✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A ba mata ilimi don inganta tarbiyya – Dokta A’ishatu Kumo

Dokta A’ishatu Abubakar Kumo, kwararriyar malama ce da ta fara aikin koyarwa tun 1996 daga matakin firamare har ta kai sakandare. Yanzu kuma ta  zama…

Dokta A’ishatu Abubakar Kumo, kwararriyar malama ce da ta fara aikin koyarwa tun 1996 daga matakin firamare har ta kai sakandare. Yanzu kuma ta  zama mai koyarwa a jami’a. A zantawarta da Aminiya ta bayyana tarihin rayuwarta da burin da ta sanya a gaba:

 

Tarihin rayuwata.

Sunana A’ishatu Abubakar, ni ’yar garin Kumo ce a Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe. A can aka haife ni kuma a can na yi firamaren Central, bayan na gama sai na tafi Kwalejin Arabiyya ta Mata (WATC) da ke Alkaleri a lokacin Gombe tana Jihar Bauchi. Na kammala  a 1985 daga nan sai na tafi ATC, Azare na yi sharar fage bayan nan sai na samu tafiya Jami’ar Bayero ta Kano na yi digirin farko a bangare Nazarin Addinin Musulunci,  inda na gama a 1994. Daga nan na tafi hidimar kasa a Fatakwal inda na yi aiki da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Ribas.

 

 

Aiki

Na fara aiki ne a 1996 a matsayin malamar firamare a Karamar Hukumar Kaltungo ina nan har zuwa 1997 sai na bar Kaltungo na dawo garin Gombe na ci gaba da aiki a firamaren Unguwar Nasarawa. Lokacin da aka bude karamar sakandare a tsakanin shekarun 2003 – 2005 sai muka koma muna koyarwa a makarantar. Haka kuma da aka kafa Jami’ar Jihar Gombe a shekarar 2006 sai na fara aiki a can.

Ina nan tare da su sai na tafi na yi digiri na biyu a Jami’ar Bayero a shekarar 2018. Sannan na yi digiri na uku a kasar Malaysiya duka a bangaren Nazarin Musulunci inda har yanzu ina koyarwa a wannan jami’a ta Jihar Gombe.

 

Kalubale

Na samu kalubale da zan kira su ’yan matsaloli kadan domin babban makasudi shi ne hada aikin gida da na koyarwa. Amma koyarwa matsalolinta ba su da yawa idan ana hutu aikin yakan ragu kadan, sai dai na gyaran jarrabawa wani lokaci. Amma da a ce mu biyu ne a gida wajen mijina. To da abokiyar zamana za ta rika dauke mini wasu ’yan aikace-aikacen, ta yadda komai zai zo cikin sauki.  Saboda idan ku biyu ne, yau ke ce ke kula da miji sai bayan kwana biyu abokiyar zamanki za ta karbe ki, ka ga a kwana biyun nan za a dan samu sauki.

 

Nasara

Alhamdulillahi na samu nasara a  matsayina ta mace da na yi karatun digiri na daya da na biyu har na uku na zama Dokta duk da cewa na yi ta kokari in yi digiri na biyu tun farko aka dan samu akasi amma daga baya na samu na yi.

 

Tufafi

A matsayina ta Musulma ina sanya sutura ta mutunci kamar yadda addinin Musulunci ya koyar hakan ya sa na fi sha’awar daura zane da riga da hijabi wato shiga ta kamala.

 

Kungiyoyi

Ina cikin wata kungiya a jami’armu sunanta Sisters Forum, kungiyar mata zalla a karkashin Kungiyar Dalibai Musulmi ta Kasa (MSSN). Sannan ina cikin Kungiyar Zakka da Wakafi.

 

Kasashen da na je

Na je kasashe da yawa cikin su kuwa har da Malaysiya inda a can ne na yi digirin digirgir har na shekara uku. Na je Turkiyya da Masar da Kasar Daular Larabawa da Habasha da sauransu.

 

Yawan iyali

Alhamdulillahi, Allah Ya albarkace ni ne da ’ya daya rak daga kanta  kuma Allah bai sake ba ni wata ba.

 

Burina a rayuwa

Babban burina in ga na taimaki al’umma kamar yadda ni ma aka taimake ni, ina so in ga na samu zarafi na wallafa littafi wanda jami’o’i  za su rika amfani da shi, su ma ’yan baya su koyi wani abu daga cikinsa.

 

Hutu

Ba na zuwa ko’ina don yin hutu, a gida nake hutuna tare da iyalaina don su samu lokacina.

 

Lambar yabo

A kasar Malaysiya inda na yi digirin digirgir an ba ni lambar yabo na wacce ta fi iya gabatar da kasidarta wato Best Presenter a cikin dalibai.

 

Shawara ga mata

A matsayina ta ’ya mace ina ba iyaye shawarar su mayar da hankali wajen ilimantar da ’ya’ya mata  saboda mace idan ta yi ilimi ana ganin amfaninsa tun daga wajen rainon ciki zuwa haihuwa. Kuma ko mace ba za ta yi karatu mai tsawo ba, a ba ta dama ta yi ko da babbar sakandare. In da hali kuma ta yi NCE ko Diploma don ta inganta rayuwarta. Su ma mazan iliminsu ba wai bai da muhimmanci ba ne na fadi haka ne saboda wadansu iyayen ba sa barin ’ya’yansu mata kwata-kwata su yi karatu sai maza.

Ita kuma mace idan ta yi ilimin al’umma ce gaba daya ta yi ilimi saboda ita ke kan gaba wajen koyar da tarbiyya, duk yaron da ya tashi bai da tarbiyya za ka ji uwarsa ake fara zagi. Za a ce ba ta ba shi tarbiyya ba.

Zan so kuma in jawo hankalin wadansu iyayen da suke kin barin ’ya’yansu su yi karatu sai talla, to su gane talla masifa ce ba abin yi ba ce ga ’ya’ya mata saboda yadda tarbiyya ke tabarbarewa a wajen talla. Komai ilimin ’ya mace idan dai tana talla sai tarbiyyarta ta yi rauni saboda tana gamuwa da maza daban-daban wadanda suka fi ta zurfin hankali da wayo a nan suke fara lalata mata tunani da  tarbiyya a karshe ka ga yarinya ta haifa wa iyayenta abin kunya a gida.