Search
Subscribe
A matse nake in yi aure – Saima Muhammed

Saima Muhammed

A matse nake in yi aure – Saima Muhammed

Fitacciyar jarumar nan ta Kannywood, Saima Muhammed ta ce ko gobe ta samu miji za ta sake yin aure.

Jaruma Saima Muhammed ta dade tana jan zare a Masana’antar Kannywood, duk da cewa ba kowane irin fim take fitowa ba, kasancewar ta ce sai ta zabi fim din da take tunanin zai koyar da mutane wani abin kirki.

Ga duk wanda ya san jarumar  da rawar da ta taka a Masana’antar Kannywood, ya san an daina jin duriyarta, wanda hakan ya sa jarumar ta bayyana cewa ko a can baya ta dauki hutu domin ganin an samu canji a yanayin fina-finan masana’antar.

Daga cikin fina-finan da jarumar ta taka rawa da ya yi fice akwai fim din Zuri’a, inda jarumar ta fito a matsayin matar Ali Nuhu, daga baya ta dauki cutar kansar mama, wanda saboda haka ta umarci mijinta Ali Nuhu ya auri Zainab Indomie, inda da kanta ta rika rokon Zainab din ta auri mijinta saboda cutar da take fama da ita. Har daga baya ta amince ta aure shi.

A wata hira da Saima ta yi da BBC, ta bayyana cewa ta shiga Masana’antar Kannywood ce domin son ci gaba da kuma kokarin yin wani abu mai kyau da mutane za su rika tunawa da ita.

Sannan ta ce yanzu babban burinta a duniya shi ne ta yi aure, inda ta ce tana fata Allah Ya kawo mata miji.

“Na shiga masana’antar ce saboda ina son ci gaba, ina son yin wani hobbasa mai kyau da mutane za su gani su yi koyi da mu. Ko lokacin da na fara, idan ka kawo min labarin fim, idan na ga shirme ya fi yawa sai in ce ba zan yi ba. Ko a baya-bayan nan, an rika magana a kan an cika waka da sauransu. Sai in dauki hutu in je in dawo, watakila idan na ga abin ya yi min sai in ci gaba.

“Har na je Kaduna na yi fim guda daya, amma kamar yadda na fada sai na zabi fim da nake so. A zo a ce kawai an kawo wane ne mijina, za mu fito mu yi ta rawa muna waka. Ba zan karbi wannan ba. Zan karbi wanda zai koyar da mutane wani abu ne. Daga nan sai na yi aure, na auri wani dan asalin kasar Kongo Brazabille, amma mun rabu.”

Game da sake aure Saima ta ce, “Aure rai ne da shi. Allah ne Ya halicci aure Ya halicci saki duk da cewa ba Ya son saki. Dole sai an yi hakuri domin zama da mijin yanzu. Duniya ce ta zo karshe, ba wai ’yan Kannywood ba ne kawai. Amma da yake mun fito da kanmu duniya, shi ya sa ake ganinmu. Amma ba a kanmu ba ne kawai.

“A  taya ni da adu’a, a matse nake in yi aure. Ko gobe na samu miji zan yi aure,” inji ta.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin