✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A mara wa gwamnati wajen bunkasa ilimi – Sarkin Jama’a

Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad ya yi kira ga jama’a su mara wa Gwamnatin Jihar Kaduna baya a kokarinta na bunkasa ilimi…

Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad ya yi kira ga jama’a su mara wa Gwamnatin Jihar Kaduna baya a kokarinta na bunkasa ilimi a jihar tun daga tushe.

Sarkin ya yi wannan kira ne  lokacin da yake amsar bakuncin daliban makarantar Praise Dibine Academy da ke garin Kafanchan a lokacin da suka kai masa ziyara a fadarsa.

Sarkin ya ce wajibi ne ga duk wani mai ruwa-da-tsaki a bangaren ilimi ya bayar da cikakken goyon baya wajen ganin gwamnati ta cimma muradinta na farfado da ilimi. Sai ya shawarci daliban da suka kawo masa ziyara su mayar da hankali wajen fahimtar abin da ake koya musu.

Da yake jawabi, Shugaban Kungiyar Iyaye da Dalibai na Makarantar, Malam Shehu Dada ya yaba wa Sarkin bisa damar da ya ba su na kawo masa ziyara a fadarsa don bai wa daliban damar ganin yadda ake gudanar da harkoki a fada.

Shugabar Makarantar Misis Celestina Agbu ta bayyana farin ciki ga masarautar wadda makarantar ke karkashinta tare nuna gamsuwa da irin jagorancin da Sarkin yake nunawa a shugabancinsa.