✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

36 Lion ta lashe gasar kofin Sarkin Legas

Fitaccen kulob din nan da ake kira 36 Lion Football Club  da ke yankin Badagiri a Jihar Legas ya zama zakara a gasar cin kofin…

Daga dama Manajan Daraktan bankin Skye, Mista Durosimi Kehinde-Etti da Eletu Edibo na Legas, Cif Tajudeen Badere a tsakiya yakeFitaccen kulob din nan da ake kira 36 Lion Football Club  da ke yankin Badagiri a Jihar Legas ya zama zakara a gasar cin kofin Sarkin Legas wanda aka gudanar a filin wasa na Onikan da ke tsakiyar birnin Ikko a karshen makon da ya gabata.
Kulob din ya lashe gasar ce bayan ya lallasa abokin karawarsa Bomb Blast Football Club na yankin Ikeja ci 2 da 1.
kwallaye biyu da Lawal Yusuf da Bamgbopa Bashir na kulob din 36 Lion suka zura a ragar Bomb Blast jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ya sanya kulob din 36 Lion ya lashe kofin da ake yi wa lakabi da Kofin Oba na Legas na wannan shekara.
Wasan, wanda daruruwan ’yan kallo suka halarta ya kayatar da manyan baki wadanda suka hada da Oba na Legas Mai Martaba Oba Rilwanu Akiolu da Kwamishiniyar wasanni ta jihar, Enitan Oshodi da Daraktan wasanni na jihar, Dokta Tandoh Kweku da sauran jami’an bankin Skye Bank.
Mai horar da ’yan wasan 36 Lion, Akinsola Akinrele ya bayyana godiyarsa ga Allah kan nasarar da suka samu.  Ya ce kulob din ya cancanci lashe gasar ce saboda kwarewar da ’yan wasansa suka samu.
Tuni kulob din 36 Lion ya tafi gida da kyautar Naira miliyan daya da katon kofi yayin da kulob din Bomb Blast  ya samu kyautar Naira dubu dari 750. Kulab din da ya zo na uku ya samu kyautar naira dubu dari 250.