✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A ’yan shekarun nan biyu, ana samun rahotanni na karuwar barkewar Ciwon Shawara a daukacin jihohin kasar nan. A bara a irin wannan lokaci, an ba…

A ’yan shekarun nan biyu, ana samun rahotanni na karuwar barkewar Ciwon Shawara a daukacin jihohin kasar nan. A bara a irin wannan lokaci, an ba da rahoton jin duriyar ciwon a duka jihohin kasar nan, amma a jihohi 16 kadai hukumomi suka tabbatar da hakan.

To a bana ma, a ’yan kwanakin nan an ba da labarum barkewar ciwon a wasu sassa na kasar nan, inda aka tabbatar har wasu wadanda suka kamu a Jihar Edo sun rasu.

To mene ne ke jawo wannan annoba ta wannan ciwo na shawara ko Yellow Feber? Shekaru fiye da talatin baya, an samu saukin bullar wannan ciwo a kasar nan amma kwatsam a bara da bana sai ga shi har halaka jama’a yake kamar yadda rahotanni suka nuna. Kamar yadda muka zayyana a ’yan makonnin da suka shude, ciwon shawara ma cizon sauro ne yake jawo shi amma ba nau’in sauro mai jawo zazzabin maleriya ba, wani nau’i ne daban wato sauro nau’in Aedesegypti. Nau’in kwayar cutar da wannan sauro ke dauka ya bambanta da na Maleriya. A nan kwayar cutar birus ce sauron ke dauka mai sa ciwon shawarar. Sauron yana dauko cutar birus din ne daga wani mai ciwon ya sa wa wani.

Saboda an yi ciwon sosai a shekarun baya, yawanci mutane wadanda suka manyanta sun riga sun samu garkuwa daga kwayar cutar, ko ta alluran riga-kafi ko ta cizon sauron, don haka ko da sauron ya cije su, ya sa musu kwayar cutar, da wuya su yi ciwon. Yawanci ba ma sa sanin suna dauke da ita, domin ba sa jin wasu alamu, sai dai kawai sauro ya cije su ya dauki kwayar ya yada ciwon.

Mutane masu karancin shekaru ke nan kamar samari ’yan kasa da shekaru 30 da ’yan yara su ciwon zai fi tagayyarawa kuma su suke nuna alamun kamuwa a wannan lokaci. Alamun kuwa su ne; bayan ’yan kwanaki kamar 6 zuwa 10 da cizon sauro nau’in Aedes, za a ji alamu kamar na ciwon Maleriya, wato zazzabi da ciwon kai da ciwon gabobi da amai (wani lokaci da jini a aman ko habo), da shawara, wato idanun wasu su kada ruwan dorawa.

To, da yake sauro ne ke yada kwayar cutar, idan ana son a yaki cutar da farko sai an yi maganin sauron ke nan ta hanyar wadannan dabaru:

1. A rika tabbatarwa magudanan ruwa suna gudana sosai, ta hanyar daina zuba shara a cikinsu ko kuma rufe su ma baki daya.

2. A rika kwashe sharar unguwanni a kai-a kai.

3. Saka kaya masu rufe ko’ina a jiki a kodayaushe don gudun cizon sauro, kamar riga mai dogon hannu da safa a kafa. Shi sauron Aedes ba irin na Maleriya ba ne da ke cizo da dare kawai, shi mai sa ciwon shawara da rana yake cizo.

4. Yin amfani da gidan sauro irin na taga da kofa don rage shigar sauro dakuna.

5. Yin amfani da gidan sauro na jikin gado ko katifa yayin kwanciya.

6. Za a iya amfani da maganin feshi a daki amma a tabbatar ba kowa a ciki tukuna sa’annan a yi feshin. Idan ya gama aikinsa a bude tagogi (wadanda da ma akwai gidan sauro a jikinsu), domin iska ta fitar da maganin sauron.

Ta bangaren kiyaye ita kanta kwayar cutar kuma akwai allurar kariya, wato allurar riga-kafin kiyaye kamuwa da wannan kwayar cuta, wadda tuni wasu jihohi inda aka ba da labarin bullar ciwon an fara samarwa a cibiyoyin lafiya, inda ake wa duk ’yan tsakanin shekaru 2 zuwa 44. Haka nan ga matafiya da direbobin motocin haya wadanda za su tashi daga garuruwan da ba a ji bullar ciwon ba zuwa wadanda aka ji bullar ciwon, dole ne su ma su karbi wadannan allurai.

Wadanda suka fara nuna alamun ciwon kuma dole ne a kai su asibiti a dauki bayanai da jinin awo domin tabbatarwa ko matsalar ce, inda idan ta tabbata haka ne sai an kebe mutum an kwantar da shi an ba shi magunguna.

Na kasance a duk shekara a irin wannan lokaci sai na yi jiyya, a bana ma har kwanciya na yi domin yanzu ban fi kwana hudu da tashi ba. Shi ne nake neman shawara.

Daga Jamilu M. Adam

 

Amsa: E, da kana zuwa asibiti daidai lokacin da alamun suka fara, aka maka aune-aune da gwaje-gwaje, da tuni an gano maka matsalar an ba ka magani da ma shawarwarin yadda za ka kiyaye aukuwar matsalar da ka ce tana addabarka duk shekara.

 

Ni ma kusan a kullum sai na samu wani irin ciwon kai wanda har sai na sha masa maganin zogi mai karfi. Na je asibiti sun ba ni magani bai yi ba, dole sai na sha wanda na saba mai karfin. Shi ne nake neman shawara.

Daga Khalid Ahmed

 

Amsa: A’a da alama karamin asibiti ka je, irin sha-ka-tafin nan. Idan abu ya gagari karamin asibiti, musamman ma idan ba su yi maka wasu aune-aune da gwaje-gwaje ba, ai gaba ake karawa, wato babban asibiti ake ziyarta a yi ta bibiya da hakuri har sai an gano me ke sa maka wannan ciwon kai.

 

Ko akwai yiwuwar kamuwa da cututtuka idan mutum ya sayi kaya gwanjo ya sa bai wanke ba?

Daga Shehu M.K Suleja

 

Amsa:E, kwarai akwai yiwuwar hakan tun da wasu sun sa kayan. Ke nan yana da kyau a wanke a shanya a rana a kuma goge da dutsen guga mai zafi kafin a sa, in dai har su masu sayarwar ba sa yin wannan. Sa’annan akwai kayan gwanjon da a tsarin kiwon lafiya bai ma kamata a saya a sa ba, misali kayan ciki, irinsu soci da dan kamfai da rigar mama da ire-irensu.

 

Ni lebbana sukan yi ja su mini zafi. Jan yana kara karuwa a koyaushe. Ko hakan wata matsala ce?

Daga Adamu Dankwambo

 

Amsa: E, da alama akwai matsala amma yawanci matsalolin fata sai an gani ido da ido. Don haka yana da kyau a je a duba irin matsalar. Ka samu likita ya duba ya tabbatar.

 

Ni a wasu lokuta idan ina jin yunwa ina jin zafin ciki da kugi da karta da tashin amai.

Daga Maman Auwal

 

Amsa: E, wadannan alamu ne na matsalar ciki ko yawan gas na acid din ciki ko olsa da ire-irensu. Ke nan yana da kyau ki je asibiti a bincika idan hakan ne a ba ki magunguna.