✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2015: Ba majalisa ce za ta zaba mana Gwamna a Gombe ba – CNPP

Gamayyar Jam’iyyun Siyasar kasar nan (CNPP) reshen Jihar Gombe ta nuna rashin amincewarta kan Majalisar Dokokin Jihar ta ba Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo ikon sake…

Gamayyar Jam’iyyun Siyasar kasar nan (CNPP) reshen Jihar Gombe ta nuna rashin amincewarta kan Majalisar Dokokin Jihar ta ba Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo ikon sake tsayawa takara a shekara ta 2015, inda ta ce ba aiki majalisar ba ne ta zaba wa al’ummar jihar Gwamna ba.
Sabon Shugaban CNPP na Jihar Gombe Alhaji Sale Lawan na Jam’iyyar Labour Party ne ya bayyana haka a lokacin da suka gudanar da taron manema labarai a ofishinsu don shaida musu matsayin kungiyar kan wannan batu.
Alhaji Sale Lawan, ya ce su a jam’iyyunsu daban-daban da kasancewarsu ’yan asalin Jihar Gombe sun gamsu da irin ayyukan raya kasa da Gwamnan ke gudanarwa, amma katsalandar da ’yan majalisar suka yi ne ba su gamsu da shi ba. “Kamata ya yi a ce jam’iyyar da Gwamnan ya fito wato PDP ta ce ta sake ba shi ikon yin takara ba su ba saboda su ba wakilan jam’iyyar Gwamnan ba ne wakilan jama’a ne idan jam’iyya ta yi haka ba ta yi kuskure ba, amma su ’yan majalisa bai kamata su ci albasa da bakin jam’iyyar ko jama’ar jihar ba,” inji shi.