✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘A rage yawan kwanakin da alhazan Najeriya a Saudiyya’

A yayin da aka kammala aikin kwaso alhazan Najeriya daga kasa Mai tsarki, wani malamin addinin Musulunci kuma Shugaban darikar kadiriyya a Jos da ke…

A yayin da aka kammala aikin kwaso alhazan Najeriya daga kasa Mai tsarki, wani malamin addinin Musulunci kuma Shugaban darikar kadiriyya a Jos da ke Jihar Filato, Sheikh Na’Annabi Mu’azu Umar ya yi kira ga Hukumar Hajji ta kasa ta rage yawan kwanakin da alhazan Najeriya suke yi a Saudiyya.

Malamin ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya, inda ya ce kwanakin da alhazan Najeriya suke yi a kasa Mai tsarki na da kyau Hukumar Hajji ta kasa da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi su rage su.

Sheikh Na’Annabi, wanda yana daya daga cikin wadanda suka halarci aikin Hajjin bana, ya ce ya kamata ya zamanto kwanakin da alhazai za su yi a kasa Mai tsarki kada su tsawaita ta yadda guzurinsu zai kare, domin guzurin da ake bayarwa ba iya isar alhazai kwanakin da suke yi, kamar kwana 40 ko 50.

Haka kuma ya yi kira ga hukumomin jin dadin alhazan na kasa da na jihohi, su daidaita zaman kwanakin da alhazan Najeriya suke yi a Madina, domin tsarin zaman alhazan Najeriya a can suna samun matsalar rashin bayar da cikakken kwanakin da ya kamata alhazai su yi.

“Wadansu alhazan kwana biyu suke yi, wadansu kwana daya, wadansu kwana biyar, ko kwana bakwai. Saboda muhimmancin zaman Madina ga alhazai, ya kamata hukumomin alhazai su kara wa musu kwanaki a zaman Madina.

Wato a daidaita idan kwana bakwai-bakwai za a rika yi, sai a rika yi. Ya zamanto duk alhazan Najeriya su rika yin kwana bakwai a Madina. Amma babu dadi alhazai su rika yin kwana biyu ko daya a zaman Madina,” inji shi.

Daga nan ya yaba wa Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato kan yadda ta gudanar da ayyukan aikin Hajjin bana. Ya ce hukumar ta yi kokari sakamakon tallafawar da Gwamnan Jihar ya yi.