Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

2019: Abin da ya sa kamfe ba ya armashi

Gangamin kamfe na Jam’iyyar APC
Gangamin kamfe na Jam’iyyar APC

Yayin da yau saura kwana 36 a gudanar da babban zabe a kasar nan, sai dai har yanzu hidimar kamfe ba ta kankama  yadda aka saba ba. A shekarun baya kafin a yi zabe da watanni,  kowane yanki na kasar nan yakan dauki dumi saboda hidindimun kamfe din siyasa.

Akan kakkafa daruruwan kungiyoyin sa-kai wadanda suke kamfe ga ’yan siyasa, musamman na ’yan takarar gwamnoni da na Shugaban Kasa. Haka kuma kafafen watsa labarai kamar gidan jaridu da rediyo da talabijin sukan samu makudan kudi wajen tallata ’yan takara daga jam’iyyu daban-daban.

ADVERTISEMENT

Sai dai a bana abin ya canja sosai inda masu fashin baki da ’yan siyasa da talakawa sukashaida wa jaridar Aminiya cewa babu hidindimun siyasa sosai kamar yadda aka saba.

Hakan kuma ya kasance ne duk da cewa ba a taba samun ’yan takara masu yawa da suke neman mukamai kamar a wannan karo ba a tarihin Najeriya. Wannan shi ne karo na farko da aka yi wa jam’iyyun siyasa har 91 rajista domin su tsayar da ’yan takara. Haka kuma wannan ne karo na farko da ’yan takara 73 suka tsaya takarar Shugaban Kasa.

ADVERTISEMENT

A ranar Talatar da ta gabata, Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana wa manema labarai cewa akwai ’yan takara dubu 20 masu neman mukamai a matakai daban-daban a zabubbukan da za a gabatar a watan Fabrairu da Maris din bana.

Ya ce wannan shi ne karo na farko da aka samu ’yan takara masu dimbin yawa haka a tarihin Najeriya. Ya kara da cewa an yi rajista ga mutane sama da miliyan 80, wadanda za su kada kuri’a a cibiyoyin zabe sama da dubu 120 a kananan hukumomi 776 a jihohi 36 na kasar nan da kuma Babban Birnin Tarayya.

Farfesa Yakubu ya ce akwai mutum 1,800 masu neman zuwa Majalisar Dattawa wadda take da kujera 109; sai mutum 2,600 masu neman zuwa Majalisar Wakilai, wadda take da kujeru 360.

Sa’annan kuma akwai ’yan takara 14,000 masu neman tsayawa takarar kujerun majalisun dokoki na jihohi guda 991 da ke jihohi 36.

Babu kudi a hannun kungiyoyi da ’yan siyasa

’Yan Najeriya da dama sun yi zaton ’yan takara da jam’iyyun siyasa za su yi facaka da kudi domin yakin neman zabe kamar yadda aka saba, amma kuma bisa ga dukan alamu hakan ba za ta faru ba.

Binciken Aminiya ya gano cewa Jam’iyyar APC mai mulki har yanzu ba ta fara sakin kudi ga jami’anta, domin su fara hada-hadar siyasa ba, duk da cewa za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa a ranar 16 ga Fabrairu mai kamawa; sa’annan a gudanar da na gwamnoni da majalisun jihohi a ranar 2 ga Maris mai zuwa.

Masu fashin baki sun shaida wa Aminiya cewa kudaden da manyan jam’iyyu kamar APC da PDP suka tara lokacin da suka sayar da fom ga ’yan takara yana da yawa amma kuma bai taka kara ya karya ba, idan aka duba girman Najeriya da irin kudin da ake kashewa wajen hayar jiragen sama da filayen wasanni da fostar da ake bugawa da kuma kyaututtuka da ake bai wa ’yan barandan siyasa a kowane taro.

Akwai bayanan da ke cewa Jam’iyyar APC ta tara Naira biliyan 12 da miliyan 600 lokacin sayar da fom ga ’yan takara a matakai daban-daban, yayin da ita ma babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta samu makudan kudi. Sai dai kuma Aminiya ta gano cewa sauran jam’iyyu 89 da za su shiga zabubbukan a matakai daban-daban ba su samu kudi masu yawa ba a wajen sayar da fom.

A shekarun baya lokacin da PDP ke mulki, tara kudin yin kamfe ba abu ne mai wahala ba; domin shugabannin jam’iyyar sukan shirya manyan tarurrukan tara kudi, ta yadda jiga- jigan ’yan siyasa da manyan ’yan kasuwa da ’yan kwangila da sauransu kan bayar da gudunmawa mai tsoka domin gudanar da kamfe. Ta wannan hanya ce ake buga manyan hotunan da ake sa wa a kan alluna a sayo motoci da sauran kayan annashuwa; kuma a rarraba wa kungiyoyi kudi domin su yi kamfe.

Matsalolin PDP

Bisa ga dukan alamu PDP ba ta da kudin da take da su a da, musamman ganin cewa ba ita ce ke da madafun mulki a matakin Tarayya ba. Bincike ya nuna cewa kamfe din jam’iyyar ya ki armashi har yanzu, domin mafi yawancin ’ya’yan jam’iyyar sun yi likimo sun zura ido ga dan takararsu na Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Yawancin gwamnonin jam’iyyar sun ki fitar da kudi domin a kashe a matakin tarayya. Gwamnoni irin su Nyesom Wike na Jihar Ribas da Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom da Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato suna neman sake tsayawa takarar Gwamna, don haka kowannensu yana hidimar ce a jiharsa.

Duk da cewar jami’an Jam’iyyar PDP a matakin tarayya sun yi shiru kan batun, majiya kwakkwara ta bayyana wa Aminiya cewa akwai matsaloli sosai na rashin kudi. Don haka ko a lokacin da aka gudanar da babban taron PDP a Jihar Sakkwato, Atiku ne ya bayar da makudan kudi domin shirya bikin. Tun daga wancan lokacin kusan shi ne yake bayar da kudade a duk lokacin da za a gudanar da kamfe na shiyyoyi, kamar wanda aka yi a Ilori ta Jihar Kwara.

Matsalolin APC

Ita ma Jam’iyyar APC ta kaddamar da babban taronta na fara kamfe a Jihar Akwa Ibom mako biyu da suka gabata; inda dubban mutane suka hallara.  To amma kuma tarurrukan da suka biyo baya ba su samu tagomashin wanda aka yi a Uyon Jihar Akwa Ibom ba.

Wasu majiyoyi a Jam’iyyar APC sun bayyana wa Aminiya cewa hakan yana da nasaba da zaman dar-dar da ’ya’yan jam’iyyar suke yi.

Wadansu daga cikin gwamnonin jam’iyyar sun kaddamar da nasu kamfen din tare da gayyatar Shugaban Jam’iyyar ta Kasa, Adams Oshiomhole da makarrabansa.

A shekaranjiya Laraba sai da ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake jan kunnen ministocinsa cewa bai yarda a yi amfani da kudin gwamnati ba wajen yin kamfe.

Shugaban wanda ya yi bayani a lokacin Taron Majalisar Zartarwa ta Kasa a Fadar Shugaban Kasa, ya bukaci ministocin sun nuna wa ’yan Najeriya cewa lallai an samu canji a karkashin mulkinsa. “Tabbas ban yarda a yi kamfe da kudin talakawa ba. Ta wannan hanya ce kawai za mu tabbatar wa ’yan Najeriya cewa muna yaki da cin hanci da rashawa,” inji Buhari.

Shugaba Buhari ya ba su shawarar su yi amfani da kafafen sadarwar zamani, kamar su Facebook, Twitter da Intagram wajen jawo hankalin ’yan Najeriya su sake zaben Jam’iyyar APC.

“Tabbas babu kudi a lalitar gwamnati da za a yi amfani da su domin raba wa mutane su zabe mu; lallai ku isar da wannan sako ga ’yan Najeriya,” inji shi.

A shekarar 2015 dai miliyoyin ’yan Najeriya sun tara wa Shugaba Buhari kudi ta hanyar sayen wani kati; sa’annan ’yan siyasa da yawa irin su Bola Tinubu da Atiku Abubakar da Bukola Saraki da sauransu sun yi amfani da kudadensu wajen yi masa kamfe.

To sai dai yanzu Tinubu ne kawai yake tare da Buhari, domin sauran sun zama ’yan adawa.

A farkon wannan mako ne Shugaba Buhari ya sake nada Tinubu a matsayin jagoran kamfe dinsa na neman Shugaban Kasa. Ana ganin Tinubu ya san hanyoyin da zai bi ya samo kudi domin a yi kamfe.

Abin da sauran jam’iyun adawa ke cewa

Dan takara kuma Shugaban Jam’iyyar NCP, Dokta Yunusa Tanko, ya bayyana wa Aminiya cewa zaben bana ya ki armashi ne domin jam’iyya mai mulki ta APC ta kuntata wa al’umma.

“Da gaske ne kowa ya yi likimo, duk ’yan siyasa da ’yan takara sun zura idanu domin Shugaba Buhari da jam’iyyarsa ta APC da gangan suka kawo yunwa a kasa, sun hana kudi zagayawa a hannun jama’a. ’Yan siyasa ba su da kudi, mutanen da ke taimaka wa ’yan siyasa ma ba su da kudi, don haka ta yaya kamfe zai yi armashi? Ai ba a kamfe sai da kudi a yanzu kuma duk ’yan Najeriya suna tunanin yaya za su samu abin da za su ci ne, ba wai kudin da za su kashe a siyasa ba,” inji shi.

Tanko ya kara da cewa akwai mutane da dama da suke da kudade a kasashen waje amma sun kasa shigowa da su domin wasu dokoki masu tsauri da Shugaba Buhari ya gindaya kan hada-hadar kudade.

“Don haka ne yawancin jam’iyyun siyasa suka kasa tabuka komai a wannan lokacin; babu yadda za su yi su gudanar kamfe, domin sai da kudi ake komai,” inji shi.

Da aka tuntube shi kan shirin gangamin jam’iyyu 40 (CUPP) da suka hada hannu domin mara wa Atiku Abubakar baya, sai ya ce “A’a, mu ba mu ce za mu tara wa Atiku kudi ba; burinmu shi ne mu yi kokarin kawo masa kuri’u ta hanyar shaida wa ’yan Najeriya cewa shi ne wanda ya dace ya zama Shugaban Kasa.”

’Yan siyasa sun shirya makarkashiya – ’Yan rajin dimokuradiyya

Sai dai kuma ’yan rajin dimokuradiyya sun bayyana wa Aminiya cewa yawancin ’yan siyasa sun ki yin kamfe ne domin suna so su yi amfani da kudadensu su sayi kuri’u a ranar zabe.

Shugaban Kungiyar Wayar da Kan Matasa ta Youth Initiatibe for Adbocacy Growth, Mista Samson Itodo, ya ce akwai dalilai guda uku da suka sa kamfe ba ya armashi.

“Na farko shi ne, Hukumar Zabe ta fitar da jadawalin da wuri, tun watan Janairun bara. Don haka ’yan siyasa da jam’iyyun siyasa sun samu lokaci suna ta shirye-shirye a hankali,” in ji shi.

Ya ce na biyu shi ne, “Yawancin ’yan siyasa sun kammala shiri tsaf, suna jiran ranar zabe domin su sayi kuri’u a wajen jama’a. Dalilin ke nan da suka ki sayen gishiri da sabulu su raba wa jama’a.”

Itodo ya ce dalili na uku shi ne rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyun APC da PDP. “Har yanzu akwai ’yan takara da ke kotu; don haka suna tsoron kashe kudinsu wajen kamfe domin ba su da yakinin ko za su samu nasara a kotun,” inji shi.

Shugaban Kungiyar Connected Debelopment (CODE), Mista  Hamzat Lawal, ma ya bayyana alhininsa cewa yawancin ’yan siyasa sun yi shirin sayen kuri’a ne. “Dalili ke nan da suka ga cewa babu amfanin su yi kamfe,” inji shi.

Hukumar Zabe dai ta ce ta dauki matakai da dama domin hana sayar da kuri’a. Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce babban laifi ne saya ko sayar da kuri’a.

 ’Yan siyasa ba su buga fosta  sosai– Masu madaba’u

Wani mai sana’ar buga takardu da fosta mai suna Mukhtar Abubakar da ke Titin Jema’a, a garin  Kaduna ya ce “Gaskiya ba za a hada buga fosta a shekarar 2015 da yadda ake yin ta yanzu ba saboda yanzu akasarin ’yan siyasa sun daina buga fosta kamar yadda suka saba a shekarun baya. Muna kuma ganin kamar hakan na da alaka ne da rashin kudi. Yawanci sun koma buga babban hoto ne a kan titi maimakon fosta. A shekarun baya mutum daya sai ya buga fosta dubu hamsin, amma yanzu ko dubu biyar sai an yi da gaske.”

Shi ma Kabiru wanda ake kira da KB Mai Printing, da shagonsa ke kan Titin Jema’a cewa ya yi: “Akwai canji kan yadda mutane ke kawo buga fosta a wannan karo, musamman idan aka yi la’akari da shekarar 2015. Yanzu ’yan siyasa na matse hannu domin wasunsu na ganin kamar hasara ce buga fosta saboda haka sai suka koma buga hotunansu a jikin mota, ana yawo da su cikin gari. Wasunsu kuma sai dai abokan siyasa su buga musu amma da wuya ka ga dan takara ya sa an buga masa fosta,” inji shi.