✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A biya makarantu kudin zagon na uku —Gwamnati

Minista a Ma'aikatar Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba ya ce an kara lokacin yin rajistar jarabawar NECO da kuma NABTEB

Gwamnatin Tarayya ta ce hakkin makarantun kudi ne su karbi kudin zagon karatu na uku da zarar an bude su ga dalibai masu rubuta jarabawar kammala sakandare.

Minista a Ma’aikatar Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba, ya bayyana haka yayin amsa tambaya game da ko ya dace makarantun su karbi kudin zangon na uku wanda kullen COVID-19 ta saka aka katse shi.

’Yan jarida sun yi tamabayar ne saboda la’akari da gajartar lokacin da daliban za su yi bayan bude makarantun.

Amma Nwajiuba wanda ke jawabi ga taron kwamitin yaki da cutar COVID-19 na kasa ya ce makarantun kudi kasuwanci suke yi ba aikin jinkai ba.

“A makarantun gwamnati ba za mu ce ana biyan kudin makaranta ba, yawancinsu kyauta ne, amma ya danganta da jiha.

“Amma ba idan ka kulla yarjejeriya da mai makarantar kudi ba, wanda ko yana da tausayi, dan kasuwa ne. Yana iya tausayawa amma kasuwanci yake yi ba kyauta ba.

“Don haka ya dace a fahimci cewa hakkin makarantu masu zaman kansu ne su caji kudin aikin da suka yi”, inji Nwajiuba.

— An kara lokacin rajistar NECO da NABTEB

Ministan ya kara tunatarwa cewa daliban za su fara rubuta jarabawar NECO daga ranar 10 ga watan Oktoba, da kuma bukatar dalibai da su dage da bitar karatunsu.

“Yanzu haka mun kara lokacin rajistar jarabawar NABTEB da NECO duk da cewa an kusa fara WAEC.

“Za a fara jarabawar WAEC daga 17 ga watan Agusta zuwa tsakiyar Satumba.

“Daga nan za mu fara gudanar da jarabawar NABTEB wadda za ta kai cikin watan Oktoba.

“Kimanin sati daya kafin kammala NABTEB, za a fara jarabawar NECO daga ranar 10 ga Oktoba zuwa watan Nuwamba.

Ya nuna bukatar dalibai masu rubuta jarabawa su dage da karatu da bitar darussansu, ba wasa a makarantu ba.

“Ajin karshe na da muhimmanci, kuma da shi ne ma’aunin abin da aka shekara shida ana yi a makaranta.

“Kowace jarabawa na da sakamako don haka muke bukatar malamai su ci gaba da fahimtar da su”, inji ministan.