✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A daina nada wadanda ba su da ilimin addini jagorantar alhazai – Walin Kalgo

Shehin Malami Abubakar Atiku (Walin Kalgo) ya ce bai kamata a rika nada mutanen da ba su da ilimin addinin Musulunci a matsayin jagororin hukumomin…

Shehin Malami Abubakar Atiku (Walin Kalgo) ya ce bai kamata a rika nada mutanen da ba su da ilimin addinin Musulunci a matsayin jagororin hukumomin alhazai a kasar nan ba.

Walin Kalgo ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Bunza, inda ya ce matsayin aikin Hajji a addinin Musulunci da yadda al’ummar Najeriya suka amince da gaskiyar Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ba daidai ba ne a rika daukar wadanda ba su da ilimin addini a matsayin jami’an hukomomin alhazai a jihohin kasar nan.

Ya ce rashin daukar masu ilimin addinin Musulunci a hukumomin  ne ke kawo matsalolin da alhazai ke fadawa kan yadda za su gudanar da aikin Hajji.

“Babu shakka idan ana daukar masu ilimin addini za su rika karantar da alhazai yadda za su yi komai tun daga nan gida har zuwa Kasa Mai tsarki. Don haka ina kira ga gwamnatocin kasar nan su duba wannan al’amari da idon basira kafin lokaci ya yi,” inji shi.

Sannan ya yi kira ga malaman kasar nan su fito su yi magana a kan wannan matsala da ake fuskanta a cibiyoyin kula da al’amuran alhazai a kasar nan.