✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ra’ayoyin al’ummar Nijar mazauna Benin dangane da zaben kasarsu

Wakilin Aminiya ya zanta da wasu ’yan Nijar, inda suka bayyana ra’ayoyinsu dangane da babban zaben da aka gudanar a kasarsu a kwanan baya.Alhaji Abubakar…

Wakilin Aminiya ya zanta da wasu ’yan Nijar, inda suka bayyana ra’ayoyinsu dangane da babban zaben da aka gudanar a kasarsu a kwanan baya.
Alhaji Abubakar Ishaku ya ce: “Hakika mutanenmu sun amsa kiranmu, sun fito sun kada kuri’unsu na zaben Shugaban kasa. Don haka ina kira ga Gwamnatin Nijar da ta rungumi kowa a matsayin dan kasa, mazauna kasashen waje da na cikin gida.”
Muhammadu Shehu kuwa ya ce: “Ni fatana ga wannan zaben ya zama mai albarka da samun zaman lafiya mai dorewa da alheri mai yawa.”
Sabon sarkin Buzaye na Jihar Edo, Alhaji Ibrahim Ahmadu ya yi fatan Allah Ya tabbatar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin jama’ar Nijar da sauran. Sannan ya yi kira ga jama’a da su mara wa duk wanda Allah Ya ba shi nasara baya.
Alhaji Ahmad Sagalala, tsohon sarkin Buzaye a Benin, ya ja hankalin jama’a a kan su bi doka kuma su ci gaba da zaman lafiya tare da girmama juna.
Alhaji Ahmadu Isah, sarkin Zabarmawa a Benin, ya yi addu’ar fatan alheri na samun shugabanni masu nagarta da adalci da tausaya wa jama’a da samar da zaman lafiya ga alumman Nijar da Najeriya baka daya.
 dan kasuwa mai hada-hadar canjin kudaden waje, Alhaji Mika’ila Usman, cewa ya yi: “Alal hakika muna cikin farin ciki da jin dadi kwarai domin ganin yadda al’ummarmu suka ba da himma suka fito zuwa wurin zabe da muka gudanar na Shugaban kasa. Wannan ya nuna a fili mun samu ci gaba, don haka nake yin kira da babbar murya, da su ba da hadin kai ga duk wanda sakamakon zabe ya nuna ya samu nasara kuma ina godiya ga hukumomin Najeriya da jami’an tsaro.”
Alhaji Haladu Ibrahim, shugaban matasan ’yan Nijar mazauna Benin, ya ce: “Ina kira ga daukacin matasanmu da sauran ’yan Nijar baki daya, mu hada kai mu ba shugabanninmu goyon baya; a sakamakon wannan zaben. Duk wanda Allah Ya sa ya samu nasara, mu mara masa baya.”
Su kuwa Musa Muhammed da Umaru Sulaiman da Abubakar Ibrahim, sun ba da goyon baya da yadda zaben ya gudana. Sun ce a shirye suke su ba wanda Allah Ya sa ya samu nasara goyon baya, domin su bukatarsu zaman lafiya da ci gaban kasarsu ne burinsu.
Haka kuma mata ’yan Nijar mazauna Benin, su ma sun yaba da wannan zaben, inda suka bayyana farin ciki da jin dadinsu game da shi. “Muna godiya ga Ubangiji da Ya nuna mana wanna ranar, mun ji dadi ba kadan ba.” Inji su.
Alhaji Tanimu Ibrahim ya ce: “Tsarin da aka bi aka gudanar da zaben, abin a yaba ne. A gaskiya mun gamsu da yadda wannan zaben aka gudanr da shi, don haka fatanmu a nan shi ne, Nijar ta dore da zaman lafiya da hadin kan jama’arta.”