A kawo wa al’ummar Jahun dauki
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

A kawo wa al’ummar Jahun dauki

Editan Aminiya ka ba ni dama in mika koken al’ummar Jahun. Mutane karamar Hukumar Jahun ta Jihar Jigawa sun yi fama da matsalar ambaliyar ruwa, al’amarin da ya haifar da dimbin asara a gidaje da gonaki.

Kai akwai ma wasu harkokin kasuwanci da ambaliyar ta sanya aka rufesu. Kuma mafi yawan mazauna unguwanni dole tasa suka rika neman hanyoyin shige da fice. Wasu kuwa an bar su a rabe a wasu sassa na karamar hukumar.
Wani abin mamaki kuma abin takaici shi ne, wannan musifa ta auku ne daidai da lokacin da al’ummar Najeriya ke fama da matsalar tattalin arziki. Don haka al’ummar karamar Hukumar Jahun na matukar bukatar daukin gaggawa.
Ina kira ga gwamnatocin karamar hukuma da ta jiha da ta tarayya da sauran masu hannu da shuni kan lallai su tausaya wa al’ummar Jahun. Munba kuma fatan masu rike da mukaman gwamnati za su yi amfani da mukamansu wajen kawo dauki.
Sannan akwai bukatar ma’aikatar ilimi ta kawo dauki a mazabar dan majalisar dattijai mai wakiltar Dutse, don gyara makarantun sakandaren Marabusawa/Garu da ke karamar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa.

 

Sakonnin waya

Jinjina ga Kwamishinan muhallin Katsina
A yau zan yi amfani da wannan damar domin yin jinjina ga kwamishinan muhalli na Jihar Katsina Hamza Sule Faskari a kan yadda yake gudanar da ayyukan mahalli a Jihar Katsina, wanda mu al’umma mun baya ga haka sosai da fatan Allah ya ba shi ikon kara gyara jihar mu.
Daga Usman Manika Mairuwa Road Funtuwa 08060309856 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Abin takaici ne auren jinsi a Sakkwato

Matukar dai zargin da ake yi wa wani dan Jihar Sakkwato na bai wa wadansu ’yan luwadi muhallin da suka gudanar da auren jinsi, ya zamo gaskiya, to wannan abin takaici ne da kuma Allah waddai. Muna kira ga jami’an ’yan sanda da kada su yi kasa a gwiwa wajen gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a wannan muguwar dabi’a a gaban kuliya.
Daga Mahmud Salihu kaura Namoda, Jihar Zamfara. 07067557586 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Ta’aziyyar Gambu

Muna rokon Allah ta’ala ya jikan Muhammad Gambu da rahama. Ya sa ya huta, ya sanya aljanna Firdausi ce a makomarsa. Ya kyautata bayansa.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi, Tashar Bagu Gusau. 08069807496. This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. .

Ziyarar John Kerry
Hakika zumunta a kafa take. A cikin wannan makon ne Sakataren harkokin kasashen waje na Amurka. Mista .John Kerry ya kawo ziyara a Najeriya. Da fatan wannan ziyara ta zama alheri ga Jama’a da kuma kasa baki daya, tare da kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.  Daga Haruna Muhammad Katsina. Shugaban kungiyar Muryar Jama’a. 07039205659 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it. .

Kira ga shugaban kasa

Assalamu Alakum Edita, ina neman alfarma a jaridarka mai farin jini don isar da korafina ga maigirma shugaban kasa a kan azzaluman ’yan kasuwa a kan hauhawar farashin kayan abinci. Don Allah Baba a fito da tsarin daidaita farashi, wato a Turance, “PRICE CONTROL.” Mu talakawa muna tare da kai.
Daga Aminu Tanimu Dakata, mazaunin Abuja Apo II Waru billege, Sabuwar Fanteka, abokin Idris Adamu Rigasa 08051556338.

Ga ‘yan siyasar kasar nan.

Edita don girman Allah, ka ba ni fili in shaida wa ‘yan siyasar kasar nan cewa, a kiyayi amfani da ra’ayin siyasa ana cin mutuncin masu mutunci. Bai dace ba sanya wa dabba sunan mutum don kawai bambancin ra’ayin siyasa. Jama’a a yi siyasa mai tsafta  mai cike da girmamawa. Mu tsaya, mu mutunta junammu, mu san cewar jefa wa juna kyawawan kalaman mutuntaka su ne tafarkin samun nasarar siyasa. Mu ji tsoron Allah, mu guji siyasar cin fuska,  muzantawa da dabbantarwa.
Daga Amiru Isah Bakori 07068147933

Kira ga al’ummar Najeriya

Assalamu alaikum Aminiya kira ga dukkan al’ummar Najeriya: mu chanja munanan halayen mu zuwa kyawawa, tare da yawaita addu’o’i ba-dare, ba-rana, wannan ita ce mafitar wannan kuncin rayuwa.
Daga:Auwalu Saleh Nasarawa,Gwaram Jihar Jigawa.07066811964.

Hakuri maganin zaman duniya,

Assalamu Alaikum. ’Yan uwana ’yan Najeriya don Allah  mu ci gaba  da hakuri muna masu addu’ar neman kariya kan abin da ya dame mu. Insha Allahu za mu kasance cikin rahamarSa bada dadewa ba.. Allah Ma ji rokon bawanSa ne.
Daga Badamasi Wanzami Kasuwar Elepo Jihar Lagos Nigeria.07031025054.

A rusa ’yan majalisa

Assalamu alaikum ya dace a rusa ’yan majalisa Najeriya a bar mana ciyamomi da kansiloli don ba su da amfani ga talakkawa.
Daga Shu’aibu Aliyu Adera Kwara S T08054288930.

Muna goyan bayan Buhari

Hakika muna maraba da matakin da Shugaba Buhari ke shirin dauka, na neman karin iko daga majalisun tarayya, domin fuskantar matsalar tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya, wadda yanzu haka take ci mana tuwo a kwarya. Don haka muke jan hankalin ’yan majalisun da su gaggauta amincewa da wannan bukata ta shugaba Buhari da zarar sun dawo daga hutun da suke yi. Allah ya taimaki kasar mu Najeriya.
Daga Mahmud Salihu kaura Namoda, Jihar Zamfara. 07067557586

Kira ga shugabannin Afirka da ’yan jarida  

Don Allah  a taimaka ‘a saki dan jaridar nan  Ahamad  Abba, wakilin gidan rediyo  RFI  Farance,. sakamakon tsare shi da’ake yi a kan zarginsa da ake yi a kan kungiyar Boko Haram. Domin mutumin kirki ne  ko a ranar 3 ga watan Agustar da aka gurfanar da shi a gaban kotu ba a tabbatar da laifinsa ba. Ya kamata  a sake shi. Domin ina daya daga cikin wanda nake bakin cikin kama shi.  Ya Allah ka kubutar da bawanKa Ahamad  Abba  daga ukubar da yake ciki, domin Annabi da Alkur’ani. Amin summa amin.
Daga  Masoyinsa  Abdulhameed Uzairu Abdulhameed  Gwangwan +2437013344449.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited