Koke ga Gwamnan Bauchi
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Koke ga Gwamnan Bauchi

Salam. Edita don Allah, Ka mika min kokena zuwa ga Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi, Barista M.A Abubakar. Da ya dubi al’ummar da suke unguwar Karofin Madaki  da idon rahama, ya gyara musu hanyarsu da ta tashi daga kofar Mai martaba Sarkin Bauchi zuwa titin jirgin kasa (railway). A  gaskiya wannan hanya tana bukatar gyara bisa la’akari da yadda shugabannin da suka shude suka yi biris da ita. Domin kuwa wannan titi yana daga cikin manyan tituna a cikin garin Bauchi. Da fatan wannan koke nawa zai kai ga kunnuwa Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi.
Daga: Sani Mohammed Chindo. 08030918913. This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

A kawo dauki Bauchi
Editan jaridar Aminiya ka ba ni dama in mika kokenmu ga Gwamnatin Jihar Bauchi’  Bisa wata Annoba da take ci mana tuwo a kwarya, wannan matsala dai ita ce:  Yadda masu garkuwa da mutane suke cin karensu ba babbaka a sassa daban-dabam na jihar.’  Shi ne nake so in yi kira ga Gwamnatin Jihar Bauchi, da ta yi hobbasa wajen magance wannan matsalar,  tun kafin ya yi kamari.
Daga Mudassir Maishayi Bakin Tasha Ningi. 08169139393. This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.


A yi nazarin dandalin shirya fim

Salam Aminiya, Edita ka ba ni dama domin in yi tsokaci a kan Fim billage da wasu ke ganin bai dace ba. Ya kamata jama’a su tsaya su yi nazari ga duk wani abu da gwamnati ta kawo kafin su yanke hukunci a kansa, ka da su cusa tsoro a cikin gwamnati, gwamnati ta rika ganin duk abin da ta kawo al’ummarta ba za su yi marhabin ba. Wannan fim billage da ake magana, wasu da ke kokarin ganin an hana shi ba su ma san mene ne ake nufi da Fim billage ba, to ka da mu rika fakewa da addini ko al’ada muna hana duk wani abu da za a kawo na cigaba. Idan ba haka ba wata rana za mu yi da nasani.
Daga Kabiru Myball Jihar Sakkwato 08139498956.
Hattara ’yan majalisa
Salam ina kira ga ’yan majalisar tarayya da su san cewa mu yanzu talakawa kanmu ya waye. Don haka ka tuna muna zabe na nan, Allah ya kai mu lokaci. Abin da kuka shuka, shi za ku girba.
Daga Isah Dilwaala Abuja 0805 904 4449.


Kira ga Shugaban Buhari

Aminiya don Allah a mika min sakona ga Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya kawo wa Kwanar dangora dauki saboda ruwa da mangareriyar kankara ta kashe mutane da gidaje da uwa uba kayan gonarsu. duk ya lalace.Wayyo Allah muna neman dauki Muhammad Buhari.


PDP mun gane ku

Ai PDP kun bata rawar ku da tsalle, kuma an yi walkiya mun gane. Don haka babu abin da za ku fada wa ’yan Najeriya su yarda ku, duk mai kishin PDP to dama ma’abocin cin hanci da rashawa ne. Domin duk abin da yake faruwa sakamakon abin da mu karbar ku suka aikata a tsawon shekaru 16 da kuka yi ne. Da kun yi abin arziki da duk haka ba ta faru ba, musamman game da rashawa da rashin tsaro. Don haka ina kira ga ’yan Najeriya mu yi hakuri mu ci gaba da addu’a, ka da mu yadda a dawo a sake kawo mana siyasar bambance-bambance.
Daga Garba Y. Majiya 08067742692.
Gaisuwa ga Gwamna Tambuwal
Don Allah Aminiya jarida mai sanar da gaskiya ku mika mini gaisuwa ga Gwannan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal kan biyan tsofaffin ma’aikata kudinsu da wadanda suka riga mu gidan gaskiya, tare da biyan albashi cikin lokaci.
Daga Ahmad Sani Tambuwal Smooth 07034330189


Jinjina ga Buhari  
Addu’a da fatan alkairi ga mai gaskiya  Janar Baba Muhammad Buhari.  mai gaskiya da kokarin yaki da barayin shanu. Allah ya kare jagoran al’ummar Najeriya, Allah amin. Daga Chairman Nayari 08055045212.

Dakatar da dandalin fina-finai daidai ne

Dakatar da gina wurinnan shirya wasannin kwaikwayo, wato Film billage da gwamnatin tarayya ta yi a Jihar Kano ya yi daidai, domin ban da bata tarbiyya da al’ada ba abin da zai haifar.
Daga Abdu Umar (A.U) Shuwaki karamar Hukumar kunchi, Jihar Kano.


Addu’a ga Janar Buratai
Assalamu alaikum. Edita don Allah ka ba ni dama in jinjina wa Oganmu Janar Yusif Tukur Buratai ban taba ganin shugaban sojoji kamarsa ba. Allah ya kare shi daga makiyanmu. Amin summa amin.
Daga Rabiu Lawan Soja, birnin  Binin Jihar Edo 08067653314.

Hattara ’yan fim
’Yan fim Ku daina aibata Malamai don an ki a gina muku Film billage. Idan kuna son aibatawa ne, to ku aibata Shugaba Buhari. Ai wargi wuri yake samu.
Daga AbdulAziz Maska Funtuwa 07039117305


Godiya ga Shugaban kasa
Salam. Mu al’ummar garin Bauchi muna nuna godiya ga Mai girma shugaban kasa ga tallafa wa matasa karkashin shirinsa na power. Muna godiya sosai.  Daga Maryam Lawal Bauchi.

A rusa majalisa
Assalamu alaikum. Aminiya ina so ku gaya wa  shugaban kasa, idan akwai dokar da ta bayar da dama ya rushe majalisar wakilai da dattijai gaba daya, ka nada Firayiminista.
Daga 090328969678

Addu’a ga dan majalisar kiru da Bebeji
Salam. Edita don Allah ka gaya wa  kiru da Bebeji  ba mu yi zaben tumun dare ba Allah ya ba mu mai kishin mu, Abdulmuminu Jibril Kofa  Allah ya kare mana kai ya dora ka a kan maaiya  amin.  
Daga Garban Waisu Larabawa Kofa Bebeji

Kirana ga ’yan Minjibir
Ku kara hakuri ku karkade kuri’unku, mu tara a shekara ta 2019. dan Musa yana godiya da sa albarka.
Daga Jabir Suleiman Kano 09032879687

Gaisuwa ga Aminiya
Salam dubun gaisuwa ga ma’aikatanku gaba dayanku. Allah ya kara kauna. Daga Garba Isma’ila Kyari Kafina Hausa

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited