Bayan wuya sai dadi
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Bayan wuya sai dadi

Amincin Allah yatabbata’ga Annabi muhammad {S  A W} ina kara kira ga ’yan uwana ’yan Najeriya, don son Annabi  Muhammad (SAW) su ci gaba da addu’a ga shugabanninmu da kasarmu Najeriya, abin da yake ba ni mamaki da wuya a yanzu ka ga mutane a zaune a wuri daya, ko a mota ko a kasuwa ko a tashar mota ba ka ji suna zagin Muhammad Buhari ba.

Ni ina tunanin duk wanda yake zagin Buhari ba a Gabas maso Arewa yake ba. Domin duk wanda yake  a wancan yanki ya san da taimakon Allah da taimakon Buhari muka samu zaman lafiya. Ka duba idan kabilu suka zo sayen kaya da  ka ce ya kara kudi  sai ka ji su yi mana dariya, su  ce mana sai ‘Baba!’ to fa sai Baba Buhari,  babu gudu, ba ja da baya in Allah ya so. Don haka  alhazai su yi amfani da wannan dama wajen yi wa kasa’da Shugaba Muhammad Buhari addu’a Allah ya ba shi ikon kawo canji.
Haka ma Kiristoci su ci gaba da yin addu’a a majami’u  Domin komai ya yi tsanani akwai sauki.  
Daga Abdulhameed Uzairu Abdulhameed Gwangwan Rogo  0701334444

Sakonnin waya

A daina zagin ’yan majalisa

Haba ’yan APC ya kuke zagi da aibata ’yan majalisa bayan cewa aka yi da ku ku yi sak, kuma kuka yi ai yanzu abin da ya rage muku kawai shi ne kurum ku daina zaginsu.  
Daga Abubakar Baba Kano 08033269686.

Godiya ga Shugaba Buhari

Salam mu a’lummar garin Bauchi muna nuna godiya ga shugaban kasa kan tallafa wa matasa karkashin shirinsa na inganta rayuwar5 matasa ta wajen samar musu da ayyukan yi, wato  “npower,” kamar yadda aka yi mas alakabi a Turancin Ingilishi. Allah ya saka wa shugaban kasa. Muna godiya sosai.
Daga Maryam Lawal Bauchi.

Ta’aziyyar Wali dan Tijjani

Salam Edita ka mika mini ta’aziyata ga iyalan  Alhaji Wili dan Tijjaniya (jallo). Ya Allah ka yi masa rahama, ka sa ya huta, amin. In tamu ta zo ka sa mu cika da imani, amin.
Daga Sa’adu Sani Baffa Funtuwa 08067229431

Baba ka dube mu

Assalamu alaikum. Don Allah Edita, ina son ka ba ni dama In bayyana korafina ga Maigirma Shugaban kasa Muhammad Buhari a kan tsananin tsadar kayan abinci da na masarufi a gaskiya mun fada yunwa ’YAR,BUHARI.
Daga Aminu Tanimu Dakata 08051556338

Mu canja munanan halayenmu

Assalamu alaikum Aminiya, ina kira ga dukkan al’ummar Najeriya: mu canja munanan halayen mu zuwa kyawawa, tare da yawaita addu’o’i ba-dare-ba-rana, don haka ne mafitar wannan kuncin rayuwa.
Daga Auwalu Saleh, Nasarawa, Gwaram jihar Jigawa.07066811964.

Fatan alheri ga Salihu Sagir Takai

Assalamu alaikum. Edita ina so don Allah ka ba ni dama a cikin Aminiya aminiyar al’umma in yi wa Mallam Salihu Sagir Takai  tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Kano a  jam’iyyar P.D.P fatan alheri. Da fatan Allah ya yi masa jagora
Daga Jamilu Gambo Takai 08166835313.

Ta’aziyyar ’ya’yan Jihar Gombe

Assalamu alaikum Aminiya. Ina fatan dukkan ma’aikatanku suna nan lafiya? Don Allah ku mika mini sakon ta’aziyyata ga al’ummar Jihar Gombe dangane da rasuwar ’ya’yanta, wanda hadarin mota ya rutsa da su a kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri, inda duka suka kone. Da fatan Allah ya karbi shahadarsu. Amin.
Daga Fatima U Bauchi.

Buhari ba ya talautawa ko azurtawa

Salam Aminiya, Ya kamata jama’a su sani cewa, babu wani mahaluki da zai iya azurtawa ko talautawa. Don Allah jama’a mu bar jingina wa bawa aikin da ba shi yake iya yi ba. A yau mutane sun manta da Allah yana iya jarabtar bayinSa ta hanyar da ya ga dama, komai ya faru sai a ce Buhari. Kuma Buhari mutum ne kamar kowa ba ma’asumi ba. Addu’a ya kamata mu ci gaba da yi masa Allah ya ba shi ikon yi mana adalci.
Daga Kabiru Myball Jihar Sakkwato 08139498956.

Ci gaba ko koma-baya

Salam. Edita ka isar min da sakon jinjinata ga malaman da suka yi tsaye tsayin daka ga fadakarwa, har aka samu nasarar dakatar da ginin dandalin shirya fina-finai na “film billage” daidaikun mutane suna yayata amfaninsa. Eh,  ba wai an ce ba ya da amfani ba ne gaba daya abin da ake cewa, shi ne illarsa ta fi amfaninsa yawa, duba ga  yadda samarin mu da ’yan mata suke kwaikwayar wasu dabi’u da suka yi hannun riga ga ainahin dabi’a ko halayya da tarbiya na Malam Bahaushe kashi 75 cikin 100 na tabarbarewar tarbiyyar yaran mu matasa da ’yan mata. Ina ya samo asali ? Ra’ayi riga. Kuma fahimta fuska,  wani ci gaban dai shi yake kawo ci baya. Allah ya sa mu dace.
Daga Sunusi Ahmad Bashir Sakkwato. 08032389120.

Bukatar da ta fi dandalin fina-finai.

Assalamu alaikum. Kanawa da al’ummar kasata fatan alkairi a gareku, Edita ina so ka ara min dama domin in yi kira ga mahukuntan gina dandalin shirya fina-finai na “Film billage,” su sani akwai abubuwa da dama da ake bukata a Kano, ba wai Film billage ba shi da mahimanci ba. Domin shi ma za a amfana da shi tunda haraji za a biya haraji, kuma ci gaban kasa ne. Sai dai amma idan abu ya taso a fara duba mafi mahimmanci a aiwatarwa akwai ’yan kasuwa da dama da suke bukatar shaguna, amma ba su da halin yi a gina aba su haya mana dan kara habbaka tattalin arzikin kasar nan.  
Daga Raheenat kofar Mazugal Kano 09036444468.

Mu dage da addu’a

Assalam shure-shure bayahana mutuwa to ‘yan boko haram mu dai mun san karshenku ya zo da izinin Allah. Kuma Alhamdulilla godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu zaman lafiya a kasar mu baki daya. Kuma  ina kara kira ga ’yan uwana yn Najeriya a dage da addu’ar Allah ya tabbatar mana da zaman lafiya mai dorewa.
Daga Muzakkiru Abubakar Jataka Kano

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited