Aminiya

Maraba da dokar hana sakin aure a Jihar Kano(4)

Ita kuwa wata matar mijinta ya sake ne kamar yadda wani rahoto ya nuna saboda ya aika mata cefane daga kasuwa tunda rana da niyyar ta yi masa girkin dare.  Ba su da da don Allah bai ba su haihuwa ba.  Abin mamaki ashe a cikin cefanen mijin ya manta bai hada da magi na Naira 50 da ya saba sanyawa a ciki ba.  Maimakon matar ta sayo ko ta aika a karbo mata bashi idan mijin ya dawo ta yi masa bayani. Ba tare da ta sanar da shi ko ta sayo magin ba sai ta bar cefanen da aka kai mata tunda rana ba yi girkin ba. Bayan Sallar Isha’i mijin ya koma gida yana shirin ya kwashi girki sai ya tarar da cefanen da ya aika ba a sarrafa ba.  Da ya tambayi dalili sai ta nuna ai bai sanya magi a ciki ba, ita kuma ta nuna ba za ta yi girkin ba. Nan take ya harzuka hakan ya sa ya sake ta.  Bayan ta koma gida da iyayenta suka turke ta don jin dalilin da ya sa ta koma gida sai ta kasa yi musu bayanin abin da ta yi.  Nan iyayenta suka nemi mijin inda shi kuma ya bayyana musu abin da ya faru.  Take iyayen suka yi mata kaca-kaca.  Sun yi kokarin su ba mijin hakuri amma ya nuna ba zai iya ci gaba da zama da ita ba, don ta riga ta zubar da mutuncinta a kan idonsa, kuma ko ya koma da ita watakila ma ya cutar da ita tunda soyayyar da yake yi mata a da ta yi kasa.  Ya dai ba su hakuri inda ya ce ta nemi wani mijin, shi kuma zai nemi wata macen da zai aura.

Sannan akwai matar da mijinta ya sake ta saboda ta dora girki sai ta shiga makwabta yin  hira alhali ta san gidan nasu ba kowa.  A lokacin da ta shiga gidan makwabtan sai ta buge da kallon talabijin ta manta ta dora girki.  Nan barci ya kwashe ta har girkin ya kone, hayaki ya fara turnuke gidan, gobara ta kusa tashi.  Cikin ikon Allah ashe mijin ya yi mantuwa ya koma gida, da shigarsa gidan sai ya ga hayaki ya turnuke ko’ina. Ya rika kiran matarsa amma  shiru. Hankalinsa ya yi matukar tashi, don ya dauka ko wani abu ne ya faru. Jin hayaniyar da ke fitowa daga gidan ne ya sa makwabta suka ankara suka shiga neman matar sai aka shaida musu ta shiga wani gida ne.

Abin ya ba mijin mamaki da haushi, ba tare da bata lokaci ba ya sake ta.

Shi kuma wani mijin kamar yadda wani labari ya nuna, ya saki matarsa ce saboda ba ta yi masa kwalliya ba. Ya ce ya shafe fiye da shekara biyar yana tare da matarsa amma bai taba ganin kwalliyarta ba. Kullum tana zaune ne da kayan da take yin aikin gida da su. Ashe takan caba ado da yin kwalliya ne idan za ta fita unguwa. Kafin mijin ya koma gida, sai ta riga shi komawa sannan ta tube kayan ta zuba a akwati sai kuma wani jikon. Labarin ya nuna haka na matukar tayar wa mijin hankali. Ya sha yi mata nasiha amma duk a banza. Wata rana mijin yana kan babur din acaba sai ya hangi wata kyakkyawar mace, ta caba ado. Har sun wuce sai ya umarci mai acabar da ya karkata akalar babur din don ya ga wannan mata. A zatonsa budurwa ce,  da ma ya fara tunanin ya kara aure, tunda matarsa ta gida ba ta yi masa ado, kullum tana zaune ne a cikin dauda. Duk da yake ba ta taba haihuwa ba, amma ganin sun shafe fiye da shekara biyar suna tare a ganinta ta tsufa, don haka babu dalilin da zai sa ta rika yi wa mijin kwalliya.

Isar mijin wajen matar ke da wuya sai ya yi mata sallama. Ita kuma sai ta daga kai ta amsa don ba ta san da wa take magana ba.  Hada ido ke da wuya sai mijin da ita suka rikice. Mijin ya yi matukar kaduwa ganin yadda matarsa ta yi kyau kuma ta yi adon da bai taba ganin ta yi haka ba. Ashe fitar da ta yi ma zuwa unguwar ba tare da sani ko amincewarsa ta yi ba. Nan ya shaida wa mai babur din abin da ke faruwa kuma ya umarci ya mayar da shi gida. Bayan matar ta koma gida ne ya taimbaye ta dalilin da ya sa take yi masa haka. Nan dai ta kasa ba shi gamsasshiyar amsa, inda daga nan ya rabu da ita ya sake wani auren.

ADVERTISEMENT

Mu kwana nan

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08097015805