Search
Subscribe
A nada kwamishinoni a Jihar Katsina

A nada kwamishinoni a Jihar Katsina

Wata takwas ke nan da zaben shugabannin Najeriya, sannan kusan wata hudu da rantsar da wadanda aka zaba, ciki har da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari. Sai dai tun bayan da talakawa suka fito suka biya musu bukatunsu, shugabannin sun watsar da talakawan, sun koma harkokin gabansu kawai. Mulki aiki ne, kuma aiki ja, wanda mutum daya, bai iyawa, shi ya sa dokar tsarin mulkin Najeriya ya ce dole a kafa majalisun zartarwa a matakai daban-daban na gwamnati. A matakin jiha, misali, majalisar ta kunshi kwamishinoni, su ne ma jigonta. Gwamna Aminu Bello Masari, tsohon mai yin doka ne, ya sani ko ya dace ya yi watsi da batun kafa wannan majalisa ko a’a. Idan muka yi la’akari da cewa manyan ayyuka muhimai ba a yin su sai da amincewar Majalisar Zartarwa cikakkiya, sai mu ce yanzu a gwamnatance a Jihar Katsina, sai dai garambawul da kwaskwarima, amma aiki dai bai yiwuwa.

In kuma ana yi, to ba bisa ka’ida ake yin sa ba, wanda daga karshe maimakon aikin ya kawo ci gaba, sai ma koma baya da almubazzaranci da rashawa kawai zai haifar.

Kai ko a mulkin soja ana Majalisar Zartarwa, balantana mulkin farar hula wanda sai da aka shata wa mutane karairayi suka amince suka zabi mutum.

Jinkiri mai tsawo da daukar lokaci ba kwamishinoni wadanda su ne za su jagoranci hukumomin gwamnati, ba zai kawo ci gaba ba sai dai ci baya. Mulkin nan dai lokaci gare shi, kuma in da gaske ake, to bai kamata a samu wani Gwamna da zai bata lokacin ba. Jiha kamar Katsina mai fama da manyan kalubale ,ciki har da matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa, matsalolin ilimi da kiwon lafiya, bai kamata a ce har yanzu wani abu ake daban da ya hana a kafa gwamnati a fara aikin da aka alkawarta wa mutane ba.

Abin da muke kara tambaya, a matsayinmu na ’yan kasa masu ’yanci shi ne: Me ya hana Gwamna Masari kafa gwamnati kawo yanzu? Akalla tunda gwamnatin farar hula muke, to mun cancanci a fito a bayyana wa jama’a dalilan, sai mu san irin matakin da za mu dauka a gaba. Duk wani abin da za ai inda ba gwamnati, to ana yi ne kawai.

A koyaushe na samu dama, nakan shaida wa mutane cewa dalilin da ya sa wadansu shugabanni, musamman marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa ya samu nasarar aiwatar da wasu muhimman ayyuka a Jihar Katsina, ba komai ba ne illa yadda ya zabi kwararrun mutane a matsayin wadanda za su taimaka masa. Da Umaru bai da mataimaka da bai samu nasarar da ya samu ta gina Jihar Katsina daga 1999-2007 ba.

Matsalar Jihar Katsina ba ta rashin masu bada shawara ba ce. Akwai dimbin masu ilimi, amma an yi watsi da su an dauko ’yan farfaganda da wadanda ba su da kwarewa a kowane fage an nada su a matsayin masu bada shawara. Ta yaya mutumin da bai da abu zai ba ka abin? Hausawa na cewa ‘wanda ya ce zai ba ka riga, to ka fara kallon ta wuyansa.’ Yaya za a maida jihar da ke da take da tarihi a Najeriya kurar-baya, ana ba duk wanda aka dama mukami ba tare da an yi la’akari da kwarewarsa ko cancantarsa ba, sannan a yi zaton za a samu kyakkyawan sakamako?

’Yan farfaganda da masu karyar su ’yan siyasa ne da ’yan sauya- sheka, ba za su iya ba Gwamna Masari shawarar da ta wuce irin ta ’yan fada ba, za su fadi abin da suka fahimci kawai Masarin ke so ne.

Idan Gwamna Masari yana son rubuta sunansa a kundin tarihin Jihar Katsina a matsayin daya daga cikin gwamnonin da suka yi wani abin bajinta, to dole sai ya taka wa ’yan ma’abban siyasa birki. Dole Masari ya fidda son zuciya ya tsaya ba tare da la’akari da siyasa ba,ya zabo mutane wadanda ke da shaida ta kwarewa, kuma ke da shaida ta gaskiya, cewa su masu kishin Jihar Katsina ne.

Sannan ya kamata Gwamna Masari ya gaggauta nada kwamishinoni kwararru. Shekara hudu ba nisa, in dai da gaske yake yi. Ita gaskiya, gaskiya ce, duk abin da kuka yi na nan a rubuce, kuma mutane sun sani. Mun san in da aka fito, kuma muna biye da tafiyar, don haka dan farfaganda ko dan bangar siyasa bai isa ya dakile wani abu ba. Muna fata Gwamna Masari zai ji shawarar da muka ba shi ya yi aiki da ita. Muna son a nada kwararrun mutane masu kishin Jihar Katsina bisa cancantarsu ba bisa cewa kawai sun yi wa jam’iyya hidima ba.

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa Masu Rajin Hadin Kan ’Yan Najeriya 08165270879

 

Kara harajin kaya bai dace ba

Daga Nasiru Kainuwa Hadeja

A ’yan kwanakin nan mun ji cewa za a kara harajin kaya wanda yin hakan zai iya jawo hauhawar farashin kayan masarufi. Allah Ya ji kan Umaru Musa ’Yar’aduwa domin wannan harajin da ake maganarsa an ce shi da ya zo rage shi ya yi.

Haka zalika man fetur a bisa al’ada shugabanninmu kara kudinsa suke yi, amma shi ragewa ya yi. Irin wadannan matakai da ’Yar’aduwa ya dauka tabbas ba karamin saukaka rayuwar talaka suka yi ba, kuma ya yi ne duk don talakan ya san ana yi da shi.

Shi ya sa a kullum nake fadin kaf shugabannin Najeriya da na ga mulkinsu, Umaru Musa ’Yar’aduwa ne, na yi amannar ya zo da salon mulkin da talaka zai ji dadi kwana kusa.

Allah Ya jikansa, Ya sa can ta fi nan, Malam Umaru ’Yar’aduwa in da wani hakkina a kanka na yafe maka duniya da Lahira.

Talakawan Najeriya na jin jiki, muna addu’ar Allah Ya kawo mana mafita.

Nasiru Kainuwa Hadeja (08100229688)

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin