✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun gamsu da tsare-tsaren Hukumar Kula da Harshen Larabci – Ministan ilimi

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayyana gamsuwa  kan tsare-tsare da gudumawar da Hukumar Kula da Ilimin Harshen Larabci da Nazarin Addinin Musulunci ta Kasa…

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayyana gamsuwa  kan tsare-tsare da gudumawar da Hukumar Kula da Ilimin Harshen Larabci da Nazarin Addinin Musulunci ta Kasa (NBAIS) ke yi don inganta ilimi da bayar da tarbiyya.

Ministan ya bayyana haka ne a wajen taron shekara-shekara na kasa karo na 36 da Kungiyar Malaman Koyar da Harshen Larabci da Addinin Musulunci ta shirya a  Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a ranar Larabar da ta gabata.

Ministan wanda ya samu wakilcin mukaddashin Shugaban Hukumar NBAIS, Farfesa Mohammed Safi’u Abdullahi ya ce babban dalilin da ya sanya aka kafa hukumar a karkashin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ke nan don cimma burin da gwamnati ta sanya a gaba na tabbatar da ingantuwar ilimi a Najeriya.

Ya ci gaba da cewa ma’aikatar ilimi na aiki tukuru don cimma nasarar inganta harkar ilimi da samar da kayan koyarwa tare da bayar da horo na musamman ga masu ruwa- da-tsaki a harkar ilimi nan da shekara ta 2030.

Malam Adamu Adamu ya kuma jawo hankalin kungiyar da Hukumar NBAIS su zauna cikin shirin don za su kasance cikin tsare-tsare don aiwatar da yadda za a gudanar da tsarin.

Da yake jawabi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya kalubanci ’yan ta’adda masu ta fakewa da harshen Larabci da addini suna aikata barna kan  su fito fili su daina fakewa da sunan Musulunci suna aikata munanan ayyuka.

Ya ce lokaci ya yi da al’ummar Musulmi da wadanda ba Musulmi za su hada karfi da karfe su yaki duk wani nau’in cin zarafi da kuma  kashe-kashen rayukan bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba. Sarkin Musulmin ya kuma shawarci ’ya’yan kungiyar da kada su yi sakaci su kyale kungiyar ta rushe ko ta raunana.

A jawabi Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya ce kasancewar malaman koyar da harshen Larabci da Hukumar Kula da Harshen Larabci suna tafiya tare, wata alama ce ta samun nasara.

Alhaji Shehu Idris ya yaba da namijin kokarin da NBAIS ke yi wajen tabbarar da harshen Larabci ya habaka a Najeriya bayan kwashe shekaru ana gwagwarmayar tabbatar da haka.