✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A gagauta zaben kungiyar masu horar da ’yan wasan kwallon kafa ta Karamar Hukumar Lafiya – Yusuf

An yi kira ga shugabannin Kungiyar Masu Horar da ’Yan Wasan Kwallon Kafa ta Kasa a Jihar Nasarawa su gaggauta  gudanar da zaben shugabannin kungiyar…

An yi kira ga shugabannin Kungiyar Masu Horar da ’Yan Wasan Kwallon Kafa ta Kasa a Jihar Nasarawa su gaggauta  gudanar da zaben shugabannin kungiyar na Karamar Hukumar Lafiya  da ke jihar.

Tsohon mai tsawatarwa na kungiyar a karamar hukumar, Malam Suleiman Aliyu Yusuf ne ya yi wannan kira a zantarwarsa da wakilinmu a karshen makon jiya a Lafiya. Ya ce jim kadan da sanar da fara sayar da fom din takarar mukaman reshen kungiyar ta Karamar Hukumar Lafiya shi da wadansu mambobin kungiyar sun sayi fom -fom sun cika sun mika, amma har yanzu a cewarsa ba a sanar da su ranar zaben ba, ba a kuma bayyana musu dalili ba.

Ya alakanta jinkiri da ake samu wajen shirya zaben kan son zuciya da a cewarsa wadansu shugabannin kungiyar a jihar ke nunawa inda ya ce zai yi wuya a samu ci gaba mai ma’ana a duk inda aka ce babu shugabanni na kwarai.

Ya ce shi ya sa ake samun koma-baya a harkokin kungiyar reshen karamar hukumar inda ya bukaci mahukuntan kungiyar ta kasa da ta jihar da sauran hukumomin da ke shirya zaben su gaggauta yin haka don samun ci gaba.

Malam Suleiman Aliyu ya kuma shawarci mambobin kungiyar na jihar da kasa baki daya da su rika hada kai don samun ci gaba saboda a cewarsa a yanzu babu kyakkyawan dangantaka a tsakaninsu wanda hakan a ganinsa ba alheri ba ne.