✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Addini bai bambance tsakanin mutane kan yadda za su yi rayuwa ba – Limamin Triumph

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Triump da ke Unguwar Fagge a Kano, Malam Lawan Abubakar ya shaida wa Aminiya cewa addinin Musulunci bai bayar da…

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Triump da ke Unguwar Fagge a Kano, Malam Lawan Abubakar ya shaida wa Aminiya cewa addinin Musulunci bai bayar da wata ka’ida game da yadda malamai za su yi rayuwa ba, inda ya ce kowane mutum zai yi rayuwa ne gwargwadon samunsa.

Malam Lawal ya ce “A gaskiya babu wata ka’ida da addinin ya sanya cewa ga yadda wani mutum sawa’un malami ne ko attajiri ko talaka zai yi rayuwa ba, kowane mutum zai yi rayuwa ne gwargwadon wadatarsa ko samunsa. Mu sani Allah ne ke raba arziki ga wanda Ya so, ko Ya hana wanda Ya so,  za a iya samun malamai mawadata kuma za a iya samun talakawa, don haka kowa ka dauka zai yi rayuwa ne gwargwadon samunsa.”

Malamin ya ce abin da ake ki shi ne a samu mutum yana almubazzaanci ko yana kwauro a abin da Allah Ya ba shi.

“Allah da kanSa Ya yi umarni cewa kada mutane su zama masu sakin hannu har ya yi yawa, haka kuma kada su zama masu kwauro (rowa). Sannan Allah Ya yabi bayin Allah da suke sakin hannunsu ga talakawa ba sa boye abin da Allah Ya ba su.”

Ya ce sai dai “Ba a son a samu malami ya zama mai yin rayuwar gasa, ta hanyar yin gasa da attajirai ko sarakuna ta yadda dole zai rika kwaikwayon rayuwar da suke gudanarwa.”

Malam Lawal ya ce duk da cewa malamai su ne abin koyi wajen al’umma amma ba ana nufin su kuntata rayuwarsu don suna malamai ba ne.

“Idan ka samu malami mai wadata ba zai kuntata rayuwarsa ba don kawai kasancewarsa malami dole ne zai yi abin da ya kamata na jin dadin rayuwa. Ya kamata mu sani cewa son jin dadi dabi’a ce da kusan kowane mutum ke da ita, don haka babu wanda yake son ya sha wahala sai wanda Allah Ya dora masa ita dole,” inji shi.

Malamin ya ce ko game da ciyar da iyali Allah Ya yi bayanin cewa kowane mutum zai ciyar gwargwadon abin da Allah Ya hore masa.

“Nana A’isha (RA) ta ce Manzon Allah (SAWA) yana wadatar da su da abinci na tsawon lokaci idan yana cikin wadata, kuma ta ce a kan dauki tsawon watanni ba tare da an dora tukunya a gidansu ba, har aka tambaye ta me suke ci tsawon wannan lokaci, sai ta ce suna rayuwa ne a kan dabino da ruwa,” inji shi.

Malamin ya ce jama’a su fahimci kasancewar mutum yana malami ba dole sai an gan shi cikin tsumma ba, a cewarsa addinin Musulunci ya yi umarci Musulmi ya kasance cikin tsabta da kyan gani.