari. Da a ce ba wa’adi da ba mu kawo karshen mulkin PDP ba. Ni dai ba a gabana komai ya faru ba, amma ina da labari daga kowane bangare, na kuma kasa gane waye mai gaskiya, waye marar gaskiya. Fatanmu a zauna lafiya, shugabanni ku mayar da hankali kan lamuran talakawanku.
Daga Nasiru Kainuwa Hadejia 08100229688 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.


A dubi mutanen Tiga
Edita ka mika kukan mu ga Mai girma Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje, kan lallai ya dubi halin rashin tsaro da mutanen Tiga ke ciki. Domin har asibiti an shiga an sace mutane. Allah Ya zaunar da kasar mu lafiya, yak are mu daga fitintinun da ke tasowa.Daga Ahmad Tiga 08068643445.


Godiya ga Shugaba Buhari.               

Edita mai albarka don girman allah, ka ba ni fili in nuna godiyata ga Shugaba Buhari bisa ga nadin da ya yi wa matashiya Hadiza Bala Usman na Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa. Nadin ya kara nuna gwamnati na tafiya da matasa. Muna yi mata fatan alheri, muna ba ta shawara da ta kara sanya kishin kasa a zuciya, kuma ta kawo sababbin dabarun da za su taimaki gwamnati wajen kara inganta tattalin arzikn kasar nan.
Daga Amiru Isah Bakori 07068147933.


Pele ya zo Najeriya a 1978
Rahoton wasanni, Isyaku Muhammad a jaridarku ta 22 ga Yuli 2016,  ya ce Pele zai zo Najeriya a  watan August, kuma shi ne zuwansa na biyu bayan  da ya zo a shekara 1967. Ina so in tuna maka ya zo da wani Team sun buga wasa a filin wasa na Ahmadu Bello Stadium Kaduna. Na je wasan, har shi Pele ya buga mintuna kadan a farkon wasan, kuma Guruf Kyaftin Dan Sulaiman a lokacin yana Gwamnan Plateau shi ne babban bako, ina jin a shekarar 1978 ne.
Daga Ahmed Bichi.
                 
Hattara da ’yan PDP Buhari
Edita ka ba  ni dama in yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi hattara da ’yan majalisun dattijai da na wakilan ’ya’yan tsohuwar PDP duk wannan rigimar da suke yi ba a kan talaka ba ne. Duk shiri ne na hana Buhari zaman lafiya. Daga Abubakar Umar Kofa 0805746051.


Fatan alheri ga mutane biyar

Assalamu alaikum. Fatan alheri ga Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da Hon AbdulRahman Kawu Sumaila da Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da Nasiru Yusuf Gawuna da Alhaji Tanko Almakura.  Daga Khairat Kano, 08168575451.


Jinjina ga Malam Abdulkarim dayyabu
Don Allah ku ba ni dama in yi godiya da jinjina ga Mallam Abdulkarim dayyabu, saboda jajircewa da yake yi don son a yi gaskiya da adalci a cikin kasa. Allah ya saka masa da alheri. Amin. Daga Nasiru Sani Gusau 07064340375.

 

Ta’aziyyar dan majalisar Neja
Don Allah Aminiya ki mika min sakon ta’aziyya ga iyalan tsohon dan majilisa Jihar Neja, Hon Alh Tanko Lakwaja Suleja. Daga Bello Dandin Mahe Suleja.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited