✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A dakatar da masarar da aka shigo da ita daga waje – Farfesa Salihu

Wani masani kan harkokin noma a Nijeriya kuma malami a sashen binciken aikin gona dake Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Farfesa Salihu Adamu Dadari ya…

Wani masani kan harkokin noma a Nijeriya kuma malami a sashen binciken aikin gona dake Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Farfesa Salihu Adamu Dadari ya yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari ya taimaki manoman kasar nan, ya kare masu darajar dimbin kayayyakin amfanin gonar da suka noma a daminar bana. 

Farfesa Salihu Adamu Dadari ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya. Ya ce a bana Allah Ya baiwa talakawan Najeriya ikon yin noma mai tarin yawa kuma ya saukar da ruwan sama wadatacce, don haka manoma sun yi noman shinkafa da masara da sauran kayayyakin amfanin gona fiye da kowace shekara.

Ya ce yanzu manoman Najeriya suna son gwamnati ta ba su kariya na ganin sun sayar da amfanin gonar da suka noma da daraja. “Gwamnati ta kafa kasuwannin sayen kayayyakin amfanin gona masu tsari wadanda za su sayi kayayyakin amfanin gonar da manoma suka noma a bana. Kuma ta sanya farashi kan kayayyakin amfanin gonar da manoma suka noma a bana, kuma ta fito da kudi ta sayi rarar amfanin gona da manoma suka noma ta adana a rumbunanta. Kuma matukar shugaban kasa yana son Najeriya ta tsaya a matsayinta na cigaba da akin noma a rika aikawa da kayayyakin amfanin gonar da aka noma a Najeriya zuwa kasashen waje. Domin manoman kasar nan su ji dadi, tattalin arzikin Najeriya ya farfado.” 

Har’ila yau ya yi kira ga shugaban kasa ya dakatar da maganar masarar nan da ake cewa an shigo da ita daga kasashen waje. Saboda wannan abu zai jefa manoma cikin bala’i kuma zai rushe alkawarin da gwamnatin Buhari ta yi wa mutanen Najeriya na bunkasa harkokin noma.