✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasikun Shugabanni: Ana yi wa Buhari yankan baya ne

Assalamu alaikum Editan Aminiya ka ba ni fili  in bayyana ra’ayina kan wasikun sukar lamiri tsofaffin shugabannin kasa biyu, wato obasanjo da Babangida suka aike…

Assalamu alaikum Editan Aminiya ka ba ni fili  in bayyana ra’ayina kan wasikun sukar lamiri tsofaffin shugabannin kasa biyu, wato obasanjo da Babangida suka aike wa shugaba Muhammadu Buhari, alhali suna iya ganawa da shi, don yi wa tufkar hanci kan kowace irin matsala da ta addabi kasar nan, matukar dai niyyarsu mai kyau ce. Suna  yin  yankan baya ne ga Buhari kawai,musamman yadda daukacin mutanen biyu suka hadu a kan cewa ya sauka daga mulki ko kuma kada ya tsaya takarar neman shugabancin kasar a shekara ta 2019. To su sani, mu ’yan Najeriya musamman talakawa Buhari ya fito da ayyukan alheri, su kuwa bas a son ganin ya samu nasarar kyautata rayuwar talakawan kasar, musamman yadda yake kokarin gyara barnar da aka tafka a baya. Al’umma mu fahimci cewa Baba Buhari Ikon Allah ne ya tabbatar da shi,kuma shi ne kawai zai iya kawar da shi. Idan kuwa suna zaton cewa makirce-makircensu da kulle-kulle za su iya kai ga gaci, to ‘ga fili nan, ga mai doki’ Sai a yi ta sukuwa. Tunda tarihi ya tabbatar da cewa tsohon Shugab Obasanjo ya sha aike wa shugabanni irin wadannan wasiku don nuna cewa shi kadai ne ya yi aiki kwarai, alhali a zamaninsa aka yi gwanjon dimbin dukiyar kasar nan, wasu suka zuba kudin a aljihunsu, al’amarin da ya haifar wa kasar nan dimbin asar wutar lantarki a tsawon mulkin jam’iyyarsu ta PDP. ‘’an Najeriya sai mu yi hattara. Haka za ku yi ta yi, har Allah Ya gajiyar da ku. Idan kunne yaji to jiki ya tsira. Allah Ya sa mu gane, mu zamo masu kishin kasa da al’umma, mu kiyayi kulla wa kasarmu makirci. A huta lafiya. 

Daga Mohammed Babayo, Keffi Jihar Nasarawa 08096954874.