Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
A dakatar da Infantino —Sepp Blatter

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) Gianni Infantino (Hoto: FIFA.com

A dakatar da Infantino —Sepp Blatter

Tsohon shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), Sepp Blatter, ya yi kira da a dakatar da wanda ya gaje shi, Gianni Infantino.

Blatter ya yi kiran ne bayan da mahukuntan kasar Switzerland suka bayar da sanarwa ranar Alhamis cewa sun kaddamar da bincike a kan wasu tarurruka da shugaban na FIFA mai ci ya yi da Antoni Janar na kasar, Michael Lauber.

Lauber da Infantino dai sun musanta aikata ba dadidai ba.

“A ganina, a bayyane yake karara cewa lallai ne kwamitin da’a na FIFA ya kaddamar da bincike a kan Mista Infantino, don haka dole ya dakatar da shi”, Inji Mista Blatter a wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato cewa ya fitar.

Sai dai kuma hukumar ta FIFA ba ta mayar da martini ga sakon da aka tura mata ba na neman jin ta-bakinta game da kalaman Mista Blatter.

Shi ma dai Mista Blatter, wanda ya jagoranci hukumar ta FIFA har tsawon shekaru 17, dakatar da shi kwamitin da’a na hukmar ya, daga bisani kuma ya haramta mishi shiga duk wata harka ta kwallon kafa bayan da hukumomi a Switzerland suka kaddamar da bincike a kanshi.

Har yanzu ana ci gaba da binciken kuma har yanzu ba a gurfanar da Blatter, wanda ya musanata aikata ba daidai ba, a kotu ba.

Binciken dai ya danganci wasu kudi ne Franc na Switzerland miliyan biyu da aka bai wa shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Turai na wancan lokacin, Michel Platini, a shekarar 2011 da amincewar Blatter.

Blatter da Platini sun tsaya kai da fata cewa kudin na wani aiki ne da Platini ya yi shekara 10 kafin nan.

An haramta wa Blatter shiga harkar kwallo har tsawon shekara takwas ne, amma da ya daukaka kara aka rage hukuncin zuwa shekara shida.

Shi ma Platini haramcin shekara takwas din aka kakaba masa, amma daga bisani aka rage zuwa shekara hudu.