✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A ceto asibitocin koyarwa

A labarin bin diddigi da jaridar Daily Trust ta wallafa a makon jiya, ya gano cewa asibitocin koyarwa a fadin kasar nan na cikin wani mummunan…

A labarin bin diddigi da jaridar Daily Trust ta wallafa a makon jiya, ya gano cewa asibitocin koyarwa a fadin kasar nan na cikin wani mummunan yanayi. Matsalolin da suke fuskantar sun hada da kayan aikin da suka lalace ko suka daina aiki kwata-kwata da tabarbarewar yanayin wurin aiki da rashin samun wutar lantarki da ma karancin kudaden gudanarwa. Marasa lafiya na fama da biyan makudan kudin asibiti, duk da cewa suna shafe kwanaki gabanin su sami damar likita ya duba su. A lokuta da dama, dakunan gwaje-gwaje da kuma sauran na’urorin duba masu fama da jinyar cutar daji da koda da kuma kwakwalwa sun matukar tashi daga aiki ko kuma sun gama lalacewa gaba daya. Rahoton ya kuma nuna cewa yawan majinyata na fin karfin asibitocin, wanda hakan ke shafar yadda suke sauke wani muhimmin nauyin da ke rataye a wuyansu na horas da kwararru a harkar kiwon lafiya.

Tun bayan wallafa rahoton dai ‘yan Najeriya ke ta maida martani a kan batun. Kwana guda bayan wallafa rahoton, zauren Majalisar Dattawa ya bayar da umurnin da lallai a gudanar da bincike game da batun, kamar dai yadda Sanata Dabid Umaru daga Jihar Neja, ya gabatar wa zauren. Majalisar ta dora wa kwamitinta na bangaren kiwon lafiya da ya kaddamar da zaman jin bahasi na gaggawa, game da halin da ayyukan asibitocin koyarwar kasar ke ciki kuma ya mika rahotonsa cikin mako guda. Majalisar ta kuma daddale a kan kiran Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole da ya bayyana gaban majalisar, don yin bayanin halin da asibitocin koyarwar ke ciki da kuma aikace-aikacensu. ‘Yan Majalisar Dattijan sun kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da wani tsarin da zai tallafa da kudaden da masu jinyar cutar daji da na koda ke kashewa, wajen jinya.

Yanayin da asibitocin koyarwar ke ciki tamkar manuniya ce ga irin halin da sauran cibiyoyin lafiyar kasar ke ciki. Kyafta ido don duba asibitocin Najeriya ya zama wani babban abin kunya ga kasar. A bisa kai’ida dai, asibiticin koyarwa ba su kasance matakin farko da majinyaci zai fara tunkara ba. A’a, aikinsu shi ne karbar jinyar da ta gagari asibitocin matakan farko da kuma na manyan asibitoci. Yana daga cikin aikinsu, su horar da masu karatun aikin likita da sauran jami’an lafiya. Kaico! Sai dai wadannan ba su kasance ayyukan da asibitocin ke tafiyarwa ba, sakamakon yadda sauran cibiyoyin kiwon lafiyar gwamnati suka matukar tabarbare. A sakamakon rashin na’urorin aiki da kuma na karancin kwarewar ma’aikata, a asibitocin kasa, yanzu majinyata na tunkarar asibitocin koyarwar gaba-gadi, ko da kuwa karamar cuta ce, wanda hakan ke sanya kayayyaki da ma ma’aikatan asibitocin koyarwar cikin matsi. Sakamakon hakan, yanzu wadannan asibitocin koyarwar,sun kauce daga ainihin muhimmin aikin da ke sargafe a wuyansu, wanda wannan ne dalilin da ya sa yanzu muke samun rashin wadattu da kuma kwararrun likitoci.

Mun jinjina wa Majalisar Dattijai da irin wannan hobbasa cikin gaggawan da suka yi a kan al’amarin. Sai dai muna kiran da kada a wancakalar da rahoton binciken kwamitin ya kare da kurar taskar ma’ajiyarta. Wannan muhimmin batu ne, lura da cewa yana shafar rayuka da kuma makomar kiwon lafiyar kasar nan ne. Ya zama wajibi a kan wadannan asibitocin koyarwar da su koma kan ainihin nauyin da ke sargafe a wuyansu, na horar da jami’an lafiya. Amma fa ba za mu cimma hakan ba, muddin dai matakan farko da ma manyan asibitocimu, suka ci gaba da kasancewa cikin mummunan yanayi. Sai sun kasance sun wadata da ingantattun kayan aikin da za su iya kula da majinyata, kafin matsin da asibitocin koyarwar ke fuskanta ya ragu.

Daga lokaci zuwa lokaci, masu rike da ma’akatu ko kuma masu lura da wasu kafofin gwamnati sun yi ta raki a kan ire-iren matsalolin da ke ci wa sassan nasu tuwo a kwarya. Amma wannan kawi bai wadatarwa; lokaci ya yi da za a bar yawan raki. Lallai ne su yi tunanin shayo kan wadannan kalubalen tare da samar da hanyoyin taka musu birki nan take. Akwai bukatar gwamnati ta bayar da fifiko a kan sha’anin kiwon lafiya ko kuma ta ma yi shelar dokar ta baci a bangaren. Kamata ya yi asibitocin koyarwa su zama tamkar magaryar tukewa, inda za a yi ta gudanar da nazarce-nazarce tare da samar da maslahar cututtuka masu wuyar sha’ani. Idan dai suka ci gaba da kasancewa a irin mummunan yanayin da suke ciki, a yanzu to kuwa babu kyakkyawar fata ga ‘yan Najeriya ta fuskar kiwon lafiya, wanda da damansu ba su da karfin fita ketare don samun  lafiya.

Lalacewar bangaren kiwon lafiya ya faro ne daga cibiyoyin lafiya na matakin farko, sa’annan sai abin ya ta’azzara zuwa manyan asibitoci – wanda a yanzu kuma al’amarin ya kai ga asibitocin koyarwar ma kansu. Dole ne mahukunta su taka wa lamarin birki. Lallai duk masu ruwa da tsaki a harkar su tashi tsaye wajen magance kalubalen. Ya kamata a sake yin nazarin kasafin da ake ware wa bangaren na kiwon lafiyar. Kuma a saka ido sosai a kan dukkan kwangiloli da sayan na’urori da ma gine-ginen asibitocin, don tabbatar da sun kai tsaiko. Dole ne mu ceto asibitocin koyarwa.