✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2019:  ’Yan Arewa mu sake zaben Buhari

Asalamu alaikum masu karanta wannan jarida tamu mai farin jini, Aminiya. Da fatar muna cikin koshin lafiya. Allah Ya sada mu da alheri Ya kuma…

Asalamu alaikum masu karanta wannan jarida tamu mai farin jini, Aminiya. Da fatar muna cikin koshin lafiya. Allah Ya sada mu da alheri Ya kuma ba mu zaman lafiya. Duk mutanen da suke cikin  mummunan yanayi musamman matsalar tsaro da ake samu a sassan kasar nan irin su jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Zamafara da Katsina da sauransu, Allah Ya nuna mana karshensu, amin summa amin.

To a yau zan janyo hankalin mutanen Arewa ne game da zaben da ke tafe wanda za yi nan da kasa da wata daya, ina nufin na Shugaban Kasa da sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai.  Daga baya kuma za a yi na gwamnoni da majalisun jihohi.

’Yan Arewa, ya kamata mu yi karatun ta-natsu wajen zabo shugabannin da za su ci gaba da jagorantarmu na tsawon shekara hudu masu zuwa. Mu yi la’akari da shekara hudun da suka wuce abubuwan da aka yi mana da kuma fatar wadanda za a ci gaba da yi mana nan da wasu shekara hudu.

A tawa fahimtar, ba mu da wani shugaba da ya wuce mu sake zabar Muhammadu Buhari a karo na biyu saboda ya karasa dimbin ayyukan alherin da ya faro mana.

Daga cikin abububuwan tarihin da Shugaba Muhammadu Buhari ya fara sun hada da ci gaba da yashe Kogin Neja da aka dade ana ta fafutikar samar da shi, amma sai a wannan karo hakan ya tabbata.  Ka ga yanzu kai tsaye ’yan Arewa za su ci ribar kai musu kaya tasohoshin jiragen ruwa.  Wannan ba karamin alheri ba ne.

Sannan Shugaba Buhari ya sanya a yi bincike kan albarkatun man fetur da ke karkashin kasa a yankin Arewa, inda tuni har an fara ganowa a garin Alkaleri da Kaimawa a Jihar Bauchi, abin kuma har cikin Jihar Gombe.  Ka ga wannan ma ba karamin alheri ba ne ga Arewa.

Sannan ga yunkurin da ake yi na kafa matatar man fetur a Jihar Katsina inda tuni Shugaba Buhari ya kulla yarjejeniya daga Nijar, za a rika turo mai daga can ana tacewa a Katsina.  Wannan shi ma wata nasara ce.  Sannan ga yunkurin da ake yi na inganta dam din yankin Mambilla da hakan zai kara inganta samar da wutar lantarki.  Wannan ma ci gaba ne ga Arewa.

Don haka wadannan dalilai da wasu suka sa nake kira ga ’yan Arewa musamman mu da ke zaune a Kurmi mu yi kokarin sake zabar Shugaba Muhammadu Buhari a zaben da ke tafe don mu samu ci gaba a yankunmu na Arewa.

Da fatan za a kalli wannan kira nawa da idon basira. Kuma ina addu’ar Allah Ya sa a yi zabe lafiya kuma a sanar da sakamako lafiya, amin.

 

Abdullahi Hussaini Gombe ya rubuto ne daga No 83 Layin Ikwerre, Diobu, Fatakawal da ke Jihar Ribas

08036899117.