✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A kawar da bambanci a Libya

Gamayyar wasu kasashen yammacin duniya da kuma wasu na Larabawa, sun yi kiran a gaggauta kawo karshen rikicin da ake fafatawa na neman kama iko…

Gamayyar wasu kasashen yammacin duniya da kuma wasu na Larabawa, sun yi kiran a gaggauta kawo karshen rikicin da ake fafatawa na neman kama iko da Tripoli babban birnin kasar Libya.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da ba a saba gani ba, Amurka da Birtaniya da Faransa da Italiya da Masar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa, sun yi kira a koma tattaunawa a karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya don kawo karsahen rikicin.

An fara dauki-ba-dadi ne kan neman kwace iko da babban birnin na Libya, lokacin da jagoran ’yan tawaye, Janar Khalifa Haftar ya kai hari a kan birnin.

Ya yi hakan ne a yunkurinsa na karbe birnin daga hannun Gwamnatin Libya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da sauran wasu kasashe.

To amma bayan sama da wata uku uku dakarun ’yan tawayen na barin wuta, hakarsu ba ta cimma ruwa ba, sai ma koma baya da suka samu.

Hakan ya jawo asarar  rayukan mutane kusan dubu daya.

Janar din dai yana samun goyon baya musamman daga Gwamnatin Masar da ta Hadaddiyar Daular Larabawa.

Tun a baya dai Shugaban Gwamantin  Libya Mista Serraj ya ce ya yi wa Haftar tayin ba shi wasu mukamai domin a samu maslaha, a daina zubar da jini, amma Shugaban ’yan tawayen ya nemi yi masa makarkashiya da zagon-kasa, kamar yadda Shugaban ya ce.