Mai martaba Sarkin Bare-Barin Jihar Legas, Alhaji Mustafa Mai Kanuri na Legas ya yi kira ga ’yan Arewa mazauna Kurmi da su haɗa kansu su zamo tsinsiya maɗaurinki ɗaya.
Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo, ya amince da samar da burtaloli domin kiwon dabbobi da nufin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a jihar.
Al’ummar Fulani makiyaya mazauna Iseyin a Jihar Oyo sun shiga fargaba tun bayan da a kwanakin baya suka wayi gari da wani abin alhini bayan da wasu mutane da suke zargin ’yan asalin yankin ne suka kai masu farmaki a daura da wata korama da suke kiwo, inda suka halaka Fulani makiyaya 12 tare da tarwatsa dabbobin da suke kiwo a wajen.
Sakataren Kwamitin Shura na kungiyar Limamai da Alarammomi na Jihar Kurosriba, Kyaftin Rilwan Liman ya ce kwamitinsa zai yi matukar bakin kokarinsa ya ga ya fidda kitse cikin wuta, waje samar da tabbataccen zaman lafiya da fahimtar juna musamman tsakanin Musulmin Jihar Kurosriba da wadanda ba Musulmi ba.
Wani dan siyasa da ke zaune a Kalaba Jihar Kurosriba, Alhaji Bara’u Musa ya bayyana rashin gamsuwa da yadda Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da zaben kananan hukumominta a kwanakin baya, inda ya ce yanayin zaben tamkar zubar da mutuncin jiha da na Jam’iyyar APC ne.
Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru ya nemi dukan ’yan Arewa da ke zaune a Kudu maso Yammacin kasar nan su yi rajistar sunayensu da hadaddiyar kungiyar Ci Gaban Hausawa, (SAHC) wacce take fafutukar ci gabansu a wannan sashe.
Wani Fasto a Legas ya shiga komar ’yan sanda bisa zarginsa da da laifin fashi da makami.