✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A daina sanya fadar Sarkin Musulmi a rudanin siyasa – Madawakin Dange

Tsohon shugaban karamar Hukumar Dange-Shuni a Jihar Sakkwato, Alhaji Bello Madawakin Dange ya shawarci ’yan siyasar jihar su daina amfani da sunan Sarkin Musulmi wajen…

Tsohon shugaban karamar Hukumar Dange-Shuni a Jihar Sakkwato, Alhaji Bello Madawakin Dange ya shawarci ’yan siyasar jihar su daina amfani da sunan Sarkin Musulmi wajen cin zarafi ko haddasa rudanin siyasa.
Madawakin dangen ya fadi haka ne a wani taron manema labarai a Sakkwato, inda ya ce Majalisar Sarkin Musulmi gida ne da ya kunshi mutane masu ra’ayi daban-daban da suka yi fice a fannonin rayuwa masu yawa, don haka ba daidai ba ne idan wani dan siyasa ya yi magana
game da abin da ya shafi siyasarsa a danganta shi da Sarkin Musulmi, domin Sarkin Musulmi shugaba ne na al’ummar Musulmin Najeriya da wasu sassan yammacin Afirka ba na Sakkwato kadai ba.
Alhaji Bello Dange, wanda tsohon shugaban ALGON ne a jihar ya ce, wasu masu son wargaza hadin kan Fadar Sarkin Musulmi suna labewa da wasu manyan jami’an gwamnati ko wata jam’iyya da sunan siyasa domin bata suna fadar.
Ya ce, siyasa tafiya take ba wani tabbaci na wane ne yau ko gobe, amma Majalisar Sarkin Musulmi tana nan ba inda za ta je, kuma wadanda ke neman bata mata suna domin kusanci da wani ko wasu na gwamnati, za su ji kunya domin hakarsu ba zata cimma ruwa ba. Ya ce Sanata Ahmed Maccido jinin sarautar Sarkin Musulmi ne, domin haka in ya yi magana da sunan daular kakkaninsa akwa bukatar a fahimci abin da yake magana a kai kafin a yi masa batanci.