✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A makon gobe kulob din Arsenal zai san matsayinsa a gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai

A ranar Laraba 21 ga watan Agusta ne ake sa ran kungiyoyin kwallon kafa da dama ciki har da na Arsenal da ke Ingila za…

Kocin Arsenal Arsene WengerA ranar Laraba 21 ga watan Agusta ne ake sa ran kungiyoyin kwallon kafa da dama ciki har da na Arsenal da ke Ingila za su fafata a gasar neman hayewa gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai da aka fi sani da UEFA Champions League.
Idan ba a manta ba, kungiyoyin kwallon kafa da suka kasance na hudu a gasar rukuni-rukuni na kasashen su ne za su fafata a tsakaninsu don tantance wadanda za su haye gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai da ake sa ran farawa a watan gobe.
Kamar yadda jadawalin fafatawar ta nuna, kulob din Arsenal da ke Ingila zai hadu da na Fernebache da ke Turkiyya ne a wasan farko a ranar Laraba 21 ga watan Agusta a Turkiyya yayin da za a yi wasa na biyu a ranar 28 ga watan a Ingila.
Kulob din PSb da ke Holland kuma zai hadu ne da na AC Milan da ke Italiya yayin da na Lyon zai hadu da Real Sociedad.
kungiyoyin kwallon kafa goma ne za su fafata don zakulo biyar daga cikin wadanda za su haye gasar zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai a watan gobe.