A taimaki manoman Katsina kafin damina
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

A taimaki manoman Katsina kafin damina

Editan Aminiya ka ba ni dama in yi korafi ga Gwamnman Katsina game da rabon takin zamani. Gwamnatin Jihar Katsina ta yi rabon taki tabbas, amma al’amarin ya zama tamkar ba ta raba ba. Domin akwai talakawan da ba su samu ba. Ya kamata Gwamnanmu Alhaji Aminu Bello Masari ya sani cewa idan har za a yi rabo yana da matukar alfanu a tantance manoma na hakika tun kafin damina ta fadi, ta yadda kokarinsa da na Gwamnatin Tarayya za su yi tasiri wajen habaka aikin gona a kasar nan. Uwa-uba dai manufar gwamnati ba ta wuce ta wadata kasa da abinci ba, sannan ta samar da ayyukan yi ga al’umma. Tunda muradin talakawan Jihar Katsina noma ne, musamman a yankunan karkara, suna bukatar tallafi matuka gaya. Saboda haka a yi wa manoma adashin gata, ko kuma mutum zai iya biyan kudin takinsa a duk lokacin da yake da hali. Sannan akwai bukatar malaman gona su rika shiga kowane sako na karkararmu don warware matsalolin manoma, tare da ba su shawara. A taimaka da damina, tunda noman damina na kowa da kowa ne, amma noman rani na masu kudi ne. Da fatan gwamnanmu zai ci gaba da taimaka wa manoma da taki da sauran kayan aikin gona tun kafin faduwar damina. Kuma a fito da duk tsarin da ya dace wajen inganta aikin gona a jiharmu.
 Daga Bilyaminu Sandamu Daura.08068619481.

Kira ga sarakunan kasar nan
EAmincin Allah ya tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) ina son inyi amfani da wannan fili wajen kira ga manyan sarakunan kasar nan   nagartattu, adalai, wadatattu masu imani, tabbatattu,karantattu, zakakurai, masu kishi.  Malamai da masu fada a ji, kamarsu   adalin Sarkin Musulunci  Dokta Sa’ad Abubakar da Sarkin Kano Malam Sanusi ll da na Zazzau Idris Shehu  da na kudancin kasar nan  da sauransu, da suha da kansu, su ziyarci Shugaba Muhammad Buhari G .C .O. N  a kan ya yi wa Allah  da Annabi Muhammad (S A W) da a bude iyakokin kasar nan domin shigo da abinci cikin kasar nan ko a samu sauki. Saboda manyan ’yan kasuwarmu suna amfani da wannan dama wajen takura wa talakawa tsakani har da Allah bayin Allah suna cikin wani hali. Mu kuma gaskiya mu koma ga Allah mu rinka yawan istigifari; mu rage zunubanmu. Domin halinmu ya ja mana. Allah ka yaye mana halin da muke ciki.  
Daga  Abdulhameed Uzairu Abdulhameed, Gwangwan, karamar Hukumar  Rogo Kano www 07013344449.


Yabo ga wakilin kankara

Salam. Edita don Allah ka ba ni dama in yaba wa dan majalisar mu, mai wakiltar karamar hukumar kankara da Sabuwa da Faskari Jihar Katsina a kan gudunmuwar da yake bayarwa, kamar sama wa matasa abubuwan cigaba. Allah ya saka masa da alheri, amin.
Daga AbdurRazak Tukur, kankara, Unguwar Alhaji Hamza.
Mu ci gaba da gwagwarmaya
Assalamu alaikum jama’a ma’abota wannan shafi kwanaki da dama ba a jini ba, wannan ya faru ne saboda rashin lafiyar da Allah ya jarabe ni da ita ne. Ina rokon jama’a su taya ni addu’a Allah ya ba ni lafiya. Mu ci gaba da gwagwarmaya. Daga Babangida Ahmad Jibrin Gwarzo 08141667702.  


Jinjina ga Tijjani wakilin Azare

Jinjina ga Honarabil Tijjani Muhammad Aliyu  (dan murin Madangala), dan majalisa mai wakiltar Azare da Madangala a majalisar dokokin Jihar Bauchi, a kan kokarin da yake yi wa al’ummar mazabarsa. Allah ya saka masa da alheri amin.


Gwamntin Buhari ta yi rawar gani

Jinjina ga Gwamntin Buhari sakamakon raba wa gwamnatocin jihohi (36) kason kudi na watan Yunin da ya gabata. A wannan karon jihohi sun samu karin kudi fiye da na watan baya.
Daga Baba’Alhaji Mai Aski Dallah, Hadejia.
Godiya ga Aminiya
Bisa jajircewar wannan jarida ta Aminiya ga ma’abota, ya zama wajibi mu yi godiya da jinjina. Allah ya yi muku jagora.
Daga Mainasara Nasarawa Funtuwa 08034208356.

Jijina ga jagororin canji

Salam. Jinjina ga Hon.Garba Datti Babawo da Injiniya Muhammad I Usman da Malam Sani Basawa jagororin canji a karamar Hukumar Sabon-gari.
Daga Usman Shafi’u Sarkin Baki Basawa.


Kira ga Hukumar EFCC
Salam. Edita don Allah ka ba ni dama in yi kira ga ’yan majalisu su sani duk abin da suke aikatawa talakawa suna jiran su nan da 2019. Muna kira da EFCC ta yi bincike a bisa abin da yake faruwa a majalisa, su hukunta duk mai laifi ko shi wane ne.
Daga Usman U. A Dajin 08071303018.


Talakawa a kara hakuri
Edita Don Allah a ba ni dama in yi kira ga talakawan Najeriya da su kara yi wa Baba Buhari hakuri. Domin kuwa dadi yana zuwa Insha Allahu.
Daga Abdul Lelan Kudu, karamar Hukumar Buji, Jihar Jigawa.


Gwamna el-Rufa’I ka yi koyi da Kwankwaso
Me ya sa Malam Nasiru el-Rufai ba zai duba abin da Kwankwaso ya yi wa Jihar Kano, ka yi wa Jihar Kaduna Cibiyar Ilimi.
Daga Akeem Mustapha

Soke Dandalin fim asara ce
Soke dandalin koyar da shirin fina-finai na “Film billage” a Kano babbar asara ce ga Arewa.
Daga Muhammad Salih Keffi Jihar Nasarawa

Hattara APC
 Hattara APC (Tarayya da Jihar Gombe). Shugaba Buhari, ka sani cewa Sanata Goje ne APC, sauran zababbun ko rabon siyasa ne kuma matsorata. Ba fa zai yi kyau ba.
Daga Ali Umaru.  07057576566.


Kira ga ’yan Minjibir
Ku kara hakuri ku karkade kuri’unku, mu tara a shekara ta 2019. dan Musa yana godiya da sa albarka.
Daga Jabir Suleiman Kano 09032879687

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited