✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A na shigowa da tan miliyan daya na albasa Najeriya duk shekara

A  duk shekara ana shigowa da tan miliyan 1.1 na albasa, duk da kasar nan ce ta biyu wajen noman albasa a Afirka  a bayan…

A  duk shekara ana shigowa da tan miliyan 1.1 na albasa, duk da kasar nan ce ta biyu wajen noman albasa a Afirka  a bayan kasar Masar.

Shugaba Kula da Harkokin Albasa na Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya, Musatapha Khadiri, ya bayyana haka a wajen taronsu da ya gudana a Sakkwato.  Ya ce a kowace shekara Najeriya na bukatar tan  miliyan 2.5, amma tana noma tan miliyan 1.4  a shekara abin da ya kawo mata gibin sauran ke nan da ake shigowa da su.

Khadiri ya kara da cewa rufe kan iyakokin kasa da aka yi ya kara bunkasa noman albasa a Najeriya, matakin da ya ce abin yabawa ne ga kasa don hakan zai sanya kasar ta dogara da kanta musamman a harkar noman albasa. “Rufe iyaka a yanzu ya sanya manoma mayar da hankali ga noma don ciyar da kansu, amma duk da haka akwai ’yan wahalhalu ga ’yan kasuwar albasa na Afirka,’” inji shi

Sakataren Kungiyar Manoma da ’Yan Kasuwar Albasa ta Najeriya, Aliyu Isah Mai Tasamu, ya ce da albasa za ta samu yanayi mai kyau za ta samar wa Najeriya kudin shiga Dala miliyan 420.