✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A duba kalaman A’isha Buhari a game da kashe-kashen al’umma

“Dole ne mutane su fito su yi magana. Dukkan abin da ba daidai ba, lallai ne jama`a su fada, ko mene ne.” Wasu daga cikin…

“Dole ne mutane su fito su yi magana. Dukkan abin da ba daidai ba, lallai ne jama`a su fada, ko mene ne.” Wasu daga cikin kalaman uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari Hajiya A`isha Buhari kenan a lokacin da ta kai ziyara daya daga cikin sansanin `yan gudun hijira na Dakin Baki da ke kusa da Katsina babban birnin Jihar Katsina a karshen makon da ya gabata, jihar da ta kai wa ziyarar gani da ido a karon farko tun bayan da ta afka cikin annobar mhara `yan ina da kisa da kuma sace mutane don neman kudaden fansa.

Hajiya A`isha Buhari ta jaddada cewa lallai mutane su fito su yi magana a kan wadannan kashe-kashe da sace mutane don neman kudin fansa, da suka zama abin damuwar da idan har ba a kawo karshensu ba, to, za su iya gamawa da kowa. Ta ci gaba da cewa lokacin da Sakataren gwamnatin Jihar Katsina ya yi magana a kan mummunan yananyin ta`addancin `yan ina da kisan da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da jihar ta shiga, ta aika wa da dukkan Hafshoshin tsaron kasar nan jawabin nasa inda ya ce ko dai su fito su taimaka, ko su bari a kashe su duka.

Annobar mahara `yan ina da kisan da ta addabi Jihohin Kaduna da Zamfara, ta afkawa Jihar Katsina da ke makwabtaka da jihohin biyu, tun shekaru biyu da suka wuce da sunan sace-sacen shanu, zuwa karshen shekarar da ta gabata ta rikide ta koma ta kashe-kashe da sace mutane don neman kudin fansa, irin yadda dai ta fara ta kuma zama a Jihohin Kaduna da Zamfarar.

A Jihar Katsina Kananan Hukumomin jihar takwas da suke kan iyaka da dajin Rugu annobar maharar `yan ina da kisa ta fi kamari. Zuwa yanzu za ta yi wuya a samu awa 24 , wato rana da yini  ba ka ji labarin an kashe ko sace mutane a kauyukan wadancan Kananan Hukumomin takwas ba na jihar ta Katsina .

Kananan Hukumomin su ne Sabuwa da Faskari da Dandume da Kankara da Danmusa da Safana da Batsari da Jibiya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa zuwa karshen makon jiya akwai `yan gudun hijira dubu 25 da 988 a sansanonin `yan gudun hijira takwas da ake da su a jihar kamar haka:- Katsina 1,707, Batsari 18,544, Kurfi 135, Faskari 1,440, Kankara 2,426, Dandume 513, Jibiya 616, Safana 607.

Wata babbar matsalar da ake fama da ita a yankunan da wannan annoba ta yi kamari, ita ce tabarbarewar harkokin yau da kullum, ta yadda tafiye-tafiye daga gari zuwa gari daga kauye zuwa kauye, walau don sada zumunci ko harkokin kasuwanci duk sun faskara. Ta kai matsayin da yanzu akwai hanyoyi irin su Safana zuwa Batsari, Mararrabar Kankara zuwa Sheme da wasu hanyoyin da mutane ba su iya bugun gaba su bi su, walau da dare ko da rana.

Rahotanni daga yankunan sun tabbatar da cewa in dai ba dauki daga  Allah SWT aka samu ba, kamar yadda a wadancan yankuna manoma ba su samu yin noman ranin bana ba, to akwai fargabar noman daminar ma ba samuwa zai yi ba.

Mai karatu kenan mutanen yankunan za su shiga wata akuba kenan. Gudun afkawar haka ta sanya a kwanakin baya da Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman yake karbar bakuncin tsohon Ministan Ayyukan gona a fadarsa, aka ji Sarkin yana fadawa Ministan cewa ya fadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san yadda zai kawo karshen wannan rashin tsaro da ya afkawa jihar, Sarki ya jaddada cewa Manoma da Makiya duk sun bar gidajensu da gonakinsu.

Annobar rashin tsaron a wasu sansan Jihar Katsina ita ta haifar a bana ba a yi hawa da sauran shagulgulan Sallah ba, kamar yadda aka saba yi duk shekara a Masarautun jihar biyu, wato Katsina da Daura. Tuni Masarautun biyu suka ba da sanarwar ba abin da za a yi, da ya wuce a je Sallar Idi, sannan a ci gaba da yin addu`o`I a duk lokacin da aka yi sallolin farilla biyar da ta Juma`a, da kuma a dukkan inda akwai wani taron jama`a da fatan Allah Ya kawo karshen wannan annoba, tare da wanzar da zaman lafiya kwanciyar hankali da karuwar arziki a jihar da ma kasa baki daya.

A Masarautar Daura dai an ci gaba da addu`o`in Allah Ya bayyana Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba da wasu `yan bindiga suka sace tun a ranar 1 ga watan Mayun da ya gabata a kofar gidansa da ke Daura a wancan rana bayan Sallar Magariba. Ba a ma taba sace babban mutum da aka dauki irin wannan lokaci na sama da wata guda ba tare da jin duriyarsa ba daga wadanda suka sace shi irin Magajin Garin na Daura ba.

Tabbas kiran na uwargidan shugaban kasa kira ne mai muhimmanci da ya kamata kowane dan kasa nagari ya saurareta, ya kuma san ta wace hanya zai yi maganar da za ta kawo gyara a kan yadda za a kawo karshen wannan annoba ta rashin tsaro da zaman lafiya da ta mamaye kasa.

Da ma uwargidan shugaban kasar ta sa ba yin bara a kan muhimman batuwawan da suka shafi kasa da yadda za a gyara su.

Alal misali a waccan shekarar a hira da ta yi da Sashen Hausa na BBC Landan, ta koka a kan wasu da suka kewaye mijinta (`yan shan kai), da ta yi zargin su ke hana shi gudanar da ayyukan da za su tallafawa jama`a. Tana mai cewa ita ba ta ma san wadancan mutane tare da maigidanta a lokacin da yake yakin neman zaben 2015.

Kodayake kamar yadda Hajiya A`isha Buhari ta nema, lallai akwai bukatar `yan kasa su rika magana a kan muhimman batutuwan kasa da yadda za a shawo kan su, kasancewar mulkin dimokuradiyya ake yi, mulkin da ya ba da damar kowa ya tsoma bakinsa . Amma kuma akwai bukatar komai za a fada ya tafi a kan hanyar yadda za a samu gyara, kamar yadda Hadisin Manzo SAW yake cewa “Ka fadi alheri ko ka yi shiru.” Ba kowace magana mutane za su yi ba, musamman a kan batu mai sarkakiya irin na tsaro.

Ita kuma Hajiya A`isha Buhari akwai bukatar a duk lokacin da ta samu sukunin zance da maigidanta ta rika fada masa ya kara bayar da kudade ga jami`an tsaro da suke yaki da `yan ta`adda masu tada kayar baya a sassa daban- daban na kasar nan, domin ba sau daya ba an sha jin Babban Hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai yana kokawa a kan irin yadda rashin wadatattun kudi ke dakile yakin da suke yin da `yan ta`adda a kasar nan.

A karshe ina rokon Allah SWT Ya sanya ibadun Azumin watan Ramadan da muka gabatar sun zama karbabbu a wajen Allah, tare da zama sanadin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da karuwar arzikinmu baki daya. BARKA DA SHAN RUWA kuma BARKA DA SALLAH. Allah Ya maimaitamana amin summa amin.