Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
A bar daliban Najeriya su yi jarabawar WAEC

Wasu dalibai na daukar darasi a aji. (Hoto: allAfrica.com)

A bar daliban Najeriya su yi jarabawar WAEC

Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta janye matsayinta na kin barin daliban Najeriya su rubuta jarabawar kammala makarantar sakandare ta WAEC a bana.

Shugaban Kwamitin Ilimi a Matakin Farko Julius Ihonvbere, ya yi mamakin sanarwar ta Ministan Ilimi Adamu Adamu, alhali ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa an yi ko ana yin abin da ya dace domin bude makarantu ga dalibai masu jarabawar kammala firamare da kuma karama da babbar sakandare.

“Sauyin matsayin ya nuna hukumomi na janyewa daga yaki da cutar coronavirus maimakon neman kariya da kuma magance ta”, inji shi.

Ya ce bayan illa ga kasa, hakan zai kawo “rudani a bangaren ilimi da damuwa ga iyaye da dalibai da kuma nuna wa kawayen Najeriya da ‘yan kasar cewa harkar iliminta kara lalacewa yake yi”.

Sanarwar ta shi na zuwa ne bayan kwamishinonin ilimi na jihohin Arewa sun goyi bayan matakin na Gwamnatin Tarayyar.

Da yake sanar da janye bude makarantun gwamnatin tarayya, ministan ya ce hukumar shirya jarabawar ta kasashen Yammacin Afirka (WAEC) ba ta da ikon yanke wa Najeriya lokacin da za ta bude makarantu.

Adamu Adamu ya ce ba za a bude makarantu ba sai an tabbatar da cewa dalibai ba za su kamu da coronavirus ba ta sanadiyyar zuwa makaranta.

A baya gwamnatin ta shardanta wa makarantu sabbin dokoki sake budewa.

Sharuddan sun hada da tabbatar da bayar da tazara da kuma samar da kayan wanke hannu da na gwada zafin jiki da na kashe kwayar cuta a dukkannin sassan kowace makaranta.