✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A fadada da cin zarafin yara ta hada da kare daliban a jami’o’i – Osowobi

Babbar Daraktar Kungiyar Yaki da Fyade (Stand to End Rape Initiatibe), Misis Oluwaseun Ayodeji Osowobi, ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa ta fadada…

Babbar Daraktar Kungiyar Yaki da Fyade (Stand to End Rape Initiatibe), Misis Oluwaseun Ayodeji Osowobi, ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa ta fadada dokar cin zarafin mutane ta shekarar 2015, domin ta kare cin zarafin dalibai a makarantu.

Daraktan Kungiyar Stand to End Rape Initiatibe, ta yi kiran ne a wajen taron wayar da kai da daliban da ke karatu a sashen kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) a Tsangayar Mulki ta Jami’ar Ahmadu Bello  da ke Zariya suka shirya.

Ta ce matsalar fyade a manyan makarantun Najeriya ta zama wata barazana a tsakanin malamai da dalibai maza da mata inda lamarin ke neman daukar matakan gaggawa.

Ayodeji Osowobi ta ce, malamai na amfani da razana dalibai don su biya bukatunsu na son rai ta hanyar kayar da su a jarrabawa ko da suna da kokari ta hanyar yin amfani da malamai abokansu.

Babbar Daraktar ta bukaci mahukuntan jami’o’i su samar da ofishin kula da daliban da aka ci zarafinsu ko ake neman cin zarafinsu da nufin daukar matakin gaggawa.

“Saboda  samar da kudurin hana fyade a makarantu ne kungiyar ta fito don fadakar da malamai da dalibai illar da fyade ke yi ga al’umma ba wanda ake yi wa ba ne kadai take shafa,” inji ta.

A nasa tsokacin  Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Ibrahim Garba wanda Mataimakinsa Mai Kula da Bangaren Karantarwa Farfesa Ameh ya wakilta ya ce taron fadakarwar na da muhimmanci ga jami’ar da kasa baki daya inda kuma za a yi kokarin kare aukuwar matsalar a jami’ar.

Farfesa Garba ya ci gaba da cewa Jami’ar Ahmadu Bello ta yi fice wajen bincikowa tare da samar da mafita ga matsalolin da suka shafi harkar koyo da koyarwa.

Ya kuma bukaci mahalarta taron su yi amfani da abin da da aka gabatar aka kuma tattauna a wajen taron.

A jawabin Shugaban Tsangayar Mulki kuma Shugaban Sashin Nazarin Harkokin Kananan Hukumomi, Farfesa Bashir Jumare ya bayyana taron a matsayin mai ilimantarwa.

Farfesa Jumare ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen cin zarafin mata da maza a makarantu da wadanda ba su a makaranta.

Tun farko a jawabin maraba Ko’odinetan taron, Dokta Abdulhamid Abdullahi ya ce taron shi ne karo na uku da sashin ke shiryawa.

Dokta Abdulhamid Abdullahi ya ce taron fadakarwar zai ankarar da dalibai kan yadda za su san hakkokinsu da kuma kare aukuwar fyade a makarantu.

Ya bayyana Misis Oluwaseun Ayodeji Osowobi a matsayin Jakadiyar Jami’ar da kuma Sashin Nazarin Mulkin K ananan Hukumomi bisa amincewar da ta yi na ta zo ta tattauna da dalibai ta kuma karfafa musu gwiwar tsayawa don kare hakkokinsu.