✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A hada tantancewa da kada kuri’a a zabe mai zuwa

A yayin da ya rage wata daya da ’yan kwanaki a gudanar da zaben Shugaban Kasa da sauransu hukumar zabe ta himmatu wajen bayyana matakan da…

A yayin da ya rage wata daya da ’yan kwanaki a gudanar da zaben Shugaban Kasa da sauransu hukumar zabe ta himmatu wajen bayyana matakan da ta dauka domin tabbatar da ganin ta gudanar da sahihin zabe da kowa zai yarda da shi a kasar nan.

Yanzu haka dai hukumar tana ta kokarin sanar da jama’a hanyoyin da za ta bi domin ta samun damar cimma burinta na samun zabe karbabbe. Daga cikin matakan da ta sanar akwai batun tantance masu zabe daga baya kuma su sake komawa su kada kuri’arsu.

Wannan tsarin da hukumar zabe ta fito da shi na raba tantancewa da kada kuri’a yana haifar da jinkiri wajen gudanar da zabe tare da wahalar da masu kada kuri’a da kuma jami’an zaben.

A karkashin wannan tsari masu zabe za su yi layi ne domin a tantance su, za a rufe tantancewar ne da karfe biyu na rana sannan sai a kira wadanda aka tantance su koma su karbi takardar zabe mai dauke sunayen jam’iyyu domin su kada kuri’arsu.

A yayin tantancewar ana amfani da na’urar tantance masu zabe inda za a gwada yatsunsu a tabbatar da sun yi daidai da wanda suka yi rajista da su, sannan sai a sanya wa mutum alamar da za ta nuna an tantance shi, sai ya koma ya zauna ya jira lokacin kada kuri’a.

Wannan tsarin yana daukar lokaci sosai domin a yayin tantance yatsun ana samun matsala wurin tantance wadansu mutane saboda na’urar takan ki tantance su sai an yi ta maimaitawa, wani lokacin kuma gaba daya duk yadda aka yi ba za ta karbe shi ba. Wannan yakan sanya maimakon a kammala tantancewar a lokacin da aka tsara sai a wuce lokacin.

Shi ya sanya idan aka fara kada kuri’a a kan dauki lokaci mai tsawo. Misali, a zaben Shugaban Kasa na shekarar 2015 wannan tsarin ya sanya an ci gaba da kada kuri’a har karfe biyu na dare a wasu wuraren, kuma a cikin masu jira su kada kuri’un nasu a wannan lokacin har da mata, masu aure da kuma marasa aure da ’yan mata.

Ganin matsalar da aka fuskanta dangane da raba tantancewa da  kada kuri’a ne ya sanya a wasu rumfunan zabe a wancan lokacin jami’an zabe suka yanke shawarar a rika bayar da dama ga duk wanda aka tantance ya wuce ya kada kuri’a ba sai ya jira an sake kiransa ba.

Hakan ya taimaka wajen kammala zaben da sauri.

Saboda haka ya kamata hukumar zabe ta bi wannan tsarin na hada tantancewa da kada kuri’a a zabe mai zuwa domin saukaka wa masu zabe da jami’anta da sauran wakilan jam’iyyu. Domin manyan matakai guda uku ne ko hudu ake bi a lokacin zabe. Akwai tantancewa da kada kuri’a da kuma kidayawa, sannan sai a sanar da sakamakon zaben da aka yi a rumfar, daga nan kuma sai a tafi da sakamakon wurin tattarawa.

A cikin wadannan matakai, tantancewa ce ta fi daukar lokaci, saboda haka idan aka hada su gaba daya aka yi kai-tsaye za a rage lokacin da za a dauka ana kada kuri’a da kidaya da rubuta sakamakon zaben. Sannan ba za a kai dare sosai ba da har za a iya jefa masu zabe da jami’an zabe cikin hadari ba, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalar tsaro.

Ya kamata hukumar zabe ta rika nazarin yadda aka gudanar da kowane zabe, idan ta ga akwai matsala sai ta gyara, maimakon ta rika bin tsari daya da aka saba amfani da shi, ko da yana haifar da matsala.

Kamata ya yi a fara gudanar da kada kuri’a da karfe takwas na safe a kammala da karfe shida na yamma, kuma duk wanda ya kada kuri’a ya tafi gida a bar jami’an zabe da wakilan ’yan takara su yi aikinsu, hakan zai rage cinkoso a rumfar zabe tare da sauwake wa  kowa wahalhalun da za a iya fuskanta