Martani ga Mai Martaba Sarkin Kano
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Martani ga Mai Martaba Sarkin Kano

Salam, don Allah Edita ka taimake ni da fili don in yi tsokaci a kan maganar da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu ya yi a kan Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, inda ya ce kada ya yi karko irin na tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan..
Wannan magana da Sarki ya yi ta zo mini da mamaki, don haka ina bai wa Sarki shawara da ya rika kare mutuncin sarauta don kada siyasa ta debe shi.  Mu dai ’yan Najeriya talakawa muna yi wa Shugaba Buhari kyakkawan zato da kuma fatan alheri.  Muna yi masa addu’ar Allah Ya kare shi, Ya yi masa jagora wajen tafiyar da harkokin mulkin kasar nan cikin nasara.
Mai Martaba ka tuna kai uba ne ga kowa, don haka ba komai yakamata ka rika yin babatu a kai ba.  Idan kana da shawara kamata ya yi ka samu Buhari a asirce, ba ka fito bainar jama’a kana irin wadannan kalamai ba.
Na gode da wannan dama da kuka ba ni.
Daga Rabi’u Yunus Kura Agege ,Jami’in Kasuwanci  na Mujallar Muryar Arewa  a garin Legas 09093333955

Koke ga Editan Aminiya
Salam. Aminayata. Ina mai turo sakonni masu muhimmanci, amma ba a taba buga ko da daya ba. Da fatan Edita za a duba kokena.
Daga abbass@2.effect karamar Hukumar kankara, Jihar Katsina 08035332178.
Taya  IBB murna

Ina taya tsohon shugaban kasata murna cika shakaran 75 a duniya dafan Allah zai kara maka lafiya da nisan kwana.
Daga danbukur Yaro. 08162565182.


Kira ga dangote

Editan Aminiya, ina kira ga Alhaji Aliko dangote da ya daure ya rika cika alkawurran da yake yi a Najeriya.
Daga Saminu Mayentea Batsari.08036773485.

A taimaka wa ’yan gudun hijira
 Gudun hijira, da  dabbobin layya  da kayan sallah.
Daga Usman Magaji Kalgwai, karamar Hukumar Auyo  Jihar Jigawa. 08063437O74.

Ta’aziyyar Gambu

Salam. Edita ka yi mini ta’aziya ga iyalan Alhaji Muhammadu Gambu mai wakar barayin. Ya  Allah Ka yi masa rahama, Ka san ya huta. Amin. Ln tamu ta zo Ka sa mu cika da imani. Amin.
Daga Idris Yaro Abuja .07061860202.

Gaisuwa ga Kwankwaso
Don Allah Edita ina so Aminiyar amana ta taimaka mun in tura wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso sakon gaisuwa. Kuma ina yi wa duk dan APC fatan alkhairi. Allah ya dada taimaka musu.
Daga Amira Mukhtar Ibrahim Portharcourt 07035779109.

Sako ga Maryam Booth

Salam Edita    ga sakona zuwa ga Maryam Booth Allah ya cika miki burinki na yau da kullum.
Daga Nabila Aliyu Marafa 08130681024
jinjina ga Dokta Kwankwaso

Salam Edita ka mika mini jinjina ga Dokta Rabiu Musa Kwankwaso bisa sunnar Annabi  (SAW) da ya aiwatar bisa auren zawarawa da ya yi. Ya  Allah ka saka masa da aljana amin, ka biya masa bukatunsa na alkairi amin. Ya Allah ka sa sauran shugabanni su yi koyi da shi amin.
Daga  Sa’adu Sani (Baffa) Funtuwa  09092577473.
Gaskiyar sakataren PDP

Aminiya abin da sakatari watsa labarai na jam’iyya PDP ya fadi gaskiya ne, mutane sum samu arziki sun kama kasuwanci an yi aure, an gina manyan gidaje. Yanzu kuwa matsala tasa an saki matan, ga shi zaurawa sun yi yawa.
Daga Bello Dandin Mahe Suleja.

Ta’aziyya ga Zaidu Bala
 
Aminiya ina son ku mika min sakon ta’aziyya.A madadin kungiyar Muryar Talaka ta Jihar Yobe muna mika ta’aziyyarmu ga Shugaban kungiyar na kasa Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi, bisa rasuwar mahaifiyarsa. Allah ya jikanta ya gafarta mata.
Daga Salisu Armaya’u Nguru. A madadin kungiyar Muryar Talaka ta Jahar Yobe.

Tonon sililin ’yan majalisa
  Salam jaridar Aminiya  don  Allah ko ba ni fili don in yi tsokaci a kan ’yan majalisun mu na Najeriya, to ai Hausawa sun ce mai hali bai fasa halinsa. Sai  dai in sata yake so, to sai  ga shi Allah ya tona musu asiri suna tonon silili a tsakanin su. Don an ce alhaki kwikwiyo ne, mai yinsa yake bi. To mu ‘yan Najeriya mun barku da Allah don akwai ranar gobe kiyama, ranar da babu wani sarki sai Allah Buwayi gagara misali. To ’yan uwa Musulmi da wadanda ba Musulmi ba, mu ci gaba da addu’a Allah ya kawo mana karshen zaluncin nan da suke yi. Kowa ya yi nagari don kansa.
Daga Alhaji Musa.G.B.S.JiharJigawa.

Kira ga Shugabannin Najeriya
Assalamu alaikum. Aminiya don girman Allah ku isar mana da sako ga shugabanin Najeriya a rushe ’yan majalisar tarayya da na wakilai, ko kuma a rage musu karfin iko.
Daga Haruna Ibrahin Katcha 08116467485

Jinjina ga Yarin Katsina
Jinjinar girma ga Alhaji Sule Yarin Katsina, jigo a jam’iyyar APC, masoyin Buhari, bisa ga raba motoci ga talakawan yankinsa. Hakika wannan abin a yaba ne, Allah ya saka masa da alheri.
Daga Mainasara Nasarawa Funtuwa, 08034208356.
Kira ga Gwamna Zamfara
JAminiya Don Allah ku ba ni dama inyi kira ga Gwamnan Zamfara a kan kin biyan kudin jarabawar dalibai. Wallahi gwamna ka sani Allah zai tambayeka a kan rike hakkin jama’a da ka yi. Ko ka ki biya ne  don babu ’ya’yan manya a cikin makarantun gwamnati? Mai girma gwamna a duba wannan matsalar.
Daga Ibrahim Rabilu Tsafe Zamfara 07064282182 This email address is being protected from spambots. You need JavaScript enabled to view it.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited