✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2019: Fafatawa ce tsakanin masu gaskiya da marasa gaskiya –El-Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana zaben 2019 da zaben da za a fafata tsakanin masu gaskiya da marasa gaskiya. Gwamna El-Rufai ya…

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana zaben 2019 da zaben da za a fafata tsakanin masu gaskiya da marasa gaskiya.

Gwamna El-Rufai ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabin maraba a lokacin kaddamar da yakin zabensa a Jihar Kaduna, inda ya kwatanta taron kaddamar da kamfe din PDP na shiyyar Arewa maso Yamma a Sakkwato da “taron barayi.”

Gwamnan ya kara da cewa PDP ta ranto mutane ne daga wasu kasashe masu makwabtaka da Jihar Sakkwato domin mutanen jihar sun ki fitowa. Sannan ya ce Jihar Kaduna ba jihar da za a bar PDP ta cuci al’umma ba ce. “Ayyukan da muka yi a Jihar Kaduna a cikin shekara uku na nuna cewa Jam’iyyar APC jam’iyya ce mai kaunar mutane kuma mai taimakonsu, ba jam’iyyar da za ta kwashe dukiyar al’umma ta raba wa wadasu daidaikun mutane ba. Wannan ne ya sa muke kira gare ku jama’a ku shelanta wa mutane cewa su sake zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu.

“Don haka idan lokacin kaddamar da yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Kaduna ya zo, ina so mutane su fito domin duniya ta gani cewa lallai mu ba mutanen Jamhuriyar Nijar muka tara a matsayin ’yan Najeriya ba. Babu abin da PDP za ta yi wa mutanen Jihar Kaduna da Najeriya baki daya. A cikin shekara 16 da suka yi, sun bar yawancin makarantun firamarenmu 4,250 cikin mawuyacin hali, inda suka bar su babu ban-daki babu rufi a ajujuwa kuma babu tagogi da kofofi, sannan sama da rabin daliban a kasa suke zama, a wasu makarantun kuma sama da kashi 90 na daliban a kasa suke zama,” inji shi.