Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

A makon gobe za a yi zaben cike gurbi na dan Majalisar Jihar Filato

Shugaban Hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban Hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu

Hukumar Zabe ta Kasa [INEC] ta sanya ranar 3 ga Agusta mai zuwa a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben cike-gurbi na dan Majalisar Dokokin Jihar Filato a mazabar Pengana da ke Karamar Hukumar Bassa.

Hukumar INEC za ta gudanar da zaben cike-gurbin ne a mazabar sakamakon rasuwar Dan majalisa Ezekiel Afon Bauda wanda ya rasu, lokacin da ake tsakiyar bikin murnar cin zabensa karo na biyu, a gidansa da ke garin Jos a zaben da ya gabata.

ADVERTISEMENT

Mista Yakubu Sanda na Jam’iyyar APC da Mista Yakubu Busa Buji na Jam’iyyar PDP ne za su fafata a zaben cike-gurbin.

Da yake zantawa da Aminiya kan zaben, dan takarar Jam’iyyar APC Mista Yakubu Sanda, ya ce idan ya samu nasara da yardar Allah zai yi iyakar kokarinsa karbo dukkan hakkokin al’ummar  mazabar daga Gwamnatin Jihar Filato.

ADVERTISEMENT

Ya ce zai kuma isar da dukkan koke-koken al’ummar mazabar ga gwamnatin, don ganin a share musu hawaye.

Mista Yakubu Sanda wanda ya tsaya takarar kujerar sau 4, ya yi kira ga al’ummar mazabar su zabe shi, don su tafi da gwamnatin karamar hukuma da ta jihar da kuma ta tarayya, don su kai ga samun biyan bukata.

Shi ma da yake zantawa da Aminiya dan takarar Jam’iyyar PDP, Mista Yakubu Busa Buji ya ce  kishin al’ummar mazabar ce, ya karfafa masa  gwiwar sake fitowa takarar.

Ya ce al’ummar mazabar sun zabi ’yan majalisa da dama a baya, amma ba su ga wani abu na ci gaba da suka kawo musu ba.

Ya ce idan Allah Ya sa ya samu nasara zai tsaya ya ga cewa ya samo wa al’ummar mazabar abubuwan da suke bukata.

Ya ce gaskiya a mazabar ana  fama da matsalolin rashin ruwan sha da hanyoyin mota da kuma yaran da suka kammala makarantu  ba su samu ayyukan yi ba.

Ya ce idan ya samu nasara zan tsaya wajen ganin an warware wadannan matsaloli.