✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A duba watan Shawwal ranar Juma’a —Sarkin Musulmi

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), a karkashin jagorancin Babban Shugabanta Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ta bukaci Musulmi da…

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), a karkashin jagorancin Babban Shugabanta Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ta bukaci Musulmi da su fara duban watan Shawwal ranar Juma’a.

Sakatare-Janar na Majalisar, Farfesa Salisu Shehu, ya fadi haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

A cewarsa, bisa ga shawarar Kwamitin Duban Wata na Kasa, ranar Juma’a 22 ga watan Mayun 2020, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Ramadan 1441, ita ce rana ta farko ta duban watan.

“Sai dai kuma, a wannan yinin, wata zai fadi ‘yan mintuna kadan kafin rana, lamarin da zai sa  ganin jinjirin wata ya yi matukar wahala.

“Duk da haka, a bisa koyi da Sunnar Annabi Muhammad, Babban Shugaban na kira ga Al’ummar Musulmin Najeriya da su duba jinjirin wata da zarar rana ta fadi da yammacin Juma’a 22 ga watan Mayun 2020, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Ramadan 1441”, inji Farfesa Shehu.

Ya kuma ce Sarkin Musulmin na yi wa Al’ummar Musulmin Najeriya da ma na duniya baki daya barka da Azumin Ramadan, yana addu’ar Allah Ya sa mu ga na badin-badada.

“Da wannan muke kira ga Musulmi a fadin Najeriya su saurari sanarwa daga Mai Alfrma Sarkin Musulmi game da ajiye Azumin Ramadan na bana.

“Baya ga tabbatattun shugabannin addinin Musulunci da na gargajiya a ko wanne yanki, za a iya tuntubar mambobin Kwamitin Duban Wata na Kasa don ba da sahihan rahotanni game da ganin jinirin watan”, inji sanarwar.

Yain da take tunatar da Musulmi game da wajibcin bayar da Zakkar Fid-da-kai da nufin tallafa wa marasa galihu a cikin al’umma, Majalisar ta bukaci a tabbatar abin ya kai ga wadanda suka cancanta.