✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A karon farko an karrama Amirul Hajj na jihar Katsina

A ranar Alhamis din da ta wuce ne Kungiyar ‘yan jaridun da suke aiko da rahotannin aiyukan Hajji na 2019 a karon farko a tarihin…

A ranar Alhamis din da ta wuce ne Kungiyar ‘yan jaridun da suke aiko da rahotannin aiyukan Hajji na 2019 a karon farko a tarihin Kungiyar suka karrama Amirul Hajjin 2019 daga Jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal.

‘Yan Kungiyar sun ce, sun lura da irin yadda ya gudanar da aiyukan shi a can kasa mai tsarki ba tare da nuna kasala ko bambanci a tsakanin alhazai ba, hasali ma a cikinsu yake zuwa ya zauna domin magance duk wata matsalar da ta ta so.

Wannan hali da aiki ya ja hankalin ‘yan Kungiyar har yasa suka taru da sunan Kungiyar suma suka karrama shi a karon farko kamar yadda suka ga irin abubuwan da ya yi a tarihin mutanan da suka zo da wannan mukami na Amirul Hajji.

Alhaji Kasimu Abdo, daga Jahar ta Katsina na daya daga cikin mutanan da suka shaida kuma suka yaba da irin aiyukan shi Alhaji Muntari Lawal, mutumin da ya ce, ya ba kowa mamaki a yadda ya gudanar da aiyukan shi tun daga gida har can kasa mai tsarki.

Anan ma ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba shi irin wannan matsayi a matakin kasa. An dai yi wannan bikin karramawar ce a hotel din Stone Hedge da ke Abuja.